Yadda Morocco ta kafa tarihin ɗaga Kofin Duniya na FIFA U20
Published: 20th, October 2025 GMT
Morocco ta ɗaga Kofin Duniya na FIFA U20 a karon farko a tarihin gasar, bayan ta doke Argentina da ci 2 da nema, tawagar da ta fi kowace ƙasa a duniya lashewa a tarihi
Wannan gagarumar nasara ya sa ta zama ƙasar Afirka ta biyu da ta ɗaga wannan kofi bayan Ghana, wadda ta yi nasara a shekarar 2009.
Gwamnonin Kano, Katsina da Jigawa sun ƙulla yarjejeniyar bunƙasa wutar lantarki Kano Pillars ta dakatar da KocintaA yammacin jiya Lahadi ce aka gudanar da wasan ƙarshe a filin wasa na Estadio Nacional Julio Martínez Prádanos da ke birnin Santiago na Chile, gidan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Universidad de Chile da kuma babbar tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar.
‘Yan wasan tawagar ƙwallon ƙafar Morocco ta ‘yan ƙasa da shekaru 20 sun buga wasan ƙarshe cikin natsuwa da ƙarsashi, cike da ƙwarin gwiwa, lamarin da ya ba da gudunmuwa haƙarsu ta cimma ruwa.
Ɗan wasan gaban Morocco, Yassir Zabiri, shi ne gwarzon wannan karo, inda a cikin minti na 12 da fara wasa ya ci ƙwallon farko ta hanyar bugun tazara, sannan daga bisani ya sake jefa ƙwallo ta biyu bayan hutun rabin lokaci.
Tawagar Argentina, wadda ke neman kofi na bakwai a tarihin wannan gasa, sun yi duk mai yiwuwa wajen riƙe ƙwallo a yayin wasan, amma suka gaza fasa bayan Morocco da ke ƙarƙashin jagorancin Youssef Benchaa.
Morocco dai ta taka rawar gani sosai a wannan gasa, inda ta fara doke Spain, Brazil, Koriya ta Kudu da Amurka, sannan a wasan kusa da ƙarshe ta doke Faransa a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Tawagar Morocco ta yi rashin nasara ne kawai a hannun Mexico a matakin rukuni, amma daga nan ta ƙara ƙaimi suka ci gaba da taka rawar gani har suka ɗaga kofin.
Messi ya jajanta wa ‘yan wasan ArgentinaTauraron ƙwallon ƙafa, Lionel Messi, ya jajanta wa tawagar Argentina ta ‘yan ƙasa da shekaru 20, bayan rashin nasarar da ta yi a gasar da aka kammala ranar Lahadi a ƙasar Chile.
Messi ya wallafa a Instagram cewa, “Ku saurara, yara!!! Kun taka rawar gani a gasar, kuma duk da cewa mun so ganin kun ɗaga kofin, mun yi murna da abin da kuka ba mu, da kuma alfaharin yadda kuka kare tutar ƙasarmu da zuciyarku.”
Wannan rashin nasara ta ja hankalin tauraron ɗan wasan, wanda ya taɓa lashe gasar ta ‘yan ƙasa da shekaru 20 tare da Argentina a shekarar 2005.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Argentina Kofin Duniya
এছাড়াও পড়ুন:
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja
“Wannan mummunan lamari da ya faru a ranar 11 ga Oktoba, 2025, a Wawa Cantonment, Jihar Neja, ya haifar da yanayi mai cike da tashin hankali, inda mazauna sansanin suka shiga cikin mamaki kan yadda irin wannan abin takaici zai iya faruwa,” in ji wani bangare na sanarwar.
A cewar rundunar sojoji, an gano gawarwakin Lance Corporal Femi da matarsa a cikin gidansu dake gini na 15, daki mai lamba 24, Corporals and Below Kuarters, a cikin sansanin.
Binciken farko ya nuna cewa sojan yana kan aiki a lokacin kuma ya nemi izini daga babban jami’i domin ya kula da wasu harkokin kansa kafin ya dawo aiki.
“Rundunar Sojin Nijeriya tana matukar bakin ciki kan wannan lamari, sannan tana taya iyalan, abokan aiki, da abokan marigayin jimami kan wannan babban rashi.
“Rundunar soji kuma tana addu’ar Allah ya jikansu cikin salama,” in ji Nwachukwu.
An ajiye gawarwakin marigayin, sannan an fara gudanar da cikakken bincike don gano dalilan da suka haifar da wannan abin takaici.
“Brigadier Janar Ezra Barkins, kwamandan 22 Armoured Brigade, ya tabbatar wa jama’a cewa sakamakon binciken zai kasance a bayyane kuma za a duba shi sosai, tare da daukar matakan da suka dace don hana faruwar irin wannan lamari a nan gaba,” in ji Nwachukwu.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA