Aminiya:
2025-10-21@22:59:10 GMT

Majalisa ta soma binciken yadda aka kashe $4.6bn na tallafin kiwon lafiya

Published: 21st, October 2025 GMT

Majalisar Wakilai ta amince a soma binciken yadda aka yi amfani da tallafin ƙetare da ya kai dala biliyan 4.6 da Nijeriya ta karɓa daga shekarar 2021 zuwa 2025, domin yaƙi da cututtukan HIV/AIDS, tarin fuka (TB), da zazzabin cizon sauro (maleriya).

Wannan na zuwa ne bayan ƙudirin da Honarabul Philip Agbese daga Jihar Benuwe ya gabatar a yayin zaman majalisar na ranar Talata.

Gwamna Bala Mohammed ya ƙirƙiri sabbin masarautu 13 a Bauchi Uba Sani ya yi wa ma’aikatan manyan makarantu ƙarin kashi 70 a albashi

Agbese ya bayyana cewa Nijeriya ta karɓi kusan dala biliyan 1.8 daga Global Fund da kuma dala biliyan 2.8 daga Hukumar Raya Kasashe ta Amurka (USAID) a tsakanin 2021–2025, sai kuma sama da dala biliyan 6 daga shirin tallafin Amurka na PEPFAR domin tallafa wa tsarin kiwon lafiya da yaƙi da cututtuka.

Sai dai ya bayyana damuwa cewa duk da wannan gagarumar gudunmawa, har yanzu Najeriya na daga cikin ƙasashen da suka fi fama da cutar HIV da tarin fuka da maleriya a duniya.

Ɗan majalisar ya yi gargadin cewa, muddin ba a dauki mataki ba, Najeriya na iya gaza cimma muradin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanya a ƙarƙashin manufofinta na kawo ƙarshen cututtukan HIV, tarin fuka, da zazzabin cizon sauro nan da shekarar 2030.

Dangane da hakan ne majalisar ta umurci Kwamitin Kiwon Lafiya, HIV/AIDS, TB da Malaria ya binciki yadda aka kashe kuɗaɗen, tare da kawo mata cikakken rahoto nan da makonni hudu.

Haka kuma, ta buƙaci Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, da ya gabatar da cikakken tsarin aiwatar da tallafin da majalisa ta amince da shi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Majalisar Wakilai Tarin Fuka Zazzabin Maleriya dala biliyan

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda Kwankwaso ya yi murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya sanar da shirinsa na ɗaga darajar Kwalejin Jinya ta Nafisatu da ke Kwankwaso zuwa cikakkiyar Jami’ar Kiwon Lafiya albarkacin bikin zagayowar ranar haihuwarsa.

Taron na wannan Talatar, 21 ga watan Oktoban 2025, ya gudana ne a garinsa na Kwankwaso da ke Karamar Hukumar Madobi, inda aka yaba da ci gaban da makarantar ta samu tun daga kafuwarta a 2019 zuwa yanzu.

Tinubu ya naɗa sabon Minista Alƙaluman wucin-gadi na nuna Paul Biya ya lashe zaɓen Kamaru

Kwankwaso ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin ƙara buɗe damammaki ga mata matasa su sami ilimin kiwon lafiya mai zurfi.

Ya jaddada cewa makarantar ita ce ta farko a Najeriya da ke karɓar dalibai mata kaɗai.

Ya kuma gode wa gwamnatin Jihar Kano bisa tallafa wa shirin ungozoma na Community Midwives, wanda ke taimakawa wajen inganta lafiyar mata a ƙauyuka.

A nasa jawabin, Farfaesa Saleh Ngaski Garba, shugaban majalisar gudanarwar makarantar, ya bayyana cewa kwalejin ta taimaka sosai wajen bai wa mazauna ƙauyen ilimin jinya da ungozoma, kuma yanzu tana da ɗalibai sama da 400 da suka kammala karatu.

Kwankwaso ya ce gina jami’ar zai amfanar da Kano da Najeriya baki ɗaya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jihar Jigawa Za Ta Kashe Sama Da Biliyan Daya Wajen Gyaran Ajujuwa A Makarantu
  • Yadda Kwankwaso ya yi murnar zagayowar ranar haihuwarsa
  • Sin Ta Bayar Da Tallafin Dala Miliyan 3.5 Ga Shirin Samar Da Abinci A Zambia
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Aikin Hanya Akan Kudi Sama Da Naira Biliyan 4
  • EFCC ta ƙwato fiye da naira biliyan 500 a shekara biyu — Shetima
  • Muna Samun Gagarumin Cigaba Wajen Dawo Da Zaman Lafiya A Zamfara-Gwamna Lawal
  • Sanata Barau Ya Kai Ziyarar Gani Da Ido Aikin Da Ake Yi A AKTH
  • Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20
  • Tawagar Likitocin Sin Ta Samar Da Tallafin Jinya Ga Kananan Yara Kyauta A Togo