Aminiya:
2025-12-05@23:13:40 GMT

Alƙaluman wucin-gadi na nuna Paul Biya ya lashe zaɓen Kamaru

Published: 21st, October 2025 GMT

Kwamitin da Kotun Tsarin Mulki ta Kamaru ta kafa domin sake ƙirga ƙuri’un zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar ranar 12 ga Oktoba, ya miƙa rahotonsa a wannan Talatar.

Sakamakon da kwamitin ya gabatar ya nuna cewa shugaban ƙasa mai ci, Paul Biya, ya samu nasara da kashi 53.66 na ƙuri’un da aka kaɗa, yayin da Isa Tchiroma Bakary ya zo na biyu da kashi 35.

19.

Tinubu ya naɗa sabon Minista Yadda Zanga-zangar Kanu ta ja wa ’yan kasuwa da ma’aikata asara

Sai dai ɓangaren jam’iyyar adawa, musamman ta Tchiroma, sun yi watsi da wannan sakamako tun kafin a sanar da shi a hukumance.

Alƙaluman kwamitin sun nuna cewa jam’iyyar RDPC ta shugaba Biya ta samu ƙuri’u 2,474,179, yayin da Cabaral Libi ya zo na uku da sama da kashi 3.41.

A halin da ake ciki, jagoran adawa, Issa Tchiroma Bakary, wanda shi ne tsohon minista kuma tsohon kakakin gwamnati, ya ce shi ne ya lashe zaɓen da sama da kashi 60 na ƙuri’un da aka kaɗa, bisa ga abin da bayanan runfunan zaɓe ke nunawa.

Jam’iyyun adawa da kuma ƙungiyoyin farar hula da ke mara masa baya sun buƙaci hukumomi da su girmama zaɓin al’umma, maimakon ƙoƙarin murɗe sakamako, wanda a cewarsu hakan na iya jefa ƙasar cikin rikicin siyasa.

Kotun Tsarin Mulki ce kaɗai ke da ikon bayyana sahihin sakamakon zaɓe, kuma ana sa ran za ta yi hakan a ranar Alhamis mai zuwa, bayan da kwamitin da ta naɗa ya kammala aikin ƙirga ƙuri’un da ya shafe kwanaki uku yana gudanarwa a birnin Yaounde.

Tuni dai gwamnatin Kamaru ta jibge jami’an tsaro a wasu manyan biranen ƙasar kamar Douala, Yaounde, Bafoussam da kuma Garoua, mahaifar madugun adawa Tchiroma Bakary.

Tun dai bayan gudanar da zaɓen ne Tchiroma ya ayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara da tazara mai yawa a gaban Paul Biya, lamarin da ya haifar da cece-kuce tsakanin ’yan ƙasar.

Rahotanni sun bayyana cewa an jibge ’yan sandan kwantar da tarzoma domin daƙile yunƙurin zanga zangar watsi da sakamakon zaɓe da ake sa ran sanarwa ranar Alhamis 23 ga wannan wata da muke ciki.

Tchiroma Bakaray, mai shekara 76, wanda ya raba gari da Paul Biya a farkon shekarar nan inda ya ƙaddamar da gagarumin yaƙin neman zaɓe da ya samu karɓuwa daga ɗimbin jama’a da kuma wani ɓangare na ‘yan adawa da ƙungiyoyi masu zaman kansu.

Idan ba a manta ba, a zaɓen shugaban ƙasa na 2018, ɗan takarar jam’iyyar hamayya na wancan lokaci Maurice Kamto ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen kwana guda bayan kammala kaɗa ƙuri’a.

Daga bisani an kama shi sannan aka yi amfani da barkonon-tsohuwa da ruwan zafi wajen tarwatsa magoya bayansa da suka yi zanga-zanga.

Paul Biya, mai shekara 92, wanda shi ne shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya, yana neman yin ta-zarce a karo na takwas bayan ya shafe shekaru 43 a kan mulki.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Issa Tchiroma Bakary Kamaru Paul Biya

এছাড়াও পড়ুন:

Wani ya yi shigar mahaifiyarsa da ta mutu ya je karvar kuxin fanshonta

Wani ya yi shigar mahaifiyarsa da ta mutu ya je karvar kuxin fanshonta

Ana binciken wani tsohon ma’aikacin jinya a qasar Italiya bisa zargin ya yi shigar mahaifiyarsa da ta mutu kuma ya je ma’aikatar fansho a matsayin mahaifiyarsa don neman fanshonta. Haka kuma an gano ya voye gawarta a cikin gidansa har tsawon shekaru uku bayan mutuwarta.

Mutumin xan Italiya ya saka tufafin mahaifiyarsa da ta mutu sannan ya yi kwalliya da gazar da jan-baki kamar yada take yi, ya je bankin da take ajiya yana neman a biya shi kuxi fanshonta, bayan ya voye gawarta a gida.

Mutumin mai shekaru 56, ma’aikacin jinya da ya rasa aikinsa a garin Mantua, ya sami damar karvar dubban kuxi na Yuro kafin asirinsa ya tonu, kamar yadda Jaridar Corriere della Sera ta Italiya ta ruwaito.

An kuma yi zargin cewa, ya naxe gawar mahaifiyarsa, Graziella Dall’Oglio, sannan ya voye ta a cikin firji a gidansu har tsawon shekara uku ba tare da ya sanar da ma’aikatar fansho ba, inda ya riqa zuwa yana cire kuxin fanshon da ake tura mata yana bidirin gabansa.

Mis Dall’Oglio ta rasu kimanin shekara uku da suka gabata, tana da shekara 82. Amma xanta bai bayar da rahoton mutuwarta a hukumance ba, maimakon haka ya naxe gawarta a cikin zane, ya saka ta a cikin wata jakar ajiye kaya sannan ya voye ta a gidan.

Rahotanni sun ce, ya yi shigar mahaifiyarsa, sanye da jan-baki da hoda da gazar da kuma sarqa, sannan ya tafi sabunta katin shaidarta da ya qare a ofishin gwamnati da ke wajen Borgo Virgilio.

Bayanai sun nuna cewa, ya yi wa kansa aski sannan ya sanya gashin mata a kansa kamar irin na mahaifiyarsa da ta rasu, kuma ya sanya kayan ado kamar yadda ta saba.

Jaridar ta bayyana cewa, wannan wani sabon salon damfara ce kamar irin na fim xin ‘Mrs Doubtfire’, wanda aka yi a shekarar 1993 da Robin WilliaMis da ya fito a ciki. Mutumin ya bayyana a ofishin gwamnati da ke wajen Mantua a farkon wannan watan, inda aka yi zargin ya bayyana kansa a matsayin Mis Dall’Oglio.

Wani ma’aikacin ma’aikatar fansho ne ya harvo jirginsa, inda ya lura da cewa, akwai alamar tambaya game da ‘matar’ da take neman a canza mata katin. Musamman da yake ya san wacce take da ainihin katin ba ta da kaurin wuya, sannan kuma muryarta ba ta maza ba ce. Wannan ce ta sanya ma’aikacin bai wata-wata ba cikin sauri ya kai rahoto ga ‘yan sanda nan da nan kuma ya sanar da magajin garin Mantua.

’Yan sanda sun ce, da isarsu sai suka kwatanta hotunan Mis Dall’Oglio na gaske da na xanta da ya yi shigar burtu kuma sun fahimci cewa, akwai lauje a cikin naxi.

Bincike ya nuna xan ya karvi kuxin fanshonta na shekaru uku da suka kai kusan Fam 47,000 kuma da mallakar gidaje uku, a cewar rahotanni.

Bayan an kama shi, ‘yan sanda sun je gidansa, inda suka gano gawar Mis Dall’Oglio da aka voye a xakin wanki.

“Ya shigo ofishin ma’aikatar fansho yana sanye da dogon siket, ya yi ado da jan baki da jan-farce da sarqa da ‘yan kunne irin na tsofaffi,” Francesco Aporti, magajin garin Borgo Virgilio ya shaida wa Jaridar Corriere della Sera.

“Amma sai dai yana da kaurin wuya, sannan kuma fatar hannunsa ba ta yi kama da na tsohuwa ‘yar shekara 85 ba.

“Muryarsa kuma ta maza ce duk da yake ya yi shigar mata. Amma da a ce ba a lura da waxannan abubuwa ba da ya ci lalai.”

Da yake magana game da mahaifiyar wanda ake zargin, magajin garin ya ce, “Wataqila ta mutu ne saboda dalilai na rashin lafiya, amma za a tabbatar da hakan ne kawai ta hanyar binciken gawar.” Wannan labari ne mai ban mamaki kuma abin baqin ciki ne qwarai.”

‘Yan sandan Italiya sun ce, gawar mahaifiyar an naxe ta da zanin gado sannan aka saka ta a wata jakar kaya, aka sanya ta cikin firji.

Daga baya ’yan sanda sun xauki gawar zuwa wajen ajiye gawarwaki a asibitin da ke yankin don yin gwajin qwaqwaf da nufin gano musabbabin rasuwarta. Yanzu haka ana binciken mutumin a kan laifukan zamba da voye gawar da ya yi ba bisa qa’ida ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Na kashe N100bn a kan harkar tsaro a 2025 — Zulum
  • An harbe manomi saboda rikici kan filin kiwo a Borno
  • Ziyarar Putin a Indiya alama ce da ke nuna cewa New Delhi na yin watsi da gargadin Trump?
  • ’Yan sandan Borno sun kama matashin da ake zargi da kashe makwabciyarsa da wuƙa
  • ’Yan Najeriya suna da ƙwarin guiwa a kaina, ba zan ba su kunya ba — Ministan Tsaro
  • Rikicin Kungiyoyin Asiri Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Wani Matashi A Jihar Kwara
  • Wani ya yi shigar mahaifiyarsa da ta mutu ya je karvar kuxin fanshonta
  • Har yanzu ban bar yin waqa ba-Yusuf Lazio
  • Yau Majalisar Dattawa za ta tantance sabon Ministan Tsaro
  • Mako mai Majalisa za ta kada ƙuri’a kan ƙudurin ƙirƙirar sabbin jihohi