NLC ta sa zare da gwamnati kan yajin aikin ASUU
Published: 20th, October 2025 GMT
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin makonni huɗu domin ta warware duk wata tankiya da ke tsakaninta da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) da sauran ƙungiyoyin jami’o’i da na manyan makarantu.
Shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin ganawa da ’yan jarida a Labour House da ke Abuja.
Ajaero ya ce, idan gwamnati ta gaza kammala tattaunawa da ƙungiyoyin cikin wa’adin da ta bayar, NLC ba za ta yi wata-wata ba wajen ɗaukar matakin da ya dace ta hanyar amfani da dukkan wani tanadi da doka ta yi.
Ya kuma bayyana cewa sun gano cewa wasu ƙungiyoyin haɗin gwiwa a ƙarƙashin NLC suna ganawa da jami’an gwamnati ba tare da izini ko umarni daga uwar ƙungiya ba, wanda shi ne dalilin da ya sa yarjejeniyoyi da dama ba a cika su ba.
Jawabin da Kwamared Ajaero ya yi na zuwa ne bayan taron da NLC ta yi da shugabannin ƙungiyoyin jami’o’i ciki har da ASUU, SSANU, NASU da NAAT.
A makon da ya gabata ne ASUU ta ayyana yajin aikin gargaɗi na makonni biyu, bayan ƙarewar wa’adin na kwanaki 14 da ta bai wa gwamnati, dangane da batutuwan da suka shafi walwala da jin daɗin ma’aikata, albashi, da aiwatar da yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya tun a shekarar 2009.
Sai dai Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya ce bai kamata ASUU ta shiga yajin aiki ba, domin a cewar tattaunawa ta ta yi nisa, kuma gwamnati ta saki Naira biliyan 50 na kuɗaɗen alawus ɗin malaman jami’o’i, tare da ware Naira biliyan 150 a cikin Kasafin 2025 domin gyaran jami’o’in.
A yayin taron da NLC ta gudanar, Kwamared Ajaero ya jaddada cewa daga yanzu, ƙungiyar ƙwadago ko wata ƙungiya a ƙarƙashinta ba za ta sake ganawa da jami’an gwamnati ba tare da izini ba, musamman waɗanda ke da alhakin aiwatar da yarjejeniyoyin da ake sanya hannu a kai.
Ya kuma soki matakin da gwamnatin ta ɗauka na amfani da dokar “ba aiki, ba albashi” kan mambobin ASUU yana mai cewa:
“Mun yanke shawarar bai wa gwamnati wa’adin mako huɗu domin ta kammala dukkan tattaunawa a wannan bangare. Mun fara da ASUU, amma matsalolin sun wuce na ASUU kaɗai.
“Idan bayan mako huɗu ba a kammala komai ba, za mu kira taron gaggawa na ƙasa domin ɗaukar matakin gama-gari, wanda dukkan ma’aikata da ƙungiyoyi a faɗin ƙasa za su shiga ciki.”
Ya ƙara da cewa, “Zamanin sanya hannu kan yarjejeniyoyi da yi wa ƙungiyoyin da ke neman haƙƙinsu barazana ya ƙare.
“Wannan batu na ‘ba aiki, ba albashi’ daga yanzu zai zama ‘ba albashi, ba aiki’. Saboda mun gano cewa fiye da kashi 90 cikin 100 na yajin aikin da ake yi a ƙasar nan na faruwa ne saboda rashin cika ƙa’idar yarjejeniyoyi.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yajin aiki
এছাড়াও পড়ুন:
Sanata Barau Ya Kai Ziyarar Gani Da Ido Aikin Da Ake Yi A AKTH
Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada kudirinta na inganta harkar kiwon lafiya a fadin kasar nan, daidai da manufar sabunta kudiri na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wato Renewed Hope Agenda.
Wannan tabbacin ya fito ne daga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, yayin da yake ziyarar duba ayyukan gine-gine da ke gudana a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), wanda shi ne ya tallafa wajen samar da su.
Yayin da yake magana da ’yan jarida a lokacin ziyarar, Sanata Barau ya ce wadannan ayyuka na da nufin kara karfin cibiyoyin kiwon lafiya a cikin gida, tare da rage yawan tafiyar da ake yi zuwa kasashen waje domin neman magani, ta hanyar samar da ingantattun kayan aiki a asibitocin cikin gida.
“Wadannan shirye-shirye suna cikin cikakkiyar manufa ta Shugaba Tinubu ta farfado da sashen kiwon lafiya,” in ji shi. “Nigeria na da kwararrun ma’aikatan lafiya, kuma idan aka samar musu da ingantattun kayan aiki, za a karfafa gwiwarsu, kuma za mu iya cimma burin kasa wajen ingantaccen tsarin kiwon lafiya.”
Dan majalisar ya kara da cewa, idan an kammala wadannan ayyuka, za su taimaka wajen kara ingancin ayyukan asibitin, tare da bai wa jama’a damar samun kulawar lafiya ta zamani da inganci.
A nasa bangaren, Babban Daraktan Asibitin, Farfesa Abdulrahman Sheshe, ya nuna godiya bisa wannan taimako, yana mai cewa ayyukan suna tafiya yadda ya kamata, kuma ana sa ran kammalawa da kaddamar da su kafin shekarar 2026.
A cewarsa, ayyukan sun hada da gina Cibiyar Nazarin Cutar Zuciya da Kwakwalwa (Cardio-Cerebral Center), Cibiyar Kula da Yara (Pediatric Center), da masaukan daliban jinya, da sauran muhimman gine-gine.
“Wadannan sabbin cibiyoyi za su kara yawan gadon marasa lafiya, kuma za su ba mu damar gudanar da ayyukan da ba mu iya yi ba a baya,” in ji Farfesa Sheshe.
Ya kara da cewa, sabbin cibiyoyin za su kara ingancin ayyuka, tare da karfafa matsayin asibitin wajen zama jagora a harkar kiwon lafiya a yankin.
Abdullahi Jalaluddeen