Indomie Arewa Ta Ƙaddamar da AI Career Generator Domin Ranar Yara
Published: 20th, June 2025 GMT
A ranar 27 ga Mayu, 2025, Indomie Arewa ta ƙara ɗanɗano da armashi a cikin tasowar yara. Babban kamfanin abincin tana alfaharin ƙaddamar da Indomie AI Career Generator, wata dandalin zamani irinsa na farkon da aka ƙirƙira don nuna irin baiwar da yara ke da ita ta hanyar ba su damar ganin makomarsu ta wata sabuwar hanya.
Indomie tun da dadewa tana da kaimin ciyarwa da abincin dake gina jiki da kuma cincidar Mafarkin
kowanne yaro. Wannan dandalin na Indomie AI Career Generator ya tunkari wannan manufa, na taimakawa yara su fahimci ƙarfin gwiwarsu, su yi manyan mafarkai, kuma su san cewa makomarsu tana gab da su.
“Indomie ta tallafa wa yarada dama wajen girma, koyo, da zama ababen Alfahari. Tare da wannan Manhajar,
muna ɗaukar wannan goyon baya ne zuwa mataki na gaba. muna taimakawa yara wajen hango makomarsu kuma su haɗa tunaninsu da nasarar da ke gaba.”
— Tawagar Indomie Arewa
Wannan dandali, wanda aka fassara zuwa harshen Hausa, yana amfani da fasahar zamani ta Artificial Intelligence (AI) don haɗa hoton yaro a matsayi da kuma Shiga irinta aikin da ya zaɓa a matsayin mafarkinsa. Sakamakon kuwa shi ne kyakkyawan hoto da zai ba yaron damar ganin kansa a matsayin wanda ya cimma burinsa a nan gaba.
Domin fara amfani da dandalin, iyaye na iya bin hanyoyin da aka saka a kafafen sada zumunta ko su duba
QR code. Bayan haka, za su shigar da sunan yanka na yaron, jinsin sa, zaɓin aikin da yaron ke mafarki, da kuma lambar WhatsApp. Bayan ɗaukar hoton yaron da karɓar sharudda, AI zai sarrafa hoton ya kuma ƙirƙiri hoton aiki mai ƙayatarwa wanda za a iya sauke shi a Watsa a ko ina.
Wannan dandali yana ba yara damar yin murnar baiwarsu, jin daɗin mafarkinsu, da kuma matso dasu kusa da makomarsu ta hanya mai kayatarwa da damar mu’amala.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Samarwa Sassan Kasa Da Kasa Damar Shigowa Ba Tare Da Bukatar Biza Ba
A kwanakin baya, an bude tashar jirgin ruwa ta fasinja ta kasa da kasa ta kasar Sin ta farko, wato tashar jirgin ruwa ta Shekou dake birnin Shenzhen. ’Yan kasuwa daga Argentina, da Chile, da Brazil sun shiga kasar Sin ta tashar bisa sabuwar manufar shiga kasar Sin ba tare da biza ba, inda aka rage lokacin daidaita aikin canza jirgi daga awoyi biyu da rabi zuwa kasa da rabin awa. Wannan ya shaida cewa, an aiwatar da manufar shiga kasar Sin ba tare da biza ba, ba ma kawai a filin jirgin sama ba, har ma a tashar jirgin ruwa. Hakan ya hanzarta raya cinikayyar Sin da kasashen waje.
Wannan batu ya kasance wani misali, bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar shiga kasar Sin ba tare da biza ba. A cikin shekaru 5 da suka gabata, wato cikin wa’adin aiwatar da shirin shekaru biyar-biyar na raya kasar Sin na 14, gwamnatin kasar ta kara kyautata manufofin shiga kasar ba tare da biza ba a fannoni daban daban, don sa kaimi ga yin mu’amala tare da sauran sassan kasa da kasa.
A halin yanzu, kasar Sin ta bada damar shiga kasar ba tare da biza ba ga kasashe 75, inda yawan kasashen da suke da izinin ratsa kasar Sin ba tare da biza ba ya karu zuwa 55, kana yawan tasoshin bincike dake kan iyakar kasar Sin da sauran kasashe makwabta, inda ake iya shiga kasar Sin ba tare da biza ba ya karu zuwa 60, kana tsawon lokacin da ake iya yada zango cikin kasar ya karu zuwa awoyi 240, wanda hakan ya kawo sauki ga al’ummun kasashen waje, dake zuwa kasar Sin don yawon shakatawa, da yin ciniki da kuma yin ziyara.
Manufofin shiga kasar Sin ba tare da samun biza ba sun shaida cewa, Sinawa suna son baki tun a da can, kuma gwamnatin kasar Sin ta yi imani da fadada bude kofa ga kasashen waje. A shekaru 5 masu zuwa, Sin tana maraba da karin al’ummun kasashen waje da za su shiga kasar Sin, da ganewa idanunsu yanayin kasar da kuma fahimtarta. Kazalika, hakan zai kara shaida cewa, bunkasar kasar Sin na da nasaba da duniya, kana wadatar duniya tana bukatar kasar Sin baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp