Muna Samun Gagarumin Cigaba Wajen Dawo Da Zaman Lafiya A Zamfara-Gwamna Lawal
Published: 21st, October 2025 GMT
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada cewa yaki da matsalar rashin tsaro a jihar nauyi ne na gwamnatinsa da sauran masu ruwa da tsaki, da ma al’umma baki.
Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Litinin, ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake jagorantar taron majalisar zartarwa ta jihar karo na 18 da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Gusau.
Sanarwar ta ce, majalisar ta tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi jihar, ciki har da tsaro, ilimi, kiwon lafiya, da cigaban ayyukan raya kasa.
Dr. Lawal ya tunatar da mambobin majalisar muhimmancin hadin kan su wajen yaki da rashin tsaro a karkashin wannan gwamnati.
“Muna samun gagarumin ci gaba wajen dawo da zaman lafiya a mafi yawan sassan jihar. An raunana karfin ‘yan bindiga fiye da yadda ake gani a baya,” in ji shi.
Ya bukaci mambobin majalisar su kasance masu saurin daukar mataki, tare da kusanci da al’ummarsu da zababbun shugabannin kananan hukumomi, da kuma ci gaba da bayar da rahoton halin tsaro ga Kwamishinan Tsaro na Jihar.
“Haka kuma, mu ci gaba da addu’a domin shahidanmu da suka rasa rayukansu wajen kare jama’a,” in ji gwamnan.
Gwamna Lawal ya kuma shawarci mambobin majalisar da su ci gaba da kyakkyawar dangantaka da sauran jami’an gwamnati da zababbun wakilai domin tabbatar da ingantacciyar gwamnati da samar da ayyuka ga jama’a.
AMINU DALHATU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar da Wutar Lantarki a Yankunan Kananan Hukumomin Jihar
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin Jihar Jigawa ta gudanar da bikin bude tayin bada kwangilar samar da wutar lantarki a wasu garuruwa dake kananan hukumomin Jihar.
A lokacin da yake jawabi a yayin gudanar da bikin daya gudana a sakatariyar Jihar dake Dutse, Shugaban hukumar, Injiniya Zubairu Musa ya bayyana cewar tayin bada kwangilar samar da wutar da gyara da fadadawa gami da kammala wasu ayyukan za a yi sune a garuruwa 17.
Kazalika, Injiniya Zubairu Musa, yace wannan na daga cikin kudirori 12 na Gwamna Umar Namadi na hada wutar lantarki a kanana da matsakaitan garuruwan jihar da basu da wuta.
A cewar sa, garuruwan da za’a samar da wutar lantarkin a Dutse sun hada da Sabuwar Takur da sabuwar hanyar rukunin gidajen gwamnati na Godiya Miyetti da rukunin gidaje na Bulori da kuma makaranta ta musamman ta Mega.
Shugaban hukumar wanda ya samu wakilcin Sakataren hukumar, Barrista Auwalu Yakubu, yace sauran su ne garin Wurno a karamar hukumar Birnin Kudu da samar da wutar lantarkin a sabbin rukunin gidajen gwamnati na Birnin Kudu da Dutse da Ringim da Babura tare da Kazaure da kuma Gumel.
Sai samar da wutar lantarkin a garin Tsamiyar kwance a karamar hukumar Babura da samar da wutar lantarki a hanyar Nguru da Biranen Hadejia da Kafin Hausa a kananan hukumomin Hadejia da Kafin Hausa.
Ya kara da cewar sai gyara wutar lantarki a garuruwan Addani da Ruruma da Ringim a karamar hukumar Yankwashi da kammala aikin samar da wutar lantarki a garuruwan Tage, Siga, Garin-Wakili, Fandum, Gauta, Ona, Baturiya da Barma-Guwa a karamar hukumar Kirikasamma.
Injiniya Zubairu yace sai kuma samar da wutar lantarki a garin Gwari a Miga da kuma garin Agura a karamar Kafin Hausa.
Sauran sun hada da kammala aikin samar da wutar lantarki a Dandidi a Gagarawa da Matsa a karamar hukumar Malam-Madori da kuma aikin fadada samar da wutar lantarki a Jami’ar Khadija dake garin Majia a karamar hukumar Taura.
A nasa jawabin, wakilin hukumar tantance ayyukan kwangila ta jihar Jigawa, ya ja hankalin ‘yan kwangilar da suka nuna sha’awarsu ta gudanar da aikin da su gudanar da aiki mai inganci, tare da bin dokoki da ka’idojin gudanar da ayyukan kwangila na hukumar.