An Yi Fashi Da Makami A Gidan Adana Kayan Tarihin ” Louvre” Na Kasar Faransa
Published: 21st, October 2025 GMT
Da misalin karfe 9;30 na safiyar ranar Lahadi ne dai wasu mutane masu dauke da makamai su ka kutsa cikin gidan adana kayan tarihi na ” Louvre” inda su ka yi awon gaba da kayayyaki masu daraja.
Ministun harkokin cikin gidan Faransa da na al’adu sun ce; barayin sun dauki mintuna 4 zuwa 7 kadai su ka yi satar.
Da dama daga cikin kafafen watsa labarun kasar ta Faransa sun bayyana abinda ya faru da cewa ya yi kama da abinda ake gani a cikin fina-finai.
Satar dai ta jawo cece-kuce a tsakanin ‘yan siyasar kasar, yayin da kafafen watsa labaru suke yi wa lamarin isgili ta hanyar yin zane-zane.
Jaridar “La Progress” ta amabci cewa a baya ma an taba satar fitaccen zanan “Moniliza” da Leonardo Davinci na kasar Italiya ya zana.”
A wani labarin daga kasar Faransa tsohon shugaban Kasar Nicolay Sarkozi ya fara zaman Kurkuku Na Shekaru 5
A yau Talata ne za a fara kidaya lokacin zaman kurkuku na tsawon shekaru 5 bayan da wata kotu ta same shi da laifin karbar kudaden da ya yi yakin neman zabe daga tsohon shugaban kasar Libya Mu’ammar Kaddafi.
Gabanin shigarsa gidan yarin, Sarkozy ya fada wa jaridar “ La Tribune Dimanche” cewa; Ba na tsoron zaman kurkuku, zan ci gaba da zama cikin izzata.”
An dauki shekaru masu yawa ana yin shari’ar tsohon shugaban kasar ta Faransa, Nicolay Sarkozi bisa zargin da aka yi masa na cewa ya karbi kudaden da ya yi yakin neman zabe da su daga tsohon shugaban kasar Libya Mu’ammar Kaddafi a 2007.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Yemen : An yi jana’izar babban hafsan sojin kasar Shahid al-Ghamari a Sana’a October 21, 2025 Iran da Iraki sun bukaci duniya da ta dakatar da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza October 21, 2025 Equatorial Guinea ta zargi Faransa da karan-tsaye wa zaman lafiya a kasar October 21, 2025 Faransa : Sarkozy, ya fara zaman gidan yari na shekara 5 October 21, 2025 Gaza : Falasdinawa 97 sojin Isra’ila suka kashe tun bayan cimma yarjejeniya October 21, 2025 Iran Da Faransa Zasu Yi Musayar Fursinoni, Esfandiari Tana Daga Cikin Wacce Za’a Sallama October 21, 2025 Gaza: Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa 57 A Cikin Sa’o’i 24 Da Suka Gabata October 21, 2025 Kakakin Majalisar Dokokin Kasar Lebanon Ya Ce Babu Wata Tattaunawa Da HKI October 21, 2025 Tom Barak: Saudiyya na gab da kulla alaka da Isra’ila a hukumance October 21, 2025 Kremlin: Rasha a shirye take don fadada hadin gwiwa da Iran a dukkanin fannoni October 21, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: tsohon shugaban kasar
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Yamen Tana Tsare Da Ma’aikatan MDD 50 Ta Kuma Kwace Kayakin Aikinsu
Gwamnatin kasar Yemen ta kama wasu ma’aikatan MDD a ranar Lahadi a cikin kasar a wani sumamen da Jami’an tsaron kasar suka yi kan sansaninsu, inda suka kama ma’aikatan suka kuma kawace kayakin aikinsu.
Shafin yada labarai na Yanar Gizo ArabNews na kasar Saudiya sun ya nakalto kamfanin dillancin labaran Associated Press yana cewa a jiya Lahadi ne jami’an tsaron yemen suka kama yemenawa 11 da kuma yan kasashen waje 15 a wani wurin aikinsu a unguwar Hada na birnin San’a babban birnin kasar.
Labarin ya kara da cewa sun sallami 11 daga cikinsu bayan tambayoyi masu yawa. Jean Alam kakakin MDD a yemen ya tabbatar da wannan labarin ya kuma kara da cewa hukumarsa ta tuntubi jami’an gwamnati a San’a don ganin an sake dukkan ma’aikatansu da ake tsare da su yemenawa ko yan kasashen waje. Sannan jami’an tsaro su kawo karshen farwa cibiyoyin hukumar da ke birnin san’a.
Labarin ya kara da cewa jami’an MDD da aka kama sun hada da na ‘World Food Programme, UNICEF da kuma naofishin mai kula da ayyukan MDD a kasar da ya shafi aikin jin kai da kuma bada agaji.
Gwamnatin san’a dai ta bayyana cewa tana zakulo masu aikin leken asirine a cikin ma’aikatan wadan nan hukumomi na MDD. Labarin ya kara da cewa a halinyanzu akway ma’aikatan hukumomin majalisar kimani 50 a tsare. Sannan mafi yawansu yan kasar ta Yemen ne, wadanda take zarginsuda aikiwa kasashen waje.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gwamnatin Colombia Ta Bukatci Bayani Daga Amurka Kan Kashe Wani Dan Kasar A Tekun Carabian October 20, 2025 An Fara Kidayar Kuri’un Zabukan Kananan Hukumomi 16 Da Aka Yi A Libya October 19, 2025 Araqchi: Iran Da Kasashen China Da Rasha Suna Shirin Kawo Karshen Takunkuman Turai October 19, 2025 Miliyoyin Mutanen Amurka Sun Yi Zanga-zanagr Nuna Kin Jinin Donald Trump October 19, 2025 Sheikh Na’im Kassim Ya Mika Sakon Ta’aziyyar Shahadar Gumari Na Kasar Yemen Ga Sayyid Husi October 19, 2025 Sojojin HKI Sun Shiga Cikin Yankin Qunaidhara Na Kasar Syria October 19, 2025 Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Keta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta October 19, 2025 Hamas ta yi Allah wadai da Isra’ila kan keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta October 19, 2025 An gudanar da zanga-zanga a sassa da dama na Amurka October 19, 2025 MDD : “Zai dauki lokaci” kafin a rage yunwa a Gaza October 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci