Kungiyar Kare Hakkin Bil-Adama Ta Amnesty Ta Zargi Gwamnatin Tanzaniya Da Musgunawa ‘Yan Adawa
Published: 20th, October 2025 GMT
Kungiyar kare hakkin dan Adama ta Amnesty International ta ce: Gwamnatin Tanzaniya ta wurga yanayin tsoro tare da tsananta danniya gabanin babban zaben kasar
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta zargi mahukuntan Tanzaniya da haifar da yanayin tsoro da kuma tsananta danniya gabanin babban zaben da aka shirya yi a ranar 29 ga watan Oktoba, tare da yin amfani da dabarun yaki da ‘yan adawa, ‘yan jarida, kungiyoyin farar hula, da masu kare hakkin bil’adama.
Amnesty International ta bayyana cewa: Gwamnatin shugaba Samia Hassan na ci gaba da ayyukanta na danniya da suka hada da kama mutane ba bisa ka’ida ba, tilasta bacewar mutane, da kuma kashe-kashen ba bisa ka’ida ba, ba tare da hukunta wadanda suka aikata laifuka ba.
Kungiyar ta yi nuni da yadda ake ci gaba da kai hare-hare kan shugabannin ‘yan adawa, inda aka haramtawa fitattun ‘yan takarar shugaban kasa tsayawa takara, yayin da wasu kamar Tundu Lissu ke fuskantar shari’a kan tuhume-tuhumen siyasa da suka hada da hada baki da furta kalaman karya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Dakarun kare Juyin Musulunci Na Iran Sun Bayyan Shirinsu Na Karfafa Dabarun Hadin Guiwa Da yamen October 20, 2025 October 20, 2025 Kotu A Faransa Ta Yanke Hukumci Zama Gidan Yari Ga Tsohon Shugaban Kasar Nicola Sarkozi October 20, 2025 Isra’ila Ta Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta Sau 80 Ta Kashe Mutane 97 Ta Jikkata 230 October 20, 2025 Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Mukaman Gwamnatin Tinubu inji Shugaban FCC October 20, 2025 Grossi: Za a iya warware batun Shirin nukiliyar Iran ne kawai ta hanyar diflomasiyya October 20, 2025 Trump: Shugabanin Hamas ba su da hannu a kisan sojojin Isra’ila 2 a Gaza October 20, 2025 Iran Da Azerbaijan Suna Gudanar Da Atisayen Hadin Guiwa Na Sojojin Ruwa A Tekun Caspian October 20, 2025 Gwamnatin Yamen Tana Tsare Da Ma’aikatan MDD 50 Ta Kuma Kwace Kayakin Aikinsu October 20, 2025 Gwamnatin Colombia Ta Bukaci Bayani Daga Amurka Kan Kashe Wani Dan Kasar A Tekun Carabian October 20, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dokokin Akwa Ibom ta yi fatali da ƙudurin neman hana cin naman kare
Majalisar Dokokin Jihar Akwa Ibom ta ƙi amincewa da wani kudiri da ya nemi haramta ci da sayar da naman kare a jihar.
Kudirin, wanda ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Etinan, Uduak Ekpoufot ya gabatar ranar Talata, bai samu ko da dan majalisa daya da ya mara masa baya ba.
Yau Majalisar Dattawa za ta tantance sabon Ministan Tsaro Mako mai Majalisa za ta kada ƙuri’a kan ƙudurin ƙirƙirar sabbin jihohiJaridar nan ta gano cewa Uduak ya roki majalisar da ta yi la’akari da matsalolin kiwon lafiya da ke tattare da cin nama kare, yana gargadin cewa yadda ake yanka dabbobin ba tare da tsafta ba na iya jefa masu cin nama cikin haɗarin kamuwa da cututtuka irin su rabies, salmonella, trichinella da sauran kwayoyin cuta.
Ya kuma bayyana hanyoyin da ake amfani da su wajen kashe karnuka a kasuwancin a matsayin na rashin tausayi.
Duk da hujjojin da ya gabatar, babu wani ɗan majalisa da ya goyi bayan kudirin, lamarin da ya tilasta wa kakakin majalisar ya yi hukunci da cewa an ƙi amincewa da shi.
Akwai dai sassa da dama na Najeriya, musamman a kudancin kasar nan da ma wasu sass ana Arewacin kasar da ke cin nama kare.
A farkon wannan shekara, wani masani kan namun daji, Edem Eniang, ya ce mata ’yan Najeriya suna cin nama kare fiye da maza, bisa wasu al’adu da ke ɗaukar cewa naman yana inganta laushin fata.
Ya ce wannan al’ada ta fara fitowa fili ne a wata lakca da wani masanin dabbobi, Richard King, ya gabatar.
Eniang ya kuma nuna damuwa kan raguwar adadin karnuka saboda yawan cin naman su da ake yi.
Ya ba da misalan wasu lamarin da suka faru a Ibeno da Oron a jihar ta Akwa Ibom, inda aka sace karnuka aka yanka su don abinci, cikin su har da wata karya mai shayarwa da ’ya’yanta ƙanana.