HausaTv:
2025-10-21@14:32:47 GMT

Faransa : Sarkozy, ya fara zaman gidan yari na shekara 5

Published: 21st, October 2025 GMT

Tsohon shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, ya fara zaman gidan yari na shekara biyar a gidan yarin La Santé da ke tsakiyar birnin Paris.

An same shi da aikata laifin hada baki wajen samun kudaden yakin neman zabensa na shekarar 2007 daga tsohon shugaban Libiya, Muammar Gaddafi.

Sarkozy ya musanta aikata laifin, kuma ya nemi a sake shi daga gidan yari yayin da yake neman daukaka kara.

Wannan dai shi ne karo na farko a tarihin jamhuriya ta biyar da wani tsohon shugaban kasar zai kwana a gidan yari.

Magoya bayansa sun taru da sanyin safiyar yau a wajen gidansa na Paris.

A shafin sa na sada zumunta ya yi wa magoya bayansa alkawarin cewa .gaskiya za ta yi nasara.

Za a tsare Sarkozy, wanda yake da shekaru 70 a sashen kebantattun fursunoni.

A tarihin Faransa, shugabanni biyu ne kawai suka taba zuwa gidan yari kafin shi da suka hada da Philippe Pétain, wanda ya yi hadin baki da Jamusawa a lokacin Yakin Duniya na Biyu, da kuma Sarki Louis na 16, kafin a kashe shi.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza : Falasdinawa 97 sojin Isra’ila suka kashe tun bayan cimma yarjejeniya October 21, 2025 Iran Da Faransa Zasu Yi Musayar Fursinoni, Esfandiari Tana Daga Cikin Wacce Za’a Sallama October 21, 2025 Gaza: Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa 57 A Cikin Sa’o’i 24 Da Suka Gabata October 21, 2025 Kakakin Majalisar Dokokin Kasar Lebanon Ya Ce Babu Wata Tattaunawa Da HKI October 21, 2025 Tom Barak: Saudiyya na gab da kulla alaka da Isra’ila a hukumance October 21, 2025 Kremlin: Rasha a shirye take don fadada hadin gwiwa da Iran a dukkanin fannoni October 21, 2025 Jagora Ya Mayar Da Martani Ga Trump Cewa; Su Ci Gaba Da Mafarkinsu October 20, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Jaddada Aniyarta Ta Yin Riko Da Hakkokin Kasarta October 20, 2025 Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran Ya Karbi Bakwancin Takwaransa Na Iraki October 20, 2025 Wakilin Amurka A Siriya Ya Matsa Lamba Kan Saudiyya Da Lebanon Da Siriya Don Kulla Alaka Da Isra’ila October 20, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: a gidan yari

এছাড়াও পড়ুন:

Doha: Pakistan da Afghanistan sun amince da tsagaita bude wuta a tsakaninsu

Ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta sanar da cewa, kasashen Pakistan da Afghanistan sun amince da tsagaita bude wuta nan take a tattaunawar da ake yi a Doha babban birnin kasar.

Ma’aikatar ta tabbatar da cewa bangarorin biyu sun amince da tsagaita bude wuta a wani zagayen shawarwarin da kasashen Qatar da Turkiyya suka jagoranta a ranar Asabar.

Ma’aikatar ta kara da cewa kasashen biyu sun kuma amince da da a ci gaba da tattaunawa a cikin kwanaki masu zuwa don tabbatar da dorewar tsagaita bude wuta.

Ministan tsaron Pakistan Khawaja Muhammad Asif ya ce bangarorin biyu za su sake ganawa a ranar 25 ga watan Oktoba a Istanbul domin tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban da aka samu game da hakan.

A baya dai bangarorin biyu sun sanar da cewa za su gudanar da tattaunawar zaman lafiya a Doha a kokarin da suke na kawo karshen rikicin da ya barke a kan iyakar Afghanistan da Pakistan a cikin kwanakin nan.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Isra’ila ta ce mashigar Rafah za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai abin da hali ya yi October 19, 2025 Araqchi: Kuduri Mai Lamba 2231 Ya Zo Karshe October 18, 2025 Kasashen Iran, Rasha, Da China Sun Jaddada Rashin Halaccin Dawo Da Tsohon Takunkumi Kan Iran October 18, 2025 Masani Kan Harkokin Tsaro Ya Ce: Makami Mai Linzamin Iran Kirar Ghadir Ya Aike Da Sako Ga Isra’ila October 18, 2025 Jami’in Majalisar Dinkin Duniya Ya Ce: An Rusa Gaza Gaba Daya October 18, 2025 Joseph Kabila Ya Koma Kasarsa Domin Kalubalantar Hukuncin Kisa Da Aka Yanke Kansa October 18, 2025 Gaza Ta Bukaci A Binciki Isra’ila Kan Sace Sassan Jiki A Gawarwakin Falasdinawa October 18, 2025 Hamas Ta Bukaci A Kafa Kotun Kasa Da Kasa Kan Gawarwarkin Da Isra’ila Ta Dawo Mata Da Su. October 18, 2025 Madagascar : An rantsar Da Michael Randrianirina A Matsayin Shugaban Kasar October 18, 2025 Iran Ta yi Tir Da Harin da Isra’ila Ta kai Kudancin Kasar labanon. October 18, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Equatorial Guinea ta zargi Faransa da karan-tsaye wa zaman lafiya a kasar
  • Iran Da Faransa Zasu Yi Musayar Fursinoni, Esfandiari Tana Daga Cikin Wacce Za’a Sallama
  • Kakakin Majalisar Dokokin Kasar Lebanon Ya Ce Babu Wata Tattaunawa Da HKI
  • Tom Barak: Saudiyya na gab da kulla alaka da Isra’ila a hukumance
  • Kotu A Faransa Ta Yanke Hukumci Zama Gidan Yari Ga Tsohon Shugaban Kasar Nicola Sarkozi
  • An Fara Kidayar Kuri’un Zabukan Kananan Hukumomi 16 Da Aka Yi A Libya
  • Sojojin HKI Sun Shiga Cikin Yankin Qunaidhara Na Kasar Syria
  • Hamas Ta Gabatar Da Sunayen Kwararrun Da Zasu Gudanar Da Harkokin Gaza
  • Doha: Pakistan da Afghanistan sun amince da tsagaita bude wuta a tsakaninsu