Jihohin Jigawa, Katsina Da Kano Za Su Kaddamar Da Asusun Wutar Lantarki Mafi Girma A Najeriya
Published: 20th, October 2025 GMT
Jihohin Jigawa, Katsina da Kano sun amince da hadin gwiwa kan kasuwar wutar lantarki ta jihohi uku, tare da samun kaso a kamfanin Future Energies Africa (FEA), wanda shi ne ke da hannun jari mafi girma a Kano Electricity Distribution Company (KEDCO).
Kwamishinan wutar lantarki na jihar Jigawa, Injiniya Surajo Musa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse.
Ya ce gwamnonin jihohin ukun sun cimma wannan matsaya ce a birnin Marrakech, kasar Morocco, yayin taron kolin manyan jami’ai kan samar da wutar lantarki.
Injiniya Surajo Musa ya kara da cewa a yayin taron, jihohin Kano da Katsina sun amince da yin hadin gwiwa da jihar Jigawa wajen samun kaso a Future Energies Africa, domin karfafa tsare-tsaren ci gaban KEDCO.
“Jihohin uku tare da kamfanin Future Energies Africa za su kaddamar da wani asusun samar da wutar lantarki na musamman wanda shi ne irinsa na farko da ake sa ran zai kai Naira Biliyan 50 a matakin farko, domin hanzarta samar da wuta a cikin jihohin uku,” in ji shi.
Sanarwar ta kara da cewa jihohin za su duba hanyoyin da Dokar Wutar Lantarki (Electricity Act) ta tanada, domin yin hadin gwiwa kan kasuwar wutar lantarki ta jihohin uku, inda kowanne zai amfana.
Ya ce FEA tare da gwamnonin jihohin uku za su rika gudanar da taron kasa da kasa sau daya a shekara, sannan su rika ganawa duk bayan watanni uku domin duba ci gaba da karfafa dangantakar kasuwar wutar lantarki ta Arewa maso Yamma.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa wutar lantarki
এছাড়াও পড়ুন:
Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xinjiang Ta Janyo Karin Jari A Rubu’i Uku Na Farkon Shekarar Nan October 19, 2025
Daga Birnin Sin Tawagar Likitocin Sin Ta Samar Da Tallafin Jinya Ga Kananan Yara Kyauta A Togo October 19, 2025
Daga Birnin Sin An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin October 18, 2025