FG Ta Jaddada Bukatar Samarda Sabbin Ka’idojin Visa Domin Taimakawa Kasuwancin A Duniya
Published: 17th, February 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya tayi kira don samun tsarin visa mai sassauci ga kamfanonin Najeriya da ke neman kafa masana’antu da kasuwanci a ƙasashen waje.
Ministan Yada Labarai da Wayarda Kan Jama’a, Mohammed Idris, shine ya yi wannan kiran a Addis Ababa, Ethiopia, yayin da ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a wani taro da mambobin gudanarwa na Al’ummar Najeriya a Ethiopia, a cikin tattaunawa da aka yi a wajen zama na 38 na Taron Shugabannin Kasashe na Tarayyar Afirka (AU).
Ya jaddada cewa, yayin da Najeriya ke ci gaba da samar da yanayi mai kyau ga kamfanonin waje don zuba jari da aiki cikin ƙasar, yana da kyau da kuma amfanar juna ga sauran ƙasashen duniya su ba da irin wannan tallafi ga kasuwancin Najeriya da ke son faɗaɗa a duniya.
“A cikin shekarar da ta gabata, na wakilci Najeriya a Indonesia kuma na gano cewa akwai kamfanoni 50 na manyan kamfanoni na Indonesia suna aiki a Najeriya amma ba mu da kamfanoni guda biyar na Najeriya da suke aiki a Indonesia. Idan suna son zuwa ƙasarmu don kasuwanci saboda yawan jama’armu da ikon siyan kayayyaki da ayyukansu, to ya kamata a samu tsarin cudeni in cudeka da za a ba da dama ga ‘yan Najeriya; kuma matsalar visa ita ce wannan matsalar da ake samu a Ethiopia da Indonesia. Yana da wahala sosai ga mutane su ba ‘yan Najeriya visa,” in ji shi.
Da yake magana akan batun soke visa na e-visa da Visa-on-Arrival na gwamnati ta Ethiopia ga matafiya daga Najeriya, Idris ya tabbatar da cewa wannan zai mika shine ga Ministan Harkokin Waje don samun cikakken tattaunawa ta diflomasiyya.
Ya kuma nuna damuwarshi da halin da ‘yan Najeriya a Ethiopia suke fuskanta, Ministan ya jaddada cewa manufofin visa tsakanin ƙasashe yawanci suna bisa ka’idar amana ce.
Ya bayyana cewa gwamnatoci suna aiwatar da ƙa’idojin visa a matsayin martani ga manufofin da aka ba wa ‘yan ƙasashensu, yana mai nuna muhimmancin samun yarjejeniyoyi masu daidaito da amfanar juna a cikin tafiyar da harkokin kasashen waje da diflomasiyya.
“Duk wata dangantaka da sauran ƙasashe tana bisa ka’idar amana. Don haka, idan mun ba su Visa-on-Arrival, babu dalilin da zai sa su kasa baza su ba mu Visa-on-Arrival ba” in ji shi.
Ministan ya yi kira ga ‘yan Najeriya da ke zaune a ƙasashen waje su ci gaba da nuna kyakkyawan hali da zama ɗan kasa mai alhakin don inganta matsayin ƙasarsu Nigeria a idon duniya.
Ministan ya yi amfani da wannan dama don sanar da al’ummar Najeriya game da manufofin gwamnatin Tinubu, yana jaddada cewa an samu nasarori masu yawa wajen farfado da tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa, dakile rashin tsaro, da dawo da martabarta ga masu zuba jari a Najeriya.
Idris ya ce Najeriya ta samu kimanin dala miliyan 1.07 a cikin zuba jari na waje (FDI) domin kafa masana’antu na magunguna da kayan magani.
Ya jaddada cewa wannan zuba jari mai muhimmanci yana nuni da farawa na masana’antar magungunan Najeriya ta hanyar sanya ƙasar a matsayin babban mai ruwa da tsaki a samar da magunguna, kara ƙarfin samar da magunguna na cikin gida, rage dogaro da kayayyaki daga waje, ƙirƙirar ayyukan yi, da ƙarfafa sashen lafiya na ƙasar.
Ministan ya bayyana cewa a cikin kwanaki ƙasa da 250, an rarraba Naira biliyan 32 ga ɗalibai a ƙarƙashin Tsarin Lamunin Ɗalibai don tabbatar da cewa babu ɗalibi da zai rasa damar samun ilimi mai kyau saboda rashin kuɗi.
Idris, wanda ya tabbatar da alkawarin gwamnati wajen magance matsalolin tsaro, ya bayyana cewa a cikin shekarar 2024 kawai, hukumomin tsaro sun kashe ‘yan ta’adda da masu laifi 8,000, sun ceto mutane 8,000 da aka sace, kuma sun samu kama mutane 11,600.
Ministan ya bayyana cewa hanyar Kaduna-Abuja, wacce a da take da matsalolin laifi, yanzu an tsaftace ta daga abubuwan laifi, yana mai cewa ingantaccen tsaro a wannan hanya ya kawo babban sauƙi ga masu tafiya.
Idris ya ce gyara wani abu ne mai wahala sosai amma akwai ci gaba mai kyau zuwa wadata ga kowa kamar yadda shugaban kasa ya yi alkawari.
A cikin jawabin sa, Shugaban Al’ummar Najeriya a Ethiopia, Mr. Muideen Alimi, ya ce wani ɓangare na shirin aikinsu shi ne haɗin gwiwa da Hukumar ‘Yan Najeriya a Diaspora don shirya taron ƙwararru kan ƙarfafa ci gaban tattalin arziki ta hanyar cinikayya a cikin Afirka.
Ya roki Najeriya ta tallafa wajen cimma wannan shirin na kafa Babban Bankin Afirka da kuma samun ƙarfi a Cibiyar Kuɗaɗen Afirka.
Taron ya samu halartar Darakta Janar na Hukumar ‘Yan Najeriya a Diaspora, Mrs. Abike Dabiri-Erewa, da sauran manyan jami’an gwamnati.
Rel/Adamu Yusuf
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Bukatar Kasuwancin Duniya Samarda Taimakawa
এছাড়াও পড়ুন:
An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin
Hukumar jin daɗin jama’a ta Jihar Kwara tare da haɗin gwiwar Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya sun kama wasu mabarata a titunan Ilorin, ciki har da wasu da aka samu da kuɗaɗen ƙasashen waje.
Daga cikin waɗanda aka kama akwai wani mabaraci mai suna Musa Mahmud daga Jihar Kano, wanda aka samu da takardar daloli.
Musa Mahmud ya shaida wa manema labarai cewa wani ne ya ba shi takardar Dala a Abuja.
Jami’ai sun bayyana damuwa kan yadda masu bara ke riƙe da kuɗaɗen da ba su dace da yanayin rayuwarsu ba.
Mutuwar majinyata: Asibitin Aminu Kano na roƙon KEDCO ya dawo da wutar lantarki Cire tallafin man fetur shi ne abin da ya dace —Sarki Sanusi II“Za mu bincika asalin waɗannan kuɗaɗen da kuma dalilin da ya sa suke da su,” in ji Adebayo Okunola, shugaban cibiyar gyaran hali a Jihar Kwara.
Jami’an gwamnati sun kwashe kusan mutane 40 daga wuraren da suka haɗa da Tipper Garage, Offa Garage, Tank da Geri Alimi Roundabout.
Jami’an sun ce bakwai daga cikin waɗanda aka kama an taɓa kama su a baya, amma sun koma tituna bayan an sako su.
Kwamishinar jin daɗin jama’a ta jihar, Dakta Mariam Imam, ta ce adadin masu bara da aka kama ya ragu sosai idan aka kwatanta da na baya, inda ta ce suna sauya dabaru don su guje wa kama.
Ta roƙi jama’a da su daina ba wa masu bara kuɗi kai tsaye, su maida gudummawarsu ta hanyar wuraren ibada da gidajen marayu.
Jami’an gyaran hali sun ce za a tilasta wa waɗanda aka kama su yi aikin tsaftace tituna a matsayin horo da kuma darasi.
Wasu daga cikin masu barar sun roƙi gwamnati da ta tausaya musu, ba su da wata hanyar rayuwa sai bara.