Sin Ta Fadada Matakin Rage Haraji Ga Kasashe Masu Raunin Tattalin Arziki
Published: 19th, June 2025 GMT
Tawagar kasar Sin a taron birnin Geneva, ta shaidawa kungiyar cinikayya ta duniya WTO, cewa kasar ta fadada matakinta na rage harajin fito da take karba daga kasashe masu karancin karfin tattalin arziki, daga kaso 98 bisa dari zuwa kaso 100 bisa dari.
A jiya Laraba ne tawagar ta Sin ta bayyana wannan albishir, inda ta ce baya ga janye dukkanin harajin fito baki daya, Sin ta sha alwashin kara aiwatar da matakai na ingiza cinikayyar hajoji, da karfafa kwarewar aiki, da aiwatar da kwasa-kwasai na horar da sana’o’in fasaha a kasashen Afirka masu raunin tattalin arziki.
Kazalika, tawagar ta Sin ta ce wadannan matakai na da nufin samar da sabbin damammakin habaka ci gaban wannan rukuni na kasashen Afirka, tare da bayar da gudummawar daidaitawa, da ingiza ci gaban cinikayya tsakanin sassan kasa da kasa.
Membobin kungiyar WTO sun jinjinawa wannan albishir na tawagar Sin, yayin da wakilai daga kasashen Afirka masu raunin tattalin arziki, da sauran sassan kasa da kasa suka bayyana godiya game da hakan, suna masu nuni da tarin kalubale, da yanayin rashin tabbas da kasashe masu tasowa ke fuskanta a duniya. Har ila yau, membobin WTOn sun yi kira ga karin kasashen duniya da su yi koyi da kasar Sin, wajen samar da manufofi masu dacewa, da tallafin horar da kwararru, da tallafawa rukunin kasashe masu karancin karfin tattalin arziki, ta yadda za a iya bunkasa cinikayya mai dorewa, da game dukkanin sassan kasa da kasa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: tattalin arziki
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya Za Ta Aiwatar da Shirin Daƙile Sulalewar Kuɗaɗen Haraji
“daidaita farashin ya kasance hanya daya tilo da za a iya amfani da ita wajen tafiyar da harkokin kasuwa da kuma tabbatar da gaskiya,” in ji shi.
Edun ya nuna ƙalubale a tsarin biyan ciniki a Nijeriya, tare da lura da cewa har yanzu ana samun yawan hada-hadar kasuwanci ta hanyoyin da ba kamata ba.
Ya bayyana cewa gwamnati na binciken gyare-gyare da nufin ƙara bayyana gaskiya, ciki har da yiwuwar gudanar da cinikin danyen mai daga ƙasashen waje da na naira.
“Yawancin mu’amalar kasuwancinmu ana gudanar da su ne a waje da tashoshi na yau da kullun. Muna aiki kan gyare-gyaren da za su inganta tsarin,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp