EFCC ta ƙwato fiye da naira biliyan 500 a shekara biyu — Shetima
Published: 21st, October 2025 GMT
Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya bayyana cewa, Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziki ta’annati ta samu nasarar tara dukiyar da ta haura naira biliyan 500 a tsawon shekaru biyu na gwamnatinsu.
Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu, ya bayyana haka ne a yayin wani taron bita da ƙara wa juna sani na alƙalai da Hukumar EFCC tare da haɗin gwiwar Hukumar Shari’a ta Najeriya (NJC) suka shirya a birnin Abuja.
Shettima ya buƙaci alƙalai da sauran ma’aikatan ɓangaren shari’a da su ƙara ƙaimi tare da yin aiki bisa gaskiya da adalci, yana mai gargaɗin cewa ana fara samun matsala ne a ƙasa da zarar masu riƙe da amanar hukunci suka fara tauye haƙƙin mai haƙƙi.
Mataimakin shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsu ba ta tsoma baki a harkokin shari’a, yana mai cewa “mun ba ɓangaren shari’a da hukumomin yaƙi da cin hanci damar gudanar da ayyukansu ba tare da katsalandan ba,” in ji shi.
Da yake bayyana irin nasarorin da aka samu a fannin yaƙi da cin hanci da rashawa, Shettima ya ce EFCC ta samu nasarar ƙwato fiye da naira biliyan 500 a cikin shekara biyu da suka gabata.
“A cikin shekara biyu na wannan gwamnatin, EFCC ta samu nasarar gurfanar da sama da mutum 7,000 a gaban kotu, sannan ta ƙwato dukiyar da ta haura naira biliyan 500,” in ji Shettima.
Ya ƙara da cewa, kuɗaɗen da aka ƙwato ana amfani da su ne a shirye-shiryen tabbatar da walwalar al’umma, ciki har da shirin bayar da bashi ga ɗalibai da sauran manufofin tallafa wa jama’a.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: naira biliyan 500
এছাড়াও পড়ুন:
Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da Suka Kashe Malamin Jami’a
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ‘Yansanda Sun Kama Alburusai 400 A Delta October 20, 2025
Manyan Labarai Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi October 19, 2025
Manyan Labarai Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna October 19, 2025