SUBEB Ta Gudanar Da Jarabawa Ga Malaman Da Ke Neman Mukaman Sakatarorin Ilimi A Jigawa
Published: 20th, October 2025 GMT
Hukumar Kula da Ilimin Firamare ta Jihar Jigawa (SUBEB) ta gudanar da zagaye na biyu na jarabawa ga malamai da ke neman mukamin sakatarorin ilimi a kananan hukumomi 27 na jihar.
Shugaban hukumar, Farfesa Haruna Musa, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse.
A cewarsa, malamai 129 ne suka zauna jarabawar daga cikin 159 da suka rubuta zagaye na farko a Jami’ar Tarayya ta Dutse.
Farfesa Musa ya kara da cewa tambayoyin jarabawar sun shafi matsalolin da makarantun da ke karkashin hukumar ke fuskanta da kuma hanyoyin warware su.
Ya ce malamai za su kuma fuskanci jarabawar kwamfuta domin a tantance iya rubuta rahotanni da aikawa da saƙonni ta hanyar zamani.
Gidan Radio Najeriya ya ruwaito cewa an gayyaci malamai daga jami’a domin su sa ido kan jarabawar da kuma tantance waɗanda suka fi cancanta don mukamin sakataren ilimi.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Mahukunta sun kai samame wani gidan shan Shisha a Kano
Mahukunta sun kai samame tare da rufe wani gidan shan Shisha da ke kan titin Abdullahi Bayero a cikin ƙwaryar birnin Jihar Kano.
Bayanai sun ce wata rundunar haɗin gwiwa ce ta kai samamen da ta ƙunshi jami’an ukumar Kula da Yawon Buɗe Ido da kuma na Hukumar Hana Sha da Fataucin Ƙwayoyi (NDLEA) reshen Jihar Kano, da Hukumar ’Yan Sanda a Jihar Kano.
An tsinci gawar wata mata da aka yi wa kisan gilla a Yobe An kama sojoji 20 kan yunƙurin kifar da gwamnatin TinubuWannan na cikin wata sanarwa da Hukumar Yawon Buɗe Ido ta Jihar Kano ta fitar a ranar Asabar, inda ta ce jami’an NDLEA sun kama wasu kayan maye da kuma wasu mutane da ake zargi da shaye-shaye a wurin.
Hukumar ta ce wannan aikin wani bangare ne na yunƙurin gwamnati a fagen yaƙi da matsalar shaye-shaye da kuma ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a ko’ina a faɗin jihar.
Shugaban Hukumar Yawon Buɗe Ido ta Jihar Kano, Alhaji Tukur Bala Sagagi ya jaddada cewa akwai dokar hana shan shisha a Jihar Kano, don haka gwamnati ba za ta lamunci karya wannan doka ba.