HausaTv:
2025-12-05@21:19:01 GMT

Gaza : Falasdinawa 97 sojin Isra’ila suka kashe tun bayan cimma yarjejeniya

Published: 21st, October 2025 GMT

Bayanai daga Falasdinu na cewa a kalla Falasdinawa 97 ne sojojin Isra’ila suka kashe tare da jikkata wasu 230 tun bayan da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta fara aiki a Gaza a ranar 10 ga watan Oktoba.

A cikin wata sanarwa da ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya fitar, ya ce ‘yan mamayar  sun aikata laifuka 80 tun bayan ayyana tsagaita bude wuta, wanda hakan ya saba wa dokokin jin kai na kasa da kasa.

Laifukan sun hada da harbin bindiga kai tsaye kan fararen hula da gangan, da kama fararen hula.

A cewar sanarwar, sojojin na Isra’ila sun yi amfani da motocin soji, tankunan yaki da aka jibge a gefuna da wuraren zama, da jirage marasa,

lamarin da ke tabbatar da cewa Isra’ilar ba ta bi yarjejeniyar tsagaita bude wutar ba kuma tana ci gaba da manufofinta na kisa da ta’addanci a kan mutanenmu.”

Gwamnatin Gaza ta dorawa sojojin Isra’ila alhakin keta hakkinsu tare da yin kira ga Majalisar Dinkin Duniya da bangarorin da suka shiga Tsakani wajen cimma yarjejeniyar da su dauki mataki cikin gaggawa kan hakan.

A ranar 10 ga watan Oktoba ne yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin kungiyar Falasdinawa ta Hamas da Isra’ila, bisa shirin da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar ta fara aiki.

Yarjejeniyar ta tanadi janye sojojin Isra’ila a hankali, da musayar fursunoni, da shigar da kayan agaji cikin gaggawa

Yarjejeniyar na da nufin kawo karshen yakin shekaru biyu da Isra’ila ta yi kan Gaza wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa sama da 68,000, tare da raunata kusan 170,000, tare da lalata mafi yawan ababen more rayuwa na Gaza.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Da Faransa Zasu Yi Musayar Fursinoni, Esfandiari Tana Daga Cikin Wacce Za’a Sallama October 21, 2025 Gaza: Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa 57 A Cikin Sa’o’i 24 Da Suka Gabata October 21, 2025 Kakakin Majalisar Dokokin Kasar Lebanon Ya Ce Babu Wata Tattaunawa Da HKI October 21, 2025 Tom Barak: Saudiyya na gab da kulla alaka da Isra’ila a hukumance October 21, 2025 Kremlin: Rasha a shirye take don fadada hadin gwiwa da Iran a dukkanin fannoni October 21, 2025 Jagora Ya Mayar Da Martani Ga Trump Cewa; Su Ci Gaba Da Mafarkinsu October 20, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Jaddada Aniyarta Ta Yin Riko Da Hakkokin Kasarta October 20, 2025 Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran Ya Karbi Bakwancin Takwaransa Na Iraki October 20, 2025 Wakilin Amurka A Siriya Ya Matsa Lamba Kan Saudiyya Da Lebanon Da Siriya Don Kulla Alaka Da Isra’ila October 20, 2025 Amnesty Ta Zargi Gwamnatin Tanzaniya Da Musgunawa ‘Yan Adawa October 20, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: da Isra ila

এছাড়াও পড়ুন:

Mutum 6 sun rasu, 13 sun jikkata a hatsarin mota a Kogi

Aƙalla mutum shida ne suka rasu, yayin da wasu 13 suka jikkata, bayan wata bas ɗauke da nakasassu ta yi hatsari a kan hanyar Lokoja zuwa Okene.

Waɗanda abin ya shafa suna komawa Okene ne bayan halartar bikin Ranar Nakasassu ta Duniya ta 2025 a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Lokoja.

Jirgin fadar shugaban ƙasa ya ƙi sayuwa wata 5 bayan saka shi a kasuwa ’Yan sanda sun kama mutum 28 kan zargin lalata mata da yara a Yobe

An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci daban-daban a jihar, inda suke ci gaba da samun kulawa.

Kwamishinan Harkokin Sadarwa na Jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, ya ce wannan hatsari abun baƙin ciki ne ga gwamnati da jama’a.

Ya ce Gwamna Ahmed Usman Ododo ya umarci gwamnatin jihar da ta biya dukkanin kuɗin maganin waɗanda suka jikkata kuma ta tura jami’ai zuwa asibitoci don tallafa wa waɗanda abin ya shafa da iyalansu.

Fanwo ya ce: “Gwamnatin Jihar Kogi tana jimami sosai tare da iyalan waɗanda suka rasu guda shida, kuma za ta tallafa musu.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jami’an tsaro sun kama masu garkuwa da mutane 7 a Gombe
  • Iran Ta Mayar Da Martani Kan Sanarwar Bayan Taron  Majalisar Kasashen Yankin Tekun Fasha
  • Microsoft Za Ta Fuskanci Hukunci Kan Waimaka Wa Isra’ila A  Laifukan Da Take Aikatawa Kan Falasdinawa
  •  An Kira Yi Gwamnatin Canada Da Ta Kama Olmert Da Livini Na “Isra’ila
  • An Kashe Shugaban ‘Yan Dabar Gaza “Abu Shabab” Da Isra’ila Ke Goyon Baya
  • MDD ta bukaci a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma janyewa daga Tuddan Golan na Siriya
  • Mutum 6 sun rasu, 13 sun jikkata a hatsarin mota a Kogi
  • Hamas Za ta Mikawa Isra’ila Samfurin  Da Aka Samu A Karkashin Burabutsai A Yankin Gaza
  • Masar Ta Sanar Da Tattaunawa Da Amurka Don Shirya Sake Gina Gaza
  • Isra’ila Ta Hana Motocin Agaji 6000 Shiga Gaza Duk Da Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta