NAJERIYA A YAU: Matakan daƙile kisan matafiya a hanyoyin Najeriya
Published: 23rd, June 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Matsalar tare fasinjoji da kashe su a hanyoyin Najeriya na ƙara tsananta, musamman a yankunan Arewa.
Misali, a shekarun baya an sha tare matafiya a kashe su a hanyar Abuja zuwa Kano. A kwanakin baya ma an kashe wasu matafiya a garin Uromi da ke jihar Edo a hanyar su ta komawa Kano.
Sai na kwanan nan da ya faru a Jihar Filato inda aka kashe wasu matafiya da ke kan hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure.
NAJERIYA A YAU: Yadda Tsarin Ilimi Ke Karya Gwiwar ’Yan Najeriya DAGA LARABA: Ko Kare Kai Daga Harin ‘Yan Ta’adda Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro?Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne da nufin gano matakan daƙile afkuwar haka a nan gaba.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kisan Matafiya Matafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Shettima ya bar Abuja don halartar taron majalisar ɗinkin duniya a New York
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa birnin New York na Ƙasar Amurka, domin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80.
Taron zai gudana daga ranar Litinin, 22 ga watan Satumba, zuwa ranar Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2025.
Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu Jami’ar European-American ta musanta bai wa Rarara digirin girmamawaShettima zai wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wannan babban taro.
Zai gabatar da jawabi, tare da shiga muhawarar shugabannin ƙasashe a zauren taron.
A yayin taron, Mataimakin Shugaban zai kuma bayyana sabbin muradun Najeriya a ƙarƙashin yarjejeniyar kare muhalli.
Wannan zai gudana ne a wani taro na musamman kan sauyin yanayi da Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya zai shirya a ranar Laraba, 24 ga watan Satumba.
Haka kuma, Shettima zai halarci wani taron koli kan samar da gidaje masu sauƙi da sauƙin farashi, wanda Shugaban Ƙasar Kenya zai jagoranta.
Bayan kammala taron, Shettima zai wuce Birnin Frankfurt, na Ƙasar Jamus, inda zai gana da jami’an bankin Deutsche Bank kafin dawowa Najeriya.