Za mu ci gaba da tattaunawa da Iran kan yarjejeniyar nukiliya — Trump
Published: 25th, June 2025 GMT
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce wakilan ƙasarsa za su gana da na Iran domin ci gaba da tattaunawa kan makaman nukiliyarta a mako mai zuwa.
“Za mu tattauna da Iran a mako mai zuwa, ƙila mu ƙulla yarjejeniya ko kuma akasin haka, ba na ce ba,” in ji shi yayin jawabinsa a taron ƙasashe na ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO da ake yi a ƙasar Netherlands.
“Ba su daɗe da gama yaƙi ba, yanzu za su ci gaba da harkokinsu. Ban damu dole sai na ƙulla wata yarjejeniya da su ba,” a cewarsa.
A jiya Talata ce Trump ya soki Isra’ila da Iran, bayan zargin ƙasashen biyu da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ƙulla.
Lamarin na zuwa ne bayan ɓullar rahoton kai wa juna hari daga dukkan ƙasashen biyu, duk da ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta ’yan sa’o’in da suka gabata.
Trump ya ce ƙasashen sun daɗe suna faɗa da juna, kuma a wannan mataki ana iya cewa ba su ma san abin da suke yi ba.
Ya ce: “Ba abin da muke so ke nan ba, ina tabbatar muku cewa ina fushi da abin da suka aikata.”
Shugaba Trump ne mutum na farko da ya fara sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ilan da Iran, bayan shafe kwana 12 suna kai wa juna hare-hare.
Sai dai Iran ta musanta sanarwar da Trump ya yi cewa ta amince da tsagaita wuta a yaƙinta da Isra’ila, inda ta ce ƙofarta a buɗe take don dakatar da yaƙin, matuƙar Isra’ila ta dakatar da kai mata hari.
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ne ya yi wannan jawabi, a saƙon da ya wallafa a shafinsa na X a wannan Talata, yana mai cewa ya zuwa yanzu babu wata matsaya da suka cimma ta tsayar da wannan yaki, har sai Isra’ila ta fara dakatar da farmakinta a Iran, da ƙarfe 4 agogon Tehran, sannan Iran za ta mayar da wukarta cikin kube.
Tun cikin dare Litinin wayewar gari Talata ne Trump ya yi shelar cewa Isra’ila da Iran sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta na mataki-mataki daga ƙarfe 4:00 agogon GMT ranar Talata, da zummar kawo ƙarshen mummunan tashin hankali da aka shafe kusan makonnin biyu ana yi.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce yarjejeniyar ta nemi “cikakkiyar tsagaita wuta,” inda Iran za ta fara daina aiki [kai hare-hare], sannan Isra’ila za ta daina bayan sa’o’i 12.
Ana sa ran tsagaita wutar zai kasance “ƙarshe a hukumance” ga abin da Trump ya kira “Yaƙin kwanaki 12.”
“Bisa zaton cewa komai zai tafi yadda ya kamata, zan so na taya ƙasashen biyu murna, Isra’ila da Iran, game da kasancewa da ƙarfin hali da bajinta da kuma basirar kawo ƙarshen abin da ya kamata a kira “Yaƙin kwanaki 12,” kamar yadda Trump ya wallafa.
Rikicin ya ɓarke ranar 13 ga watan Yuni ne a lokacin da Isra’ila ta ƙaddamar da hare-hare kan wuraren soji da nukiliya da kuma fararen-hula a Iran ciki har da tashar inganta yuraniyom ta ƙarƙashin ƙasa da ke Fordo.
Tehran ta mayar da martani da hare-haren makamai masu linzami kan wurare a Isra’ila, lamarin da ya janyo jerin ramuwar gayya da ya ta ƙasashen biyu suka fara kai hare-hare kan juna kai-tsaye.
Tashin hankali ya ƙaru a lokacin da Amurka ta yi tarayya da Isra’ila wajen kai hare-hare ranar 22 ga watan Yuni, inda ta kai hare-hare kan tashoshin nukiliyar Iran uku lamarin da ya sa makami mai linzamin Iran ya kai hari kan sansanin sojin saman Amurka na Al Udeid da ke ƙasar Qatar.
Trump ya haƙiƙance cewa hare-haren da suka kai sun tarwatsa tashoshin nukiliyar na Iran, tare da cewa jami’an ƙasar ba su iya kwashe wani abu daga tashoshin ba “saboda abubuwa ne masu wuyar kwashewa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Iran Isra ila nukiliya yarjejeniyar tsagaita wuta kai hare hare
এছাড়াও পড়ুন:
Mali ta ƙulla yarjejeniyar nukiliya da Rasha
Shugaban Mali, Assimi Goita da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar makamashin nukiliya a fadar Kremlin da ke birnin Moscow.
Wannan dai na cikin wasu yarjejeniyoyi da Mali da Rasha suka rattaba hannu waɗanda aka tsaro domin inganta alaƙar kasuwanci da tattalin arziki.
Trump ya soki Iran da Isra’ila kan saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta An tura ’yan China 6 kurkuku kan laifin ta’addanci a NijeriyaShugaba Vladimir Putin ya shaida wa shugaban kasar ta Afirka ta Yamma da ke ziyara cewa akwai wasu fannoni na musamman da za a iya ƙara haɗin kai.
Putin ya karbi bakuncin Kanal Assimi Goita a fadar Kremlin, inda suka tattauna tsawon awanni biyu, kamar yadda kafafen yaɗa labaran gwamnati na Rasha suka bayyana.
Putin ya ce dangantakar Rasha da Mali tana samun “kyakkyawan ci-gaba” duk da cewa cinikayyar ɓangarorin biyu a halin yanzu tana da “ƙaranci,” kamar yadda rahoton Kremlin ya nuna.
Daga cikin abin da yarjejeniyar ta ƙunsa akwai haɗin kai domin samar da makamashin nukiliya, kamar yadda Rashar ta bayyana.
Goita dai yana ƙara ƙulla alaƙa da Rasha ne bayan juyin mulkin da ya jagoranta a shekarar 2021, sannan ya juya wa Faransa — wadda ta raini ƙasarsu baya.
Da yake jawabi a ranar Litinin, Putin ya ce sun inganta yarjejeniyar ne, sannan suka tattaunawa hanyoyin da za su ƙara ƙulla alaƙa a “ɓangarorin ma’adinai da makamashi da agaji.”
Goita ya yi godiya ga Rasha bisa irin “karamcin” da aka masa, sannan ya nanata shirin Mali na ɗabbaƙa yarjejeniyar, waɗanda ya ce sun ƙunshi ɓangarori da dama.
Alaƙar tsaro dai na cikin muhimman abubuwan da ke tsakanin Rasha da Mali.