Gwamna Lawal Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Yaƙi Da Ƙalubalen Tsaro
Published: 20th, October 2025 GMT
Gwamnan ya kuma buƙaci mambobin majalisar da su kasance masu aiki da faɗakarwa, su kasance kusa da jama’ar yankunansu da kuma shugabannin ƙananan hukumomi. Ya umarce su da su riƙa isar da rahotanni na yau da kullum ga Kwamishinan Tsaro, tare da yin addu’a ga waɗanda suka rasa rayukansu wajen kare al’umma da zaunar da zaman lafiya a jihar.
Bugu da ƙari, Gwamna Lawal ya ƙarfafa mambobin majalisar su ƙara haɗin kai da sauran jami’an gwamnati domin tabbatar da ingantacciyar tafiyar da al’amuran mulki da gudanar da ayyukan ci gaba cikin nasara.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Zanga-zanga: Jami’an tsaro sun kafa shingayen bincike a wajen Abuja
Rundunar sojin da ke tsaron shugaban ƙasa da ’yan Sanda sun kafa shingayen bincike a manyan hanyoyin shiga Abuja da fata Abuja.
Matakin ya biyo bayan zanga-zangar neman a sako jagoran ƙungiyar ta’addanci ta IPOB, masu neman ɓallewa daga Najeriya, Nnamdi Kanu.
Zanga-zangar na zuwa ne a yayin da ake zargin yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, har aka tsare wasu manyan sojoji aƙalla 16 da ake zargin wani tsohon gwamna ya ɗauki nauyinsu juyin mulkin suka shirya aiwatarwa.
Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta musanta zargin alhali wasu majiyoyi masu tushe sun tabbatar mana da gaskiyar zargin yunƙurin.
Juyin mulki: Ana zargin tsohon gwamnan da ɗaukar nauyin sojojin Najeriya Jami’an tsaro sun buɗe wa masu zanga-zangar Nnamdi Kanu wuta a AbujaA safiyar Litinin ɗin nan ne Omoyele Sowore, jagoran tafiyar #RevolutionNow, ya jagoranci zanga-zangar neman sakin Nnamdi Kanu a sassan Abuja.
Zanga-zangar ta haddasa cunkoson ababen hawa a wurare da dama da suka hada da yankin Bwari, Zuba, Nyanya da sauran hanyoyin shiga birnin Abuja.
Musamman, an rufe hanyar da ke haɗa Bwari da Tsakiyar Birni a yankin War College da ke Ushafa, da kuma Dutse-Sokale, abin da ya sa ma’aikatan gwamnati da dama suka maƙale a hanya.
Da fari, jami’an tsaro sun taƙaita tsauraran matakai ne a wuraren da suka haɗa da Fadar Shugaban Kasa, Majalisar Tarayya, Kotun Daukaka Kara, Hedikwatar ’Yan Sanda ta Kasa, da kuma Dandalin Eagle Square.
Sai dai wata majiya daga hukumar tsaro ta shaida wa wakilinmu cewa faɗaɗa shingayen zuwa unguwannin da ke wajen birnin ya zama dole domin hana “’yan kutse daga waje” shiga cikin birnin.
“Yanzu ana binciken kowace mota da ke shigowa cikin birni. Wannan mataki ne domin bambance masu neman tayar da fitina da ’yan ƙasa na gari. Ba za mu yarda a samu tashin hankali a cibiyar gwamnati ba,” in ji majiyar.
Wani jami’in tsaro ya kuma bayyana cewa bayanan sirri sun nuna masu zanga-zangar na sake tsara dabaru tare da yiwuwar shigo da wasu matasa zauna-gari-banza domin tayar da da tarzoma.
Wani ma’aikacin gwamnati, Isaac Babalola, ya shaida wa wakilinmu cewa ya koma gida bayan ya maƙale na tsawon lokaci a cunkoson motoci a kusa da War College Camp da ke Ushafa.
“Ana tsayawa ana binciken kowace mota sosai, abin ya haddasa cunkoso mai tsanani,” in ji shi.
Haka kuma, wasu direbobi da suka taso daga Mararaba–Nyanya sun bayyana takaici, suna cewa sun karaya saboda ba su shirya irin wannan tsaiko ba.