A gefe guda kuma ta roƙi jama’a su yi watsi da rahoton jaridar, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da aikinta cikin gaskiya da amana.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Da ɗumi-ɗuminsa ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta October 22, 2025 Labarai Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal October 22, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe October 22, 2025.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu Ya Nemi Alkalai Su Kara Kaimi Wajen Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Alkalan Najeriya su kasance masu gaskiya, rikon amana da tsoron Allah wajen yanke hukunci. Ya ce duk wata al’umma tana fara rushewa ne idan bangaren shari’a ya lalace.

Ya bayyana cewa gwamnati na kokarin inganta walwala da albashin Alkalan domin karfafa ikon cin gashin kansu.

Da yake bude taron bita na EFCC da NJI a Abuja, Shugaban  wanda Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta  ya ce adalcin Alkalai ne ginshikin ci gaban kasa.

Ya nuna damuwa kan yadda ake jinkirta shari’o’in manyan laifukan rashawa, yana mai cewa an fi hanzarta shari’ar masu laifin yanar gizo.

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa ba a taba kare kowa saboda siyasa a gwamnatinsa ba, inda ya bayyana cewa EFCC ta samu nasarar gurfanar da mutane sama da 7,000 tare da karbo kadarori fiye da Naira Biliyan 500 cikin shekaru biyu.

Ya bukaci Alkalan su ci gaba da koyon sabbin dabaru, musamman wajen shari’o’in yanar gizo da laifukan kuɗi, tare da tunatar da su cewa cin hanci yana shafar kowa.

A nata bayanin Babbar Alkalin Najeriya, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta bukaci Alkalan su tabbatar da yin adalci ba tare da jinkiri ko son zuciya ba.

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya yaba da hadin kan da Alkalan je basu, yana mai cewa nasarorin da aka samu sun nuna jajircewa wajen yaki da cin hanci da rashawa.

 

Daga Bello Wakili

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisa Ta Tabbatar Da Yusuf A Matsayin Sabon Shugaban NPC, Wasu 2 A Matsayin Kwamishinoni
  • Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da Suka Kashe Malamin Jami’a
  • Tinubu Ya Nemi Alkalai Su Kara Kaimi Wajen Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa
  • Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja
  • Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC
  • Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi
  • Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna
  • An saki Ɗan Uwa Rano bayan tsare shi kan zargin ɓata sunan hadimin gwamnan Kano
  • ’Yan sanda sun tsare ɗan jarida kan zargin ɓata sunan hadimin gwamnan Kano