Kiran Gwamnatin Tarayya Ga ‘Yan Jarida: Ku Zama Jigo Wajen Gina Dimokuraɗiyyar Nijeriya
Published: 22nd, June 2025 GMT
Ya nemi ‘yan jarida da su riƙa amfani da kafafen su wajen haska labarai da ke nuna sauye-sauyen da aka samu a hukumomi, yadda jama’a ke shiga cikin harkokin gwamnati, cigaban ababen more rayuwa da bunƙasar tattalin arziki, a matsayin wani ɓangare na rawar da kafafen ke takawa wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya.
“Yayin da muke bikin shekaru 26 na ci gaba da mulkin dimokiraɗiyya a Nijeriya, dole ne kafafen yaɗa labarai su riƙa yaɗa labaran da ke bayyana nasarorin da dimokiraɗiyyar ƙasar nan ta samu, irin su gyaran hukumomi, gina ababen more rayuwa, shiga jama’a cikin harkokin gwamnati, da kuma cigaban tattalin arziki,” inji shi.
Idris ya ƙara da cewa yayin da kafafen yaɗa labarai suke haska waɗannan nasarori ta hanya mai ma’ana, hakan zai taimaka wajen girmama sadaukarwar da ta haifar da dimokiraɗiyyar Nijeriya tare da ƙarfafa haɗin kan ƙasa da amincewar jama’a da gwamnati.
Ya ƙara da cewa, “Ta yin hakan, kafafen yaɗa labarai suna tabbatar da matsayin su a matsayin ginshiƙi wajen ɗorewa da ƙarfafa tafarkin dimokiraɗiyyar Nijeriya.”
Ya kuma sake tabbatar da cewa gwamnatin Tinubu tana da cikakken niyyar kare ‘yancin faɗar albarkacin baki da ‘yancin kafafen yaɗa labarai.
“Na sha faɗa a wurare da dama, kuma zan sake faɗa a nan, cewa gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da kare ‘yancin kafafen yaɗa labarai a matsayin ginshiƙi kuma tushen dimokiraɗiyyar Nijeriya.
“Za mu ci gaba da ƙarfafa manufofi da shirye-shiryen da za su ba kafafen damar bunƙasa wajen cika nauyin da ya rataya a wuyan su ga dimokiraɗiyya da al’umma,” inji shi.
Ya kuma taɓo ƙalubalen da ‘yan jarida suke fuskanta a wannan zamani na dijital, ciki har da tasirin Ƙirƙirarrar Basira (AI), yaɗuwar labaran ƙarya da rawar da jaridar jama’a ke takawa.
“Bayyanar Ƙirƙirarrar Basira (generative AI) cikin ‘yan shekarun nan ta ƙara dagula lamarin, inda ake cika mu da hotuna da bidiyo na bogi da yaɗa labaran ƙarya, wanda ya sa aikin jarida na gaskiya ya fi wuya, amma kuma ya fi zama wajibi fiye da da,” inji shi.
Ministan ya bayyana cewa ana nan ana aiki tare da UNESCO domin kafa Cibiyar Ilimin Kafofin Watsa Labarai (MIL) ta musamman a Abuja.
“Shi ya sa muke haɗa gwiwa da UNESCO wajen kafa Cibiyar Ilimin Kafofin Watsa Labarai (MIL) a nan Abuja, wacce za ta zama ta farko irin ta a duniya. Da zarar ta fara aiki, wannan cibiyar za ta zama wani babban tushe wajen inganta aikin jarida na gaskiya a Nijeriya,” inji shi.
Idris ya kuma bayyana shirye-shiryen gwamnatin Tinubu na haɗa kai da NUJ wajen fuskantar muhimman matsalolin aikin jarida da suka haɗa da walwalar ma’aikata, daidaiton jinsi, da sauya fasalin aiki zuwa tsarin zamani.
“Muna da niyyar aiki tare da ku da kuma tallafa maku wajen fuskantar waɗannan matsaloli yayin da kuke ƙoƙarin daidaita kan ku da sabon yanayin ƙarni na 21,” inji shi.
Yayin da ya bayyana cewa ɗaya daga cikin manyan ayyukan kafafen yaɗa labarai shi ne sa ido kan ayyukan gwamnati, Ministan ya buƙace su da su riƙa kallon gwamnati a matsayin abokiyar aiki wajen gina Nijeriya mai zaman lafiya da cigaba.
“Ko da yake kuna da rawar da kuke takawa wajen sa ido a kan gwamnati – kuma muna maraba da hakan – akwai buƙatar ku riƙa kallon mu a matsayin abokan aiki, kuma masu haɗa kai wajen samar da zaman lafiya, tsaro da cigaba da ƙasar nan ke nema ƙarƙashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu,” inji ministan.
Ya kuma taya NUJ murna kan cikar ta shekaru 70 da kafuwa tare da yaba wa ƙungiyar kan ƙaddamar da wani littafi da ke bayyana tarihin ta.
“Ina da yaƙinin cewa aikin jarida yana da buƙatar ko yaushe ya riƙa bayyana labaran sa da kan sa da kuma tsara yadda za a bayyana shi; domin ba wani zai yi mana hakan ba,” inji shi.
Idris ya kuma yaba da girmamawa ga Shugaban Taron, Cif Aremu Olusegun Osoba, da kuma Mamallakin jaridar Vanguard, Mista Sam Amuka-Pemu, bisa gagarumar gudunmawar da suka bayar a harkar jarida da hidima ga jama’a, yana mai cewa su ne abin koyi a wannan sana’ar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: kafafen yaɗa labarai aikin jarida
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda Nijeriya Za Ta Ci Gajiyar Fara Yada Shirye-shiryenta Na Rediyo Da Sinanci
A fannin noma ma, watsa shirye-shiryen da Sinanci zai taimaka wajen bayyana burin Nijeriya na fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, musamman yadda take neman aikewa da karin kayayyakin amfanin gona zuwa babbar kasuwar kasar Sin, tare da bai wa masu ruwa da tsaki na kasar Sin damar sanin abubuwan da Nijeriya za ta iya yi, da ka’idojinta ta yadda hakan zai kara daidaita al’ummomin kasashen biyu kan dabarun kasuwanci da kara habaka musayar noma.
A halin yanzu, masana’antun kirkire-kirkiren fikira da na fina-finai, da na kayan kwalliya, da kide-kide da wake-wake suna taka rawar gani wajen harkokin al’adu da kasuwanci. Watsa shirye-shirye da Sinanci zai bai wa masu ruwa da tsaki a wannan fani na kirkire-kirkiren fikira na Nijeriya damar yin cudanya da takwarorinsu Sinawa kai-tsaye, da inganta fahimtar al’adu da yaukaka zumuncin diflomasiyya musamman ma bisa yadda kasashen biyu ke daraja al’adun gargajiya da bayar da labarai na al’mara da hikayoyi. Tabbas, wannan bangare na Nijeriya zai samu tagomashi mai albarka ta fuskar hadakar shirye-shiryen fina-finai, da bukukuwan nune-nunen, da kuma fadada samun kasuwa.
Har ila yau, yayin da Nijeriya ta shiga cikin kungiyar mawaka masu rajin ganin dunkulewar harsuna da tabbatar da damawa da kafofin watsa labaru daban-daban a duniya, watsa shirye-shiryenta da harshen Sinanci zai taimaka wa ayyukanta na diflomasiyya a fannonin tattalin arziki, da cudanyar al’adu, da hadin gwiwar manyan tsare-tsare. Don haka, watsa shirye-shiryen Nijeriya da Sinanci ba kawai bangare ne na yada labarai ba, wani babban yunkuri ne na cin moriyar samar da duniya mai kyakkyawar makoma ta bai-daya ga bil’adama. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp