Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta
Published: 20th, October 2025 GMT
A daren Lahadi a ƙasar Chile, ƙasar Morocco ta kafa tarihi bayan da ta doke Argentina da ci 2-0 a wasan ƙarshe na gasar Kofin Duniya na ƴan ƙasa da shekaru 20, wanda hakan ya bai wa ƙasar damar lashe wannan kofi a karon farko a tarihin ta.
Yassir Zabiri, wanda ke taka leda a ƙungiyar FC Famalicao ta ƙasar Portugal, shi ne gwarzon wasan bayan da ya ci ƙwallaye biyu a ragar Argentina tun a farkon rabin lokaci.
Wannan nasarar ta sanya Morocco zama ƙasa ta farko daga nahiyar Afrika da ta lashe kofin tun bayan nasarar Ghana a shekarar 2009. A ɓangaren Argentina kuwa, rashin nasarar ya kawo ƙarshen burinsu na lashe kofin duniya na matasa karo na bakwai, abin da ya haifar da cece-kuce a ƙasar.
Ko da yake Argentina ta rasa manyan ƴan wasanta biyu — Claudio Echeverri na Bayer Leverkusen da Franco Mastantuono na Real Madrid. Sai dai nasarar Morocco ta jawo murnar gangami a biranen Casablanca, da Rabat da sauran sassan ƙasar, alamar cewa ƙwallon ƙafar Afrika na ƙara samun karɓuwa da daraja a duniya.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kungiyar ECOWAS Ya Gana Da Shugaban Mulki Soji Na Kasar Guinea Bissau
Shugaban kungiyar kula da tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika kuma shugaban kasar saliyo Julius mada Bio yace ya tattauna da shugaban mulkin soji da ya yi juyin mulki a kasar Guinea Bissau , a kokarin da suke yi na ganin an yi aiki da kundin tsarin mulki a yankin na yammacin Afrika.
A cikin jawabin da ya wallafa a shafinsa na X bio ya fadi cewa ganawar ta su ta zo ne bayan kudurin da kungiyar ta ECOWAS ta fitar a taron da ta gudanar kan irin mataken da zaa dauka game da batun juyin mulki da aka yi a kasar Guinea Bissau a makon jiya.
Shiga tsakani a rikicin kasar Guinea Bissau ya zo ne sakamakon rashin zaman lafiya na siyasa da kuma tarihin juyin mulkin soja a kasar, tun bayan samun yanci kai a shekara ta 1974 , guinea Bissau ta sha fama da yankewar harkokin mulkin demukuradiya akai –akai.
Tshon shugaban Nigeria Goodlock Jonathan wanda ya jagoranci tawagar ECOWAS don sa ido kan yadda zaben ke gudana ya sanya alamar tambaya game da hakikanin juyin mulki da sojoji suka yi , yace wani shiri ne tsakanin shugaban kasar Embalo domin kaucewa rashin nasara a zaben da aka yi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Bude Taron Bikin Cika Shakaru 41 Da Kafa Kungiyar Tattalin Arziki Ta ECO A nan Tehran December 2, 2025 Araghchi: Halayyar Amurka ce yin matsin lamba maimakon diflomasiyya a dangantaka ta kasa da kasa December 2, 2025 Aljeriya: Taron Kasashen Afirka Don Amincewa Da Mulkin Mallaka A Matsayin Laifi December 2, 2025 Lebanon: An Gudanar Da Taron Musulunci da Kiristanci a Beirut tare da halartar Paparoma December 2, 2025 Chuck Schumer: Trump Ba Shi da Ikon Kaddamar da Yaki Kan Venezuela December 2, 2025 Najeriya: Matatar Dangote Za Ta Mika Tataccen Mai Lita Biliyan 1.5 A Watan Disamba December 2, 2025 Ramaphosa ya yi watsi da barazanar Trump na ware Afirka ta Kudu daga G20 December 2, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 165 December 1, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan 164 December 1, 2025 Baqaei: Amurka Ce Babbar Barazana Ga Zaman Lafiya Da Tsaro A Duniya December 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci