Aminiya:
2025-07-26@00:35:05 GMT

Iran ta ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin sojin Amurka

Published: 23rd, June 2025 GMT

Rahotanni na cewa ƙasar Iran ta fara abin da ta kira martani mafi girma da nasara kan hare-haren Amurka.

Kamfanin Dillancin Labaran Iran na Tasnim, ya ce dakarun juyin juya halin ƙasar sun ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami kan sansanin sojin Amurka da ke Qatar da Iraƙi

A halin yanzu ne aka samu labaran jin ƙarar abubuwan fashewar a Qatar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Iran Isra ila Rasha

এছাড়াও পড়ুন:

 Fiye Da  Kungiyoyin 100 A Duniya Sun Yi Gargadi Akan Halin Yunwa Da HKi Ta Jefa Mutanen Gaza A Ciki

Kungiyoyin agaji da kuma na hakkokin bil’adama sun yi gargadi akan yunwar da ake fama da ita a Gaza, tare da yin kira ga gwamnatoci da su yin matsin lamba domin kawo karshe killace Gaza da aka yi, da kuma shigar da kayan agaji a cikin yanki.

Kungiyoyin sun kuma dorawa HKI alhakin halin da mutanen Gaza suke ciki na yunwa.

Daga cikin kungiyoyin da su ka fitar da bayani da akwai Majalisar ‘yan gudun hijira ta kasar Norway” da “Refugee International” da wasu da adadinsu ya kai 111, sun yi gargadi akan yadda yunwa take yaduwa a cikin Gaza.

Bayanin ya kunshi cewa; Mazauna yankin Gaza suna fama da yunwa saboda killace su da Isra’ila ta yi, kuma a duk lokacin da mutanen su ka nunfi wurin da aka ware domin raba abinci sai a bude musu wuta.

Wuararen raba abincin da suke a cikin yankin Gaza dai, HKI da Amurka su ka shriya su a matsayin tarkon kashe Falasdinawa da suke zuwa wurin.

Bayanin ya kuma ce, da akwai kayan abinci, ruwa da magunguna masu yawan gaske da aka ajiye da su a wajen yankin Gaza, amma kuma Isra’ila  ta hana a shiga da su.

Haka nan kuma sun bayyana cewa; Dukkanin kayan agajin da ake da su, sun kare baki daya, kuma kungiyoyin agaji suna Kallon yadda ‘yan’uwansu suke ramewa da kama hanyar mutuwa saboda rashin abinci.

Har ila yau sun yi ishara da cewa: Dokoki da Isra’ila ta kafa ne, da su ka jawo jinki, da kuma yadda take karkatsa yankin na Gaza wanda yake a killace, su ne su ka  haddasa yunwa da mutuwa.”

 Haka nan kuma wadannan kungiyoyin sun yi kira ga gwamnatoci da su kawo karshen bin matakai na cike-ciken takardu akan dukkanin hanyoyi, saboda share fagen shigar da kayan abinci cikin  yankin Gaza.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Robert Malley: Harin Amurka A Kan Wuraren Nukiliyar Iran Babban Kure Ne
  • Tinubu ya fi mayar da hankali wajen gina Kudancin Nijeriya — Kwankwaso
  • Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji
  • Ayatullahi Makarem Shirazi Ya Jinjinawa Al’ummar Iran Kan Hadin kai Da Suka Bayar Lokacin Yakin Kwanaki 12
  • Iran Ta Zargi Amurka Da HKI Da Wargaza Dokokin Kasa Da Kasa Da Kuma Yarjeniyoyin Kasa Da Kasa
  •  Fiye Da  Kungiyoyin 100 A Duniya Sun Yi Gargadi Akan Halin Yunwa Da HKi Ta Jefa Mutanen Gaza A Ciki
  • WFP zai dakatar da tallafin abinci da kiwon lafiya a Nijeriya
  • Babban Hafsan Sojin Iran Ya Ce: Iran Zata Sanya Duk Wanda Ya Dauki Matakin Wuce Gona Kanta Nadama
  • Pezeshkian: Tunanin Kawo Karshen Shirin Nukiliyar Iran Ya Yi Kama Da Tabuwa
  • Sheikh Qasem: Nuna Halin Ko In-Kula Na Duniya Ne Ya Jawo Kisan Kiyashi A Gaza