Za mu ci gaba da yi wa Isra’ila luguden wuta — Shugaban Iran
Published: 22nd, June 2025 GMT
Shugaban Ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa ƙasarsa za ta ci gaba da mayar da martani kan hare-haren da Isra’ila ke kai mata.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake magana da shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ta wayar tarho.
Uba Sani ya yi jajen ’yan ɗaurin aure 12 da aka kashe a Filato Ɗan ƙunar baƙin wake ya kashe mutum 10 da bam a BornoShugaba Pezeshkian ya ce Iran tana da niyyar yin haɗin gwiwa da sauran ƙasashe don amfani da makamashin nukiliya ta hanyar da ba ta da alaƙa da yaƙi, amma hakan ba yana nufin za su dakatar da inganta shirye-shiryensu na nukiliya gaba ɗaya ba.
Ya ƙara da cewa hare-haren da Isra’ila ke kai wa ƙasarsa ba za su wuce haka nan ba, domin kuwa Iran za ta riƙa mayar da martani mai zafi.
A ranar Asabar, rundunar sojin Iran ta yi gargaɗi cewa za ta kai wa Isra’ila ta hark ta jiragen ruwa.
A cewar wani kakakin rundunar sojin Iran da ya bayyana a wani bidiyo, duk ƙasar da ta tura makamai zuwa Isra’ila, kamar ta shiga yaƙi da Iran ce kai-tsaye, kuma Iran ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kare kanta ba.
A ranar Juma’ar da ta gabata, Iran ta harba makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa zuwa Isra’ila, lamarin da ya jikkata mutane aƙalla 19 a birnin Haifa da ke Arewacin Isra’ila, kamar yadda wani asibiti a yankin ya tabbatar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Iran Isra ila Shugaban Ƙasa yaƙi
এছাড়াও পড়ুন:
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Maso Goyon Bayan Isra’ila Suna Da Hannu A Laifukanta
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila na aikata kisan kiyashi a Gaza, kuma magoya bayanta suna da hannu a ciki
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada cewa: Rahoton kwamitin binciken gaskiya na Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar da cewa, laifukan da haramtacciyar kasar Isra’ila ta aikata a Gaza sun kai na “kisan kare dangi”, inda ya yi kira ga masu kare gwamnatin ta Isra’ila da su daina shiga da hada baki wajen aikata wadannan laifuka kan al’ummar Falastinu.
Baqa’i ya bayyana cewa: Kwamitin bincike mai zaman kansa na kwamitin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya kan laifukan da ake aikatawa a Falasdinu da aka mamaye karkashin jagorancin fitacciyar marubuciya Navi Pillay, ba ta da wata shakka game da irin laifukan da kuma irin zaluncin da ake yi a Gaza. Ya yi nuni da cewa, hukumar ta tabbatar a cikin wani bincike na shari’a mai shafuka 72 na gaskiya da alkaluma, cewa haramtacciyar kasar Isra’ila na aikata kisan kiyashi a Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Cika Kwanaki 713 Suna Kisan Kiyashi A Zirin Gaza September 18, 2025 Harin Makami Mai Linzami Yemen Ya Tilastawa Jirgin Fira Ministan Gwamnatin Isra’ila Saukar Gaggawa September 18, 2025 Eslami: Dole ne IAEA ta zama mai cikakken ‘yancin cin gashin kai September 18, 2025 Rahoto: An yi tattaunawa mai tsawo tsakanin Syria da Isra’ila a Landan September 18, 2025 Sheikh Qassem: Harin Pager jarabawa ce wadda ta kara wa masu gwagwarmaya kwarin gwiwa September 18, 2025 Pezeshkian: Iran da Masar suna da tsohon tarihi a duniya September 18, 2025 Iran ta samu Zinariya, Azurfa, da Tagulla a Gasar Kokawa ta Duniya September 18, 2025 Iran Ta Yi Nasarar Gwajin Tauraron Dan’adam Da Zai Samar Da “Internet” Ga Yankunan Karkara September 17, 2025 Za A Kada Kuri’ar Raba Gardama Akan Sabon Tsarin Mulki A Kasar Guinea September 17, 2025 Larijani: Iran Da Saudiyya Za Su Bunkasa Aiki Tare A Fagagen Kasuwanci Da Tsaro September 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci