Masu kwacen waya sun kashe ma’aikaciyar lafiya a Zariya
Published: 22nd, October 2025 GMT
Wasu da ake zargin masu kwacen waya ne sun kashe ma’aikaciyar jinya a Asibitin Gambo Sawaba da ke Zariya a jihar Kaduna mai suna Hadiza Musa.
Bayanai sun ce marigayiyar it ace mataimakiyar shugabar sashen haihuwa a asibitin.
Majalisa ta soma binciken yadda aka kashe $4.6bn na tallafin kiwon lafiya Gwamna Bala Mohammed ya ƙirƙiri sabbin masarautu 13 a BauchiMijinta, Hamza Ibrahim Idris, wanda ke aiki a Abuja, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kashe matarsa ne a ranar Asabar yayin da take dawowa daga aiki.
“A ranar Asabar, ta kira ni ta ce za ta je wajen gyaran gashi sannan ta ziyarci wani shagon masu magani a Filin Mallawa, Tudun Wada Zariya, kuma na amince.”
“Bayan na tura mata kudi, kiranmu na ƙarshe shi ne lokacin da ta bar wajen sayar da maganin kusan ƙarfe 6 na yamma. Daga nan ban sake samun ta ba.”
“Na ci gaba da kiranta har zuwa safiyar ranar Lahadi, sai na ɗauka cajin wayarta ne ya ƙare.”
Idris, wanda ya farfado daga suma a ranar Talata bayan girgizar da lamarin ya haifar, ya ce daga baya ya gano cewa marigayiyar ta hau babur din haya kusan ƙarfe 6:30 na yamma a ranar Asabar, amma daga bisani wasu suka kai mata hari don su kwace wayarta.
“Alamu sun nuna matse hannayenta aka yi, alamar cewa an tilasta mata yayin da ake ƙoƙarin kwace wayar.”
“Sannan an bugi kanta da ƙarfi, inda jini ya taru a kan nata, wanda nake zaton shine ya jawo mutuwarta.”
Idris ya ce bayan ta suma, sai barayin suka sace wayarta suka jefar da ita a gefen titi kusa da filin Idi na Mallawa a Tudun Wada Zariya.
Ya ce wani mai tausayi da ya same ta ya garzaya da ita zuwa wani asibiti, daga bisani aka tura ta zuwa Asibitin Koyarwa na ABU, Shika, inda aka tabbatar da rasuwarta.
Mijinta ya ce Hadiza ta rasu watanni uku bayan rasuwar ’yar uwarta, wadda ta ɗauki ‘ya’yanta uku a matsayin nata.
“Ta bar ‘ya’yanta uku da kuma waɗanda ta ɗauka bayan rasuwar ’yar uwarta.”
A nasa bangaren, Sakataren Asibitin, Abdulkadir Balele Wali, ya ce Hadiza mataimakiyar shugabar sashen haihuwa ce, kuma ta halarci aiki a ranar Juma’a har zuwa yamma.
Ya bayyana ta a matsayin kwararriya, mai himma da sadaukarwa, wadda ta ba da gudunmawa wajen ceton rayukan jama’a.
Sakataren ya ce rasuwarta babban rashi ne ga asibitin gaba ɗaya.
Mansur Hassan, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sanda a Kaduna, bai samu daga wayar wakilinmu ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kwacen waya Zariya
এছাড়াও পড়ুন:
APC ta rage wa Mata kuɗin tsayawa takara a Borno
Jam’iyyar APC reshen Jihar Borno ta rage wa mata kashi 50 cikin 100 na farashin fom ɗin tsayawa takara, makonni gabanin zaɓen kananan hukumomi da za a gudanar a ranar 13 ga Disamba, 2025.
Da yake sanar da hakan a Maiduguri, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Bello Ayuba, ya ce an ɗauki matakin ne domin magance matsalar ƙarancin kuɗi da ke hana mata shiga siyasa da tsayawa takara.
Yadda Morocco ta kafa tarihin ɗaga Kofin Duniya na FIFA U20 Dembele ya dawo PSG bayan jinyar makonni“Wannan wani ɓangare ne na ƙoƙarin da muke yi na samar da daidaito ga mata a fagen siyasa.
“Muna son ganin mata da yawa suna jagoranci a matakin ƙasa, suna ba da gudummawa da ƙarfinsu wajen gudanar da mulki,” in ji Ayuba.
A cewarsa, “an ƙayyade farashin fom ɗin neman kujerar shugaban ƙaramar hukuma ga maza kan naira miliyan 2, yayin da fom ɗin kansila zai ci ₦500,000, amma mata za su biya rabin wannan adadi — ₦1 miliyan da ₦250,000.”
Ya ƙara da cewa an kafa kwamitocin tantancewa da sasantawa domin tabbatar da cewa zaɓen fidda gwani zai gudana cikin gaskiya da lumana a dukkan ƙananan hukumomi 27 da gundumomi 112 na jihar.
“Za a gudanar da zaɓen fidda gwani a lokaci guda a ƙarshen wannan watan domin guje wa maguɗin zaɓe,” in ji shi.
Ayuba ya jaddada aniyar jam’iyyar ta tabbatar da sahihin zaɓe, inda ya ce Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Borno (BOSIEC) za ta gudanar da babban zaɓen a ranar 13 ga Disamba, 2025.
“Mun himmatu wajen tabbatar da ɗorewar dimokuraɗiyya ta hanyar adalci, daidaiton jinsi, da kuma gudanar da zaɓe cikin lumana,” in ji shi.
“Mata na da matuƙar muhimmanci ga shugabanci, kuma wakilcinsu yana ƙarfafa tsarin mulki.”
Masu sa ido da ƙungiyoyin kare haƙƙin mata sun yaba da matakin jam’iyyar APC, inda suka bayyana shi a matsayin muhimmiyar hanya ta ƙara daidaiton jinsi a siyasar Jihar Borno.
Sun ce rage kuɗin fom ɗin tsayawa takara ga mata ba kawai zai ƙarfafa gwiwar mata masu neman tsayawa takara ba, har ma zai zaburar da ƙananan ‘yan mata su ga shugabanci a matsayin abin da za su iya cimma.
Wannan mataki dai ya yi daidai da kiraye-kirayen ƙasa da ƙasa na ƙara shigar da mata cikin harkokin mulki, tare da ƙarfafa imanin cewa dimokuraɗiyya na bunƙasa ne idan maza da mata suka haɗa kai wajen tsara makomar al’ummarsu.