An Gudanar Da Taron Bita Na Yini 4 Ga Malaman Tafsiri Da Ke Babura
Published: 18th, February 2025 GMT
Cibiyar Malam Bukar mai kula da hidimar al’amuran da suka shafi karantar da Alqur’ani da dake Babura ta gudanar da bitar yini 4 ga Malamai masu Tafsiri da Alarammomi a garin Babura dake Jihar Jigawa.
Da yake jawabi yayin rufe bitar, Shugaban cibiyar, Sheikh Gwani Dr Murtala Bashari yace an shirya bitar ne da nufin kara zaburar da juna da kuma nusar da masu gabatar da tafsirin Alkur’ani kan maida hankali wajen karfafa bin abin Alkur’ani da Sunnar Manzon Allah don kaucewa fadawa miyagun akidu.
Shugaban Wanda jami’in gudanar da Shirin, Dr Ismail Ali kura ya wakilta, ya yabawa mahalarta bitar da jagororinsu bisa kwazonsu.
Shi ma a nasa jawabin, bako na musamman Farfesa Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya ce bitar ta zo a dai dai lokacin da ake fuskantar kalubale na rashin kyakkyawar fahimtar wasu ma’anoni na Alkur’ani da Sunnah.
A don haka, ya bukaci malaman da su kasance a cikin neman ilimi da nazari a koda yaushe.
Hakimin Babura Sarkin Ban Ringim, Alhaji Muhammad Nata’ala Mustapha ya bukaci Malamai da su kara zaburar da iyaye kan muhimmamcin ilimin addinin musulunci ga ‘ya’yansu.
Sai dai kuma, ya koka kan yadda ‘ya’ya mata suka fi maza zuwa islamiyya, knda ya bukaci iyaye su kula domin samun ingantaccen rayuwa.
Daga cikin darussan da malaman suka gabatar yayin bitar sun hada da ilimin da ya kamata mai tafsiri ya samu, da kuma kura-kuran da mai tafsiri ke samu a lokacin karatu.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Babura Jigawa Taron Bita
এছাড়াও পড়ুন:
NPA Ta Bukaci Samar Da Tsare-tsare Kan Baraguzan Jiragen Ruwa A Cikin Teku
Dantsoho wanda ya samu wakilicin Babban Manajan a Hukumar ta NPA Femi Oyewole, ya bayyana cewa, Shugaban Hukumar ta NPA, Hukumar ta mayar da hankali wajen ganin cewa, ana kare kimar Tekunan kasar.
“Hadurran zuba baraguzan kusan a kurkusa suke, wanda kuma, suke ci gaba da karuwa, wanda hakan ya nuna cewa, akwai matukar bukatar a dakile yadda ake duba baragunzan, a cikin Tekunan, baki daya,” Inji Dantsoho.
Ya ci gaba da cewa, Hukumar ta NPA bata yi kasa a guiwa ba, wajen daukar matakan da suka kamata, domin magance wannan matsalar.
“Duba da cewa, muna gudanar da ayyukan NPA yadda ya kamata da kuma bin ka;idojin da ke tafiyar da Hukumar, musamman wajen bai wa kayan Hukumar da ke a daukacin Tashoshin Jiragen Ruwan kasar kariya, kamar yadda suka kasance a matakin na kasa da kasa na dakile gurbatar da Jiragen Ruwa ke janyo wa, musamman duba da kundin tsari na (MARPOL 73/78), za mu ci gaba da lalubo da mafita kan zubar baraguzai a Tekunan kasar,” A cewarsa.
Shugaban ya kara da cewa, kayan aikin NPA na bukatar a samar masu kariyar da kamata, musamman ta hanyar bai wa Jiragen ruwa da ke tsayawa a Tashoshin kariyar da ta kamata.
Dantsoho ya bayyana cewa, NPA akai-akai ta kan tabbatar da ana ci gaba da tsaftace Tekunan daga kalubalen baraguzan da duk wata bola, da ake zubawa a cikin Tekunan kasar a daukacin Tashohin Jiragen Ruwan kasar.
Shugaban ya yi nuni da cewa, ta hanyar kwashe baraguzan da sauran bolar robobin da ake zubawar a cikin Tekunan ne, kadai, za a iya kare rayuwar dabbobin da ke rayuwa a cikin Tekunan tare da kuma samar wa Jiragen Ruwan saukin yin zirga-zirga a kan Tekunan kasar.
Shi kuwa a na sa jawabin a wajen taron Babab Sakataren Cibiyar kungiyar masu fito kaya a Jiragen Ruwa na kasa Dakta Pius Akutah, yabawa kungiyar ta wakilan masu wallafa rahotanin a Tashoshin Jiragen Ruwan kasar kan zabo wannan maudu’in domin a tattauna a kansa
Ya kuma jaddda bukatar da a tabbatar da ana tsaftace hanyoyin Ruwa da ke a Tekunan kasar, musamman domin Jiragen Ruwan da ke hawansu, su samu saukin tafiya akai ba tare da wata tangarda ba.
Akutah, wanda Mataimakin Darakata a sashen sanya ido na cibiyar ya wakilce shi a wajen taron Adeshina Sarumi, ya yi nuni da cewa, samun baraguzan a hanyoyin Ruwan na haifar da cikas ga zirga-zirgar Jiragen Ruwan.
Shi kuwa Manajin Darakta na Hukumar NIWA Bolaji Oyebamiji, ya bukaci masu ruwa da tsaki a fannin da su yi dukkan mai yuwa, domin a dakile wannan kalubalen da ake fuskanta, musaman ta hanyar wyar da kan alummar da ke da zama a daura da Tekunan kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp