ShareTweetSendShare MASU ALAKA Siyasa Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya October 21, 2025 Siyasa Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu October 20, 2025 Siyasa Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027 October 17, 2025

.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Alƙaluman wucin-gadi na nuna Paul Biya ya lashe zaɓen Kamaru

Kwamitin da Kotun Tsarin Mulki ta Kamaru ta kafa domin sake ƙirga ƙuri’un zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar ranar 12 ga Oktoba, ya miƙa rahotonsa a wannan Talatar.

Sakamakon da kwamitin ya gabatar ya nuna cewa shugaban ƙasa mai ci, Paul Biya, ya samu nasara da kashi 53.66 na ƙuri’un da aka kaɗa, yayin da Isa Tchiroma Bakary ya zo na biyu da kashi 35.19.

Tinubu ya naɗa sabon Minista Yadda Zanga-zangar Kanu ta ja wa ’yan kasuwa da ma’aikata asara

Sai dai ɓangaren jam’iyyar adawa, musamman ta Tchiroma, sun yi watsi da wannan sakamako tun kafin a sanar da shi a hukumance.

Alƙaluman kwamitin sun nuna cewa jam’iyyar RDPC ta shugaba Biya ta samu ƙuri’u 2,474,179, yayin da Cabaral Libi ya zo na uku da sama da kashi 3.41.

A halin da ake ciki, jagoran adawa, Issa Tchiroma Bakary, wanda shi ne tsohon minista kuma tsohon kakakin gwamnati, ya ce shi ne ya lashe zaɓen da sama da kashi 60 na ƙuri’un da aka kaɗa, bisa ga abin da bayanan runfunan zaɓe ke nunawa.

Jam’iyyun adawa da kuma ƙungiyoyin farar hula da ke mara masa baya sun buƙaci hukumomi da su girmama zaɓin al’umma, maimakon ƙoƙarin murɗe sakamako, wanda a cewarsu hakan na iya jefa ƙasar cikin rikicin siyasa.

Kotun Tsarin Mulki ce kaɗai ke da ikon bayyana sahihin sakamakon zaɓe, kuma ana sa ran za ta yi hakan a ranar Alhamis mai zuwa, bayan da kwamitin da ta naɗa ya kammala aikin ƙirga ƙuri’un da ya shafe kwanaki uku yana gudanarwa a birnin Yaounde.

Tuni dai gwamnatin Kamaru ta jibge jami’an tsaro a wasu manyan biranen ƙasar kamar Douala, Yaounde, Bafoussam da kuma Garoua, mahaifar madugun adawa Tchiroma Bakary.

Tun dai bayan gudanar da zaɓen ne Tchiroma ya ayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara da tazara mai yawa a gaban Paul Biya, lamarin da ya haifar da cece-kuce tsakanin ’yan ƙasar.

Rahotanni sun bayyana cewa an jibge ’yan sandan kwantar da tarzoma domin daƙile yunƙurin zanga zangar watsi da sakamakon zaɓe da ake sa ran sanarwa ranar Alhamis 23 ga wannan wata da muke ciki.

Tchiroma Bakaray, mai shekara 76, wanda ya raba gari da Paul Biya a farkon shekarar nan inda ya ƙaddamar da gagarumin yaƙin neman zaɓe da ya samu karɓuwa daga ɗimbin jama’a da kuma wani ɓangare na ‘yan adawa da ƙungiyoyi masu zaman kansu.

Idan ba a manta ba, a zaɓen shugaban ƙasa na 2018, ɗan takarar jam’iyyar hamayya na wancan lokaci Maurice Kamto ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen kwana guda bayan kammala kaɗa ƙuri’a.

Daga bisani an kama shi sannan aka yi amfani da barkonon-tsohuwa da ruwan zafi wajen tarwatsa magoya bayansa da suka yi zanga-zanga.

Paul Biya, mai shekara 92, wanda shi ne shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya, yana neman yin ta-zarce a karo na takwas bayan ya shafe shekaru 43 a kan mulki.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Alƙaluman wucin-gadi na nuna Paul Biya ya lashe zaɓen Kamaru
  • Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya
  • NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi 
  • Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu
  • Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU
  • Kungiyar Kare Hakkin Bil-Adama Ta Amnesty Ta Zargi Gwamnatin Tanzaniya Da Musgunawa ‘Yan Adawa
  • Dakarun kare Juyin Musulunci Na Iran Sun Bayyan Shirinsu Na Karfafa Dabarun Hadin Guiwa Da yamen
  • Zanga-zanga: Jami’an tsaro sun kafa shingayen bincike a wajen Abuja
  • Juyin mulki: Ana zargin tsohon gwamnan da ɗaukar nauyin sojojin Najeriya