Sin Za Ta Hanzarta Duba Bukatun Samun Lasisin Fitar Da Ma’adanan “Rare Earth” Zuwa Ketare
Published: 20th, June 2025 GMT
A yau Alhamis, ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta bayyana cewa, kasar tana ba da muhimmanci sosai kan kiyaye kwanciyar hankali da tsaron bangaren masana’antu da tsarin samar da kayayyaki a duniya, kana tana kara hanzarta sake duba bukatun samun lasisin fitar da kayayyakin ma’adanai na “rare earth” masu daraja da ake sarrafa kayayyakin fasaha da su kamar yadda yake kunshe a tanade-tanaden dokoki da ka’idoji masu alaka da hakan.
Mai magana da yawun ma’aikatar He Yadong, ya bayyana a wani taron manema labarai lokacin da yake amsa wata tambaya kan fitar da ire-iren wadannan ma’adanan cewa, kasar Sin ta amince da wasu bukatun da suka dace bisa doka, kuma za ta ci gaba da karfafa sake nazari da amincewa da ire-iren wadannan bukatun.
Har ila yau, ya ce, kasar Sin ta ci gaba da zantawa da kungiyar tarayyar Turai a matakai daban-daban ba tare da jinkiri ba, don karfafa bunkasa hadin gwiwar cinikayya da zuba jari mai inganci ba tare da tangarda ba. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Ban da haka, shugaban na Sin ya ce, kasarsa na son yin kokari tare da bangarori daban daban, wajen aiwatar da ra’ayin raya kasa na kirkiro sabbin fasahohi, da tabbatar da daidaito, da kare muhalli, da bude kofa, gami da haifar da alfanu ga kowa, ta yadda za a kafa wata al’ummar bai daya ta yankin Asiya da na tekun Pasifik.
Duk a wajen taron, yayin wani bikin mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, shugaba Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin za ta karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 33, wanda ake sa ran gudanar da shi a birnin Shenzhen na kasar Sin a watan Nuwamba na shekarar 2026. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA