Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Namadi Sambo Ya Karyata Sauya Sheƙa Zuwa APC
Published: 19th, June 2025 GMT
Wasu na ganin jita-jitar ta samo asali ne bayan wani abokin aikinsa na baya, Sani Sidi, ya koma jam’iyyar APC tare da magoya bayansa a Kaduna.
Amma Sambo ya ce hakan bai shafe shi ba.
Hakazalika, an shirya Sambo zai halarci bikin ƙaddamar da asibiti mai gadaje 300 da ke Kaduna a ranar Alhamis, 19 ga watan Yuni, 2025.
Ya halarci bikin kuma hakan ba yana nufin ya goyi bayan wata jam’iyya ba ne.
Ƙungiyarsa ta nanata cewa Sambo yana nan daram a cikin jam’iyyar PDP, kuma labarin sauya sheƙar nasa ƙarya ce da aka ƙirƙira domin tayar da hankali da ƙoƙarin cimma wasu muradu na siyasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Ta Dauki Manyan Matakan Kare Jihar Daga Ambaliyar Ruwa
Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada kudirin ta na kare al’umma daga ambaliyar ruwa kamar yadda hukumar hasashen yanayi ta kasa ta yi hasashen samu a wasu kananan hukumomin jihar a daminar bana.
Mataimakin Shugaban kwamitin fasaha kan magance ambaliya, kuma mai bai wa Gwamna Umar Namadi shawara kan ambaliya da kuma sauyin yanayi, Alhaji Hamza Muhammad Hadejia ya bayyana haka yayin da yake duba aikin jingar ruwan kogi da ya ratsa garuruwan Auyo da Tsidir da Agin da Matsa da Sorakin da Jiyan da Tage da Turabu da kuma Tandanu.
Alhaji Hamza Hadejia ya ce daga zuwan Gwamna Umar Namadi kan karagar mulkin Jihar, ya dauki kwararan matakai don kaucewa ambaliyar ruwa, domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya kuma bayyana cewar, Gwamna Namadi ya inganta harkar noma don tabbatar da isasshen abinci da samar da ayyukan yi ga al’ummar karkara.
A cewar sa, kwamitin fasaha na magance ambaliya ya zage damtse wajen sarrafa koguna da gina kwarya-kwaryar shinge a wuraren da ake sa ran ambaliya domin magance matsalar.
A don haka, Hamza Muhammad Hadejia, ya bukaci jama’a su ci gaba da bada hadin kai da goyon baya ga gwamnatin jihar domin a cimma wannan manufa domin kwalliya ta biya kudin sabulu.
ya kuma yabawa Gwamna Umar Namadi bisa hadin kai da goyon bayan da ya ke baiwa ayyukan kwamitin a kowane lokaci.
A jawaban su, Dagacin Turabu Malam Shu’aibu Saje da Shugaban ci gaban al’umma Sani Barde da tsohon kansila Umar Jiyan, sun jinjinawa Gwamna Umar Namadi da shugaban karamar hukumar Auyo da mai ba da shawara Hamza Hadejia bisa kokarin kare rayuka da dukiyoyin su, tare da tabbatar da gudunmawar su don cimma burin gwamnati kan magance ambaliya a yankin.
Sun kuma godewa gwamnatin jihar Jigawan da ta kananan hukumomi bisa samar da ababen more rayuwa da kuma bunkasa harkokin ilimi da lafiya da ruwa da wuta da hanyoyi da kuma bunkasa noma don samar da isasshen abinci da ayyykan yi a tsakanin al’ummomin karkara.
Usman Mohammed Zaria