Me Aka Gano Kan Makomar Tattalin Arzikin Kasar Sin Daga Karuwar 5.2% Na Tattalin Arzikinta?
Published: 21st, October 2025 GMT
Har ma abun da ba kasafai ake gani ba, tattalin arzikin Sin yana cike da karfin tinkarar duk wani hadari da ka iya kunno kai. Ba sabunta kayayyaki kirar kasar da kara musu inganci kadai aka samu ba, har ma abokan cinikin kasar a ketare suna ta kara yawa.
A jiya Litinin ne aka bude cikakken zama na 4 na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 a nan Beijing, inda za a tattauna da kuma ba da shawarwari kan shirin shekaru biyar-biyar na 15 na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da Karfin Iska A Karkashin Ruwa
Kasar Sin ta kammala ginin wata cibiyar adana bayanai, irinta ta farko dake karkashin teku kuma mai amfani da lantarki daga karfin iska wato (UDC), wanda aka samar a birnin Shanghai na gabashin kasar. Cibiyar ta zama wani mizanin inganci ta fuskar samar da kayayyakin sarrafa bayanai.
Cibiyar UDC wadda ke da mazauni a yankin Lingang na Shanghai, wanda yanki ne na gwajin cinikayya cikin ‘yanci, ta samu jarin yuan biliyan 1.6, kwatankwacin kimanin dala miliyan 226, kuma tana da karfin lantarki da ya kai megawatt 24.
A cewar kwamitin gudanar da harkokin yankin Lingang, kammala aikin wata babbar nasara ce ga hadadden aikin samar da cibiyar UDC da kuma makamashi mai tsafta dake cikin teku. Ya kuma nuna yadda aka samar da wani tsarin sarrafa bayanai mai kare muhalli da kuma yadda kasar ke amfani da lantarkin da aka samar daga iska. (Mai fassara: Fa’iza)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA