Red Cross ta kafa cibiyoyin rage haɗurran bala’o’i a makarantun Gombe
Published: 20th, October 2025 GMT
Ƙungiyar Agaji ta Red Cross ta Najeriya (NRCS), tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Italiya, ta kafa cibiyoyin Rage Haɗurran Bala’o’i (Disaster Risk Reduction – DRR) a makarantun sakandare guda biyu a Jihar Gombe, domin inganta shirye-shiryen kare kai daga bala’o’i da kuma ƙarfafa juriya a tsakanin matasa.
Makarantun da suka amfana da wannan shiri su ne Ƙaramar Sakandaren Gwamnati ta Pilot da kuma Sakandaren Gwamnati ta Comprehensive, Deba.
NLC ta sa zare da gwamnati kan yajin aikin ASUU An maka mahaifi a kotu kan cefanar da gidan ɗansa a KanoA yayin bikin ƙaddamar da cibiyoyin, ƙungiyar Red Cross ta raba kayan karatu da suka haɗa da jakunkuna masu ɗauke da bayanai kan DRR, littattafan rubutu, alƙalumma da kayan lissafi ga dalibai, domin ƙara musu ilimi da shiri na kare kai daga haɗurra.
Sakataren Red Cross reshen Jihar Gombe, Murtala Aji Alliyu, ya bayyana cewa manufar wannan shiri ita ce “kama su tun suna ƙanana,” ta hanyar koya musu ilimi mai amfani a fannoni huɗu — wato tsaftar muhalli, bayar da agajin gaggawa, yada bayanai, da kuma shirye-shiryen kare kai daga bala’o’i.
Ya ce ana aiwatar da wannan shiri a jihohi 12 na Najeriya domin rage haɗarin bala’o’i da kuma ƙarfafa tsaron al’umma ta hanyar ilmantar da matasa tun daga makaranta.
“Manufar ita ce a shirya matasa su san yadda za su kare kansu da kuma yadda za su amsa idan wata gaggawa ta faru. Idan aka ba su ilimi, za su zama jakadun sauyi da za su taimaka wajen gina al’umma mai juriya da tsaro,” in ji Alliyu.
A nasa jawabin, wanda ya wakilci Sarkin Deba, Alhaji (Dr) Ahmad Usman, wato Hakimin Bokna, Alhaji Abubakar Usman Tafidan Deba, ya yaba wa Red Cross da Gwamnatin Italiya bisa wannan shiri da ya bayyana a matsayin mai matuƙar amfani.
Ya buƙaci dalibai su ɗauki shirin da muhimmanci tare da haɗa gwiwa da malamansu domin tabbatar da ɗorewarsa.
Mataimakiyar Shugabar Makarantar Gwamnati ta Pilot, Malama Salifatu Abubakar, wacce ta wakilci shugaban makarantar, ta gode wa Red Cross bisa wannan kyakkyawan aiki, tare da kira ga ɗalibai da su yi amfani da ilimin da aka koya musu yadda ya kamata.
Ta ce wannan shiri ba wai ɗaliban kawai zai amfanar ba, har ma zai taimaka wajen yaɗa ilimin kare kai daga bala’o’i da kuma tabbatar da tsaro a faɗin Jihar Gombe.
Wasu daga cikin malamai da ɗalibai sun nuna farin ciki da wannan shiri, inda suka bayyana shi a matsayin abin da ya zo a kan kari kuma mai tasiri sosai.
Sun kuma yi kira ga sauran ƙungiyoyin agaji da na ci gaba da su yi koyi da Red Cross wajen aiwatar da shirye-shiryen da za su taimaka wajen gina al’umma mai juriya da kwanciyar hankali.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ambaliya jihar Gombe kare kai daga wannan shiri
এছাড়াও পড়ুন:
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja
“Wannan mummunan lamari da ya faru a ranar 11 ga Oktoba, 2025, a Wawa Cantonment, Jihar Neja, ya haifar da yanayi mai cike da tashin hankali, inda mazauna sansanin suka shiga cikin mamaki kan yadda irin wannan abin takaici zai iya faruwa,” in ji wani bangare na sanarwar.
A cewar rundunar sojoji, an gano gawarwakin Lance Corporal Femi da matarsa a cikin gidansu dake gini na 15, daki mai lamba 24, Corporals and Below Kuarters, a cikin sansanin.
Binciken farko ya nuna cewa sojan yana kan aiki a lokacin kuma ya nemi izini daga babban jami’i domin ya kula da wasu harkokin kansa kafin ya dawo aiki.
“Rundunar Sojin Nijeriya tana matukar bakin ciki kan wannan lamari, sannan tana taya iyalan, abokan aiki, da abokan marigayin jimami kan wannan babban rashi.
“Rundunar soji kuma tana addu’ar Allah ya jikansu cikin salama,” in ji Nwachukwu.
An ajiye gawarwakin marigayin, sannan an fara gudanar da cikakken bincike don gano dalilan da suka haifar da wannan abin takaici.
“Brigadier Janar Ezra Barkins, kwamandan 22 Armoured Brigade, ya tabbatar wa jama’a cewa sakamakon binciken zai kasance a bayyane kuma za a duba shi sosai, tare da daukar matakan da suka dace don hana faruwar irin wannan lamari a nan gaba,” in ji Nwachukwu.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA