Leeds ta ɗauki ɗan bayan Udinese Jaka Bijol
Published: 24th, June 2025 GMT
Leeds United ta kammala ɗaukar ɗan wasan bayan ƙungiyar Udinese na ƙasar Slovenia, Jaka Bijol mai shekaru 26 kan farashin fam miliyan 15.
Wannan dai shi ne sabon ɗan wasa na biyu da ƙungiyar ta ɗauka bayan zuwan ɗan wasan gaban Jamus, Lukas Nmecha, kyauta.
‘Harin da Iran ta kai wa sansanin sojin Amurka keta haddin Qatar ne’ Iran ta ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin sojin AmurkaCefanen Bijol da Leeds ta yi zai ƙara wa ƙungiyar tagomashi wajen tsaron bayanta a yayin da ake shirye-shiryen dawowa sabuwar kakar wasanni ta Firimiyar Ingila.
Bijol dai ya buga ƙasarsa Slovenia wasanni 63 ciki har da rawar gani da ya taka a gasar Euro 2024, inda suka yi canjaras da Ingila a wasannin cikin rukuni gabanin rashin nasara a hannun Portugal yayin bugun daga kai sai mai tsaron raga daf da tafiya matakin kwata-fainal.
Bijol ya shafe kaka uku a yana taka wa Udinese leda a gasar Serie A, inda ya haska a wasanni 95 bayan dawowarsa ƙungiyar ta Italliya daga CSKA Moscow, inda ya shafe shekaru hudu.
Leeds dai ta samu nasarar haurowa Firimiyar Ingila a watan Mayun da ya gabata, bayan ta karkare gasar Championship ta maki 100 daidai da Burnley wadda ta bai wa rata da kwallaye.
AFP
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Taya Nafisa, Rukayya, Hadiza Murnar Samun Nasarar Zama Gwanaye A Gasar Turanci Ta Duniya
Shugaban ya kuma yabawa cibiyoyin koyon ilimi tare da bayyana cewa wadannan nasarorin da aka samu shaida ne na ingancin ilimin Nijeriya wanda ke kekkenshe yara masu basira a duniya.
Tinubu ya yi imanin cewa, ilimi muhimmin abu ne ga ci gaban kasa; don haka, babbar hobbasar da gwamnatinsa ta yi a fannin, shi ne kawar da matsalolin kudi ga ‘yan Nijeriya marasa galihu da ke neman manyan makarantu ta hanyar ba su ba shi a ashirin Asusun ba da lamuni na ilimi na Nijeriya (NELFUND).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp