Tinubu Ya Nemi Alkalai Su Kara Kaimi Wajen Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa
Published: 20th, October 2025 GMT
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Alkalan Najeriya su kasance masu gaskiya, rikon amana da tsoron Allah wajen yanke hukunci. Ya ce duk wata al’umma tana fara rushewa ne idan bangaren shari’a ya lalace.
Ya bayyana cewa gwamnati na kokarin inganta walwala da albashin Alkalan domin karfafa ikon cin gashin kansu.
Da yake bude taron bita na EFCC da NJI a Abuja, Shugaban wanda Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta ya ce adalcin Alkalai ne ginshikin ci gaban kasa.
Ya nuna damuwa kan yadda ake jinkirta shari’o’in manyan laifukan rashawa, yana mai cewa an fi hanzarta shari’ar masu laifin yanar gizo.
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa ba a taba kare kowa saboda siyasa a gwamnatinsa ba, inda ya bayyana cewa EFCC ta samu nasarar gurfanar da mutane sama da 7,000 tare da karbo kadarori fiye da Naira Biliyan 500 cikin shekaru biyu.
Ya bukaci Alkalan su ci gaba da koyon sabbin dabaru, musamman wajen shari’o’in yanar gizo da laifukan kuɗi, tare da tunatar da su cewa cin hanci yana shafar kowa.
A nata bayanin Babbar Alkalin Najeriya, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta bukaci Alkalan su tabbatar da yin adalci ba tare da jinkiri ko son zuciya ba.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya yaba da hadin kan da Alkalan je basu, yana mai cewa nasarorin da aka samu sun nuna jajircewa wajen yaki da cin hanci da rashawa.
Daga Bello Wakili
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Shari a
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Tinubu Ya Nada Janar Christopher Musa Sabon Ministan Tsaro
Daga Bello Wakili
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro.
A wata wasika da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Shugaba Tinubu ya mika sunan Janar Musa domin ya maye gurbin Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya yi murabus a ranar Litinin.
Janar Musa, mai shekaru 58, wanda zai cika 59 a ranar 25 ga Disamba, jajirtaccen soja ne da ya jagoranci rundunonin tsaro a matsayin Shugaban Hafsoshin Tsaro daga 2023 zuwa watan Oktoban 2025.
An haifi Janar Musa a Sakkwato a 1967, inda ya yi makarantar firamare da sakandare kafin ya tafi College of Advanced Studies a Zariya. Ya kammala a 1986 sannan ya shiga Kwalejin Horas da matsakaitan Sojoji (NDA) duk dai a wannan shekarar, inda ya samu digiri na daya a fannin kimiyya a 1991.
An daga Janar Musa zuwa matsayin babban Laftanar (Second Lieutenant) a 1991, kuma tun daga lokacin ya yi aiki a manyan mukamai iri-iri. Daga cikin mukamansa akwai: Babban Jami’in Ma’aikata a bangaren Horaswa da Ayyuka a Hedikwatar Runduna ta 81;
Kwamandan Bataliya ta 73;
Mataimakin Darakta, Kayayyakin Aiki, Sashen Tsare-tsaren Rundunar Soja;
Wakilin Sojin Kasa a Kwamitin Horaswa na Hedikwatar Soji ta Najeriya.
A 2019, ya yi aiki a matsayin Mataimakin Babban Jami’in Ma’aikata na Horaswa da Ayyuka a Hedikwatar Cibiyar Sojin Kasa;
Kwamandan Sashe na 3 na Rundunar Lafiya Dole; da kuma Kwamandan Sashe na 3 na Rundunar Hadin Gwiwar Kasashen Yankin Tafkin Chadi (Multinational Joint Task Force).
A 2021, an nada shi Kwamandan Operation Hadin Kai, inda daga baya ya zama Kwamandan Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, kafin daga bisani Shugaba Tinubu ya nada shi Shugaban Hafsoshin Tsaro a 2023.
A cikin wasikar da ya aikewa Majalisar Dattawa, Shugaba Tinubu ya bayyana cikakken kwarin gwiwa kan ƙwarewar Janar Musa wajen jagorantar Ma’aikatar Tsaro tare da ƙara inganta tsarin tsaron Najeriya.