Aminiya:
2025-12-05@21:19:02 GMT

Fashewar tankar mai ta yi ajalin mutum 30 a Neja

Published: 21st, October 2025 GMT

Ana fargabar cewa aƙalla mutum 30 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon fashewar wata tankar man fetur a ƙauyen Essa da ke hanyar Agaei zuwa Bida a ƙaramar hukumar Katcha ta Jihar Neja.

Aminiya ta ruwaito cewa, akwai kuma kimanin mutum 40 da suka jikkata wadanda suka wawason kwalfar man fetur bayan kifewar tankar.

Bayanai sun ce da misalin karfe 11 na safiyar wannan Talatar ce tankar ta kife a titin Essan da aka bayyana cewa lalacewar hanyar ce ta haddasa hatsarin.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Neja tankar mai

এছাড়াও পড়ুন:

Gobara ta kashe mata da miji da ’ya’yansu 3 a Katsina

Wata gobara da ta tashi da safiyar Litinin ta kashe magidanci da matarsa da ’ya’yansa uku a unguwar Kofar Sauri da ke cikin garin Katsina.

Wadanda gobarar ta rutsa da su sun haɗa da Muhammad Habibu mai shekara 35, matarsa Fatima Muhammad, da ’ya’yansu uku; Khadija, Abubakar, da Aliyu, wadanda dukkansu suka ƙone har lahira.

Majalisar Dokokin Akwa Ibom ta yi fatali da ƙudurin neman hana cin naman kare Yau Majalisar Dattawa za ta tantance sabon Ministan Tsaro

Gobarar ta kuma lalata dukiyoyi da darajarsu ta kai miliyoyin naira.

An gano cewa Muhammad Habibu ma’aikaci ne na wucin gadi a hukumar ruwa ta jihar Katsina kafin rasuwarsa.

Kodayake ba a tabbatar da ainihin dalilin gobarar ba tukuna, mazauna yankin suna zargin ta faru ne sakamakon tashin wuta mai ƙarfi lokacin da aka dawo da lantarki a yankin.

An ce gobarar ta fara ne daga falon gidan sannan ta bazu cikin sauri zuwa sauran sassan gidan, yayin da iyalin ke tsaka da sharer barci.

Bayanai sun ce lokacin da suka fahimci hatsarin, wutar ta riga ta toshe dukkan hanyoyin fita.

Ɗan uwa ga waɗanda suka rasu, Kasim Aliyu, ya ce da misalin ƙarfe 3:00 na safe ya ji muryar wata mace daga nesa tana karanta kalmar shahada: “Innalillahi wa inna ilayhi raji’un.” Da farko ya ɗauka al’ada ce, sai da misalin ƙarfe 3:30 na safe ya fara jin akwai matsala.

Kasim ya ƙara da cewa: “Mai gidan ƙanina ne ubanmu ɗaya. Gobarar ta kama gidan da misalin ƙarfe 3:00 na safe. Na ji wani abu a lokacin amma ban gane ba sai da aka kira ni da misalin ƙarfe 4:00 na safe aka shaida min cewa ƙanina da iyalinsa gaba ɗaya sun mutu a gobarar. Allah ya jikan su.”

Shaidun gani da ido sun ce ƙoƙarin makwabta da masu taimakon gaggawa wajen kashe gobarar ya ci tura.

Sun yi korafin cewa jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Katsina sun iso daga baya amma zuwan nasu bai yi wani tasiri ba sosai.

Wani mazaunin yankin, Musa Hamza, ya ce: “Ina ganin lokacin da hukumar kashe gobara ta iso, mutanen cikin gidan sun riga sun mutu a gobarar. Amma zan iya cewa sun yi iya ƙoƙarinsu wajen kashe wutar, sai dai ba su samu nasarar ceto iyalin ba. Allah ya jikan su.”

Wani makwabci, Magaji Bala, ya yi korafi cewa mazauna yankin sau da yawa suna shafe kwanaki ba tare da lantarki ba, sai kuma tashin wuta mai ƙarfi ya jawo barna duk lokacin da aka dawo da wuta.

“Irin wannan lamari ya taɓa faruwa a wasu sassan garin Katsina. Kwanan nan ma kusan irin haka ya faru. Wannan ya sa dole mutane su yi taka-tsantsan,” in ji shi.

Da aka tuntubi Babban Jami’in Kashe Gobara na jihar Katsina, Rabe Audi Kurmuyal, ya tabbatar da cewa ma’aikatansa sun kashe gobarar, sabanin ikirarin da ake yi cewa sun iso daga baya.

Wasu mazauna sun dora laifin kan matsalar sauyin wuta da ake yawan samu daga kamfanin rarraba na shiyyar Kano (KEDCO), suna cewa yawan katsewa da dawowa da ƙarfin lantarki mai yawa na lalata kayan lantarki.

Sai dai kamfanin ya musanta zargin, inda ya ca ba zai yiwu a ce laifinsu ba ne, kasancewar gidan shi kadai ya kone a unguwar mai gidaje sama da 5,000.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dorinar ruwa ta kashe mutum 2, ta jikkata 6 a Gombe
  • Ina nan a PDP duk da sauya sheƙar ’yan majalisar Ribas — Wike
  • Jami’an tsaro sun kama masu garkuwa da mutane 7 a Gombe
  • Najeriya ta shigo da tataccen man fetur na tiriliyan 12.8 cikin watanni 15
  • NAPTIP ta daƙile yunƙurin safarar mutum 7 daga Kano zuwa Saudiyya
  • MDD ta bukaci a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma janyewa daga Tuddan Golan na Siriya
  • Mutum 6 sun rasu, 13 sun jikkata a hatsarin mota a Kogi
  • ’Yan sanda sun kama mutum 28 kan zargin lalata mata da yara a Yobe
  • CBN ya kara yawan kudin da mutum zai iya cirewa a mako zuwa N500,000
  • Gobara ta kashe mata da miji da ’ya’yansu 3 a Katsina