Jihar Kwara Ta Ware Naira Biliyan 8 Don Biyan Haƙƙin Ma’aikatan Da Suka Yi Ritaya
Published: 22nd, October 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Kwara ta ware kimanin Naira Biliyan 8 da miliyan dari daya domin biyan haƙƙin fansho da giratuti na ma’aikatan jiha da na kananan hukumomi da suka yi ritaya.
Kwamishinan Kuɗi na Jihar, Dakta Hauwa Nuhu, ce ta bayyana haka a yayin taro da ma’aikatun gwamnati karo na uku, wanda aka gudanar a zauren taro na ma’aikatar kuɗi a Ilori.
A cewarta, za a raba Naira Biliyan biyar da miliyan dari shida ga tsoffin ma’aikatan jiha a matsayin giratuti, yayin da aka ware Naira Biliyan biyu da miliyan dari biyar domin tsoffin ma’aikatan kananan hukumomi.
Dakta Nuhu ta jaddada cewa gwamnatin jiha za ta ci gaba da biyan fansho da giratuti a hankali domin tabbatar da cewa sauran ayyukan ci gaban jama’a ba su tsaya ba.
Ta bayyana cewa adadin giratuti da fansho ya ninka saboda aiwatar da sabon tsarin albashi na Naira Dubu Talatin da Naira Dubu Saba’in, tare da daidaiton da aka yi ga masu ritaya.
Kwamishinar ta kuma tabbatar da cewa babu wani tsohon ma’aikacin karamar hukuma ddake bin gwamnati bashi, sai waɗanda suka ƙi bayyana a lokacin tantancewar da aka gudanar a dukkanin kananan hukumomi 16 na jihar.
Ali Muhammad Rabi’u
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwara Naira Biliyan
এছাড়াও পড়ুন:
Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta Kare Kasafin Kudin 2026 a Gaban Majalisa
Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta ce za ta gudanar da aikin shigar da sabbin dokokin jihar cikin kundin bayanan dokoki da aka yi a jihar.
Babban Sakataren ma’aikatar, Barrister Lawan D. Baba, ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin sabuwar shekara ta 2026 a gaban kwamatin harkokin shari’a na majalisar dokokin jihar Jigawa.
Barrister Lawan D. Baba ya bayyana cewa ma’aikatar ta yi kiyasin kashe naira milyan 311 da dubu 847 a kasafin kudin sabuwar shekara.
Babban sakataren yace za su mayar da hankali ga batun kawar da jinkiri wajen gudanar da shari’o’i domin karfafa matakan samun shari’a cikin sauri ga al’ummar jihar.
A nasa jawabin, Shugaban kwamatin harkokin shari’a na majalisar dokokin jihar Jigawa kuma wakilin mazabar Hadejia, Barrister Abubakar Sadiq Jallo, ya jaddada bukatar wanzuwar dangantakar aiki tsakanin kwamatin da bangaren shari’a domin inganta aikin shari’a a kotu.
Kazalika, magatakardar Babbar kotun jihar da sakataren hukumar kula da ma’aikatan shari’a da kuma sakataren hukumar bada tallafin shari’a su ma sun kare na su kiyasin kasafin kudaden a gaban kwamatin.