MTN zai rufe ofisoshi 101 a Kano, Borno da Adamawa saboda gyare-gyare
Published: 22nd, October 2025 GMT
Kamfanin sadarwa na MTN ya sanar da shirin gudanar da aikin gyare-gyare a cibiyoyin sadarwa a ranar Asabar, 25 ga watan Oktoba mai zuwa.
Ana sa ran aikin zai kawo tsaiko na ɗan lokaci ga sadarwa a wasu sassan jihohin Adamawa, Borno da Kano.
Labarin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya ƙarya ne – Sarkin Musulmi Masu kwacen waya sun kashe ma’aikaciyar lafiya a ZariyaMTN ya ce aikin zai ɗauki tsawon sa’o’i biyu, daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa 8:00 na safe, inda zai shafi ofisoshi 101 na cibiyar sadarwa a cikin ƙananan hukumomi 15 a jihohi ukun.
Kamfanin ya ce aikin yana cikin wani dogon shiri na inganta ayyuka da ƙarfafa tsarin sadarwa a Arewacin Najeriya.
Aikin zai haɗa da sauya wayoyin sadarwa na cable a wani ɓangare da aka matsar daga AFCOT zuwa kauyen Bawo, inda za a maye gurbin ɓangarorin wayoyin da suka lalace.
Yankunan da gyaran zai shafa
MTN ya ce yankunan da gyaran zai shafa sun haɗa da Karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano; Girei, Song, Mubi North, Hong, Gombi, Fufore, Mubi South, Madagali, Michika, Maiha, Chibok da Yola ta Arewa a jihar Adamawa; da kuma Askira/Uba da Shani a jihar Borno.
Kamfanin ya ce sabis din 2G da 3G da 4G ba za su yi aiki ba a lokacin aikin.
MTN ta ce wannan mataki yana gina kan aikin dawo da cibiyar sadarwa da aka gudanar a watan Agusta 2025 a kan hanyar igiyar sadarwa ta AFCOT–Bawo.
Kamfanin ya ce abokan huldarsa na iya fuskantar tsaiko na ɗan lokaci, kuma ya ba da hakuri kan duk wata matsala da hakan zai iya haifarwa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gyare Gyare
এছাড়াও পড়ুন:
Dalilin da ya sa ’yan sanda suka kama ni — Muhuyi
Tsohon Shugaban Hukumar Kaɓar Koke-koke da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC), Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana dalilin da ya sa ’yan sanda suka kama shi.
Ya ce an kama shi ne saboda jagorantar shari’ar almundahanar biliyoyin Naira na Dala Inland Dry Port, wadda ta shafi tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da iyalinsa.
Jirgin sojin sama ya yi hatsari a Neja Nakiya ta hallaka yara 4 a BornoMuhuyi, ya shaida wa DCL Hausa cewa an tafi da shi Abuja cikin dare.
“Da aka kama ni, suka sanya jami’ai biyu ɗauke da bindiga a gefena, sai wasu uku a gaba. Haka muka tafi daga Kano zuwa Abuja cikin dare,” in ji shi.
Ya ce ’yan sandan sun ƙi nuna masa takardar izinin kama shi har sai da suka isa Abuja.
“Da muka isa, suka gabatar min da sabbi tuhume-tuhume na ɓatanci da kutse.
“A ina ne wanda ake zargi zai ki kare kansa ya kuma umarci ’yan sanda su kama babban lauya mai shigar da ƙara?” ya tambaya.
An bayar da belinsa, amma an umarce shi da ya koma Abuja a ranar Laraba tare da miƙa fasfo d5insa.
Ganduje da ’ya’yansa na fuskantar shari’a kan zargin canja mallakar kaso 20 a aikin Dala Inland Dry Port ba bisa ƙa’ida ba.