’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 2, sun kama wasu a Kaduna
Published: 25th, June 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, sun kashe ’yan fashi biyu, sannan sun kama wasu biyu a unguwar Makera da ke Kakuri.
Wannan ya biyo bayan musayar wuta da jami’an tsaro suka da ’yan fashin.
Gwamnan Nasarawa ya sanya wa gadar sama sunan Tinubu PDP ta mayar wa da na hannun damar Wike kujerarsa ta sakatarentaRundunar ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:10 na dare, bayan da suka samu kiran gaggawa daga mazauna unguwar Gashash a Barnawa.
Rahotanni sun ce ’yan fashi guda takwas sun shiga wani gida ɗauke da bindigu da makamai, sun sace wayoyi, kwamfutoci da sauran kayayyaki.
Bayan kiran gaggawar, DPO na Barnawa, Kakuri da Sabon Tasha tare da sojoji daga Rundunar 312 Artillery Regiment suka bi ’yan fashin har titin Makera.
Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya ce, “Da ’yan fashin suka ga jami’an tsaro, sai suka fara harbi.
“Wannan ya jawo musayar wuta, inda aka kashe biyu daga cikinsu sannan aka kama biyu da ransu.”
Jami’an tsaro sun ƙwato bindiga ƙirar gida, harsasai da wasu makamai.
Sannan sun dawo da kayan da aka sace ciki har da wayoyi bakwai, agoguna uku, kwamfutoci biyu da sauransu.
A lokacin musayar wutar, ɗan sanda ɗaya ya samu rauni amma an miƙa shi asibiti inda yake samun kulawar likitoci.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Rabiu Muhammad, ya jinjina wa jami’ansa kan yadda suka yi aiki cikin gaggawa tare da haɗin kai da sojoji da DSS.
Ya ce rundunar ta ƙudiri aniyar kare jihar daga miyagu.
Ya kuma roƙi al’umma da su riƙa sanya idanu tare da kai rahoton duk wani abun zargi.
Rundunar ta ce tana ci gaba da neman sauran ‘yan fashin da suka tsere.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda yan fashi musayar wuta
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnati Za Ta Biya Wasu Kudaden Ariyas Ga Masu Fensho Wannan Wata
An sake tabbatar wa ma’aikatan Gwamnatin Tarayya FG da suka yi ritaya cewa za a biya su wani bangare na kudaden ariyas a cikin wannan watan, kamar yadda hukumomin da abin ya shafa suka yi alkawari.
Mataimakin Sakataren ƙungiyar masu karɓar fansho ta ƙasa, Alhaji Ahmed Gazali, ya bayar da wannan tabbaci yayin da ake tattaunawa da shi ta wayar tarho daga Abuja.
Alh. Ahmed Gazali, ya yi bayanin cewas daraktan dake kula da kudade na ofishin akanta janar na tarayya ya tabbatar da daukan matakin hakan na biyan kudaden.
Ya bayyana fatan ganin kudirin FG na gaggauta biyan kudade, domin dakatar da duk wata zanga zanga wanda hakan bai dace ba ga ma’aikatan da suka yi ritaya domin bata martaban kasan nan.
Hakan kuma masu karban fensho a Radion Tarayya na kasa FRCN da Gidan talabijin na kasa NTA dake Kaduna sun nuna damuwarsu game da zargin da ake yi cewa ana kokarin wulakanta shugabannin kungiyar ma’aikatan da suka yi ritaya karkashin jagorancin kwamaret Munkaila Ogunbote.
DAGA SULEIMAN KAURA