UNICEF Ya Tabbatar Da Anniyar Na Karfafa Jagorancin Mata A Fannin Ilimi
Published: 22nd, October 2025 GMT
Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya tabbatar da aniyarsa ta inganta daidaito tsakanin maza da mata da kuma karfafa jagorancin mata a fannin ilimi a Jihar Jigawa.
Shugabar Ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Mohammed, ya bayyana hakan a wani taron da HiLWA ta shirya tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai (EU) a Dakin Taro na Manpower Development Institute.
Ya ce bincike ya nuna cewa ko da yake mata su ne mafi rinjaye a aikin koyarwa a Jigawa, suna da kaso 14 bisa 100 ne kacal a mukaman shugabanci, kamar shugabar makaranta ko mataimakiya. Wannan, a cewarsa, yana takaita gudunmawar mata wajen tsara manufofi da ci gaban ilimi.
Rahama Ya bayyana cewa matsalolin al’adu, tsarin aiki, da rashin damar samun jagoranci na hana mata ci gaba, yana mai cewa idan mata suka jagoranci makarantu, ana samun kyakkyawar gudanarwa da karin nasara ga dalibai, musamman ‘yaya mata.
Ya ce a karkashin Shirin Jinsi na UNICEF (2022–2025), za a ci gaba da dakile matsalolin da ke hana mata cigaba, samar da tsarin daukar aiki da karin girma bisa adalci, da kuma gina hanyoyin koyarwa ga mata masu neman mukaman shugabanci.
UNICEF ya jaddada cewa zai ci gaba da aiki tare da HiLWA, da EU, da Gwamnatin Jigawa domin samar da manufofi da za su karfafa mata a harkar ilimi.
Ya ce karfafa jagorancin mata ba batun adalci ba ne kadai, muhimmin mataki ne na gina kyakkyawar makomar yara.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri ta Jigawa Ta Bada Kiyasin Kasafin Kudi na Sama da Naira Biliyan 161
Daga Usman Muhammad Zaria
Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri ta Jihar Jigawa ta yi kiyasin kashe kudade miliyan dubu 161 da milyan 336 domin gudanar da ayyukan hanyoyin mota da harkokin yau da kullum a sabuwar shekara ta 2026.
Babban sakataren ma’aikatar, Malam Ahmad Isah, ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin ma’aikatar a gaban kwamatin ayyuka da sufuri na majalisar dokokin jihar Jigawa.
Babban Sakataren ya yi bayanin cewar, za a yi amfani da mafi yawan kudaden ne wajen gudanar da ayyukan hanyoyin mota tsakanin gariruwa da hanyoyin burji da kuma titunan cikin gari.
Yana mai cewar, haka kuma za a gudanar da ayyukan hanyoyi a manyan makarantun jihar ciki har Jami’ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa da kwalejin fasaha da ke Dutse da cibiyar binciken aikin gona ta Kazaure, da kwalejin koyon aikin lafiya matakin farko da ke Jahun da sauransu.
Sai dai kuma babban sakataren ya koka dangane da bukatar daukar injiniyoyi domin aiki a ma’aikatar da hukumar gyaran hanyoyin mota JIRMA da kuma daukar sabbin jami’an duba lafiyar ababen hawa wato V.I.O, idan aka yi la’akari da karancin ma’aikata saboda masu yin ritaya.
Alhaji Ahmad Isah ya kara da cewar ma’aikatar tana kokarin cimma yarjajjeniya da makarantar koyon tukin jirgin sama ta kasa da ke Zaria domin amfani da filin jirgin sama na Dutse a matsayin sansanin koyon tukin jirgin sama.
Kazalika, ya ce makarantar koyon tukun mota da ke karamar hukumar Birnin Kudu za ta amfana da wasu ayyuka a sabuwar shekara.
A nasa jawabin, shugaban kwamatin ayyuka da sufuri na majalisar dokokin jihar Jigawa kuma wakilin mazabar Bulangu Alhaji Yusuf Ahmad Soja, ya yi addu’ar Allah Ya sa kasafin kudin ya karfafa cigaban jihar nan a sabuwar shekara.