Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Aikin Hanya Akan Kudi Sama Da Naira Biliyan 4
Published: 21st, October 2025 GMT
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya kaddamar da aikin gina hanyar Babban Sara zuwa Malam Bako zuwa Shabaru zuwa Kirgi zuwa Albasu, mai tsawon kilomita 28.2, a Karamar Hukumar Sule Tankarkar,wanda kudinsa ya kakaNaira Biliyan 4.47, a ci gaba da shirin Gwamnati da Jama’a.
Aikin hanyar zai hada fiye da kauyuka 60 tare da karfafa harkokin kasuwanci da zamantakewa a yankin.
Haka kuma, gwamnan ya bude sabuwar cibiyar kula da lafiya ta farko, da makarantar Tsangaya ta zamani, da kuma rukunin samar da ruwa a yankin.
Gwamna Namadi ya bayyana cewa shirin Gwamnati da Jama’a hanya ce ta karfafa gaskiya, bayyana ayyuka da kuma baiwa jama’a damar fadin ra’ayoyinsu.
“Mun zo ne mu nuna abin da muka cimma cikin shekara biyu, mu kuma saurari jama’a domin mu kara gyara inda ya kamata,” in ji shi, yana mai jaddada cewa hakikanin gwamnati ita ce wadda ke bautar al’umma.
Ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa gyare-gyaren da ke karfafa tattalin arzikin jihohi da kananan hukumomi, inda ya bayyana cewa Jihar Jigawa na daga cikin jihohi shida da aka zaba don fara shirin ciyar da dalibai na National Home-Grown School Feeding Programme da aka farfado da shi.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya yaba da shirin, yana mai cewa ya zama abin koyi ga sauran jihohi wajen aiwatar da mulki tare da jama’a.
A nata jawabin, Minista a ma’aikatar Ilimi, Farfesa Suwaiba Said Ahmad, ta jinjinawa Gwamna Namadi bisa manyan ayyukan cigaba da ke canza rayuwar jama’a.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Aikin Hanya Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Bayan Kauce Hanya, Jirgi Ya Afka Cikin Teku A Hong Kong
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja October 20, 2025
Labarai Wani Mai Taɓin Hankali Ya Kashe Mutum 1, Ya Raunata 3 A Taraba October 20, 2025
Manyan Labarai ‘Yansanda Sun Kama Alburusai 400 A Delta October 20, 2025