Dembele ya dawo PSG bayan jinyar makonni
Published: 20th, October 2025 GMT
Zakaran kyautar Ballon d’Or ta bana, Ousmane Dembele, ya shiga cikin sahun ’yan wasan ƙungiyar Paris Saint-Germain (PSG) da za ta kece raini da Bayer Leverkusen a gasar Champions League, bayan ya shafe makonni shida a jinya.
Dembele, wanda ya samu rauni a cinya yayin da yake wakiltar ƙasar Faransa a farkon watan Satumba, ya shafe makonni yana jinya a cibiyar lafiya ta musamman da ke Qatar, kafin komarwarsa atisaye a makon da ya gabata.
Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa AFP ya ruwaito cewa, kociyan PSG, Luis Enrique, zai yi farin ciki da dawowar Dembele, la’akari da yadda ƙungiyar ta ke fuskantar ƙalubalen ’yan wasa maau fama da rauni a bana.
Dembele mai shekaru 28 bai haska ba a wasan da PSG ta yi 3–3 da Strasbourg ba a gasar Ligue 1 a ranar Juma’a, amma ana sa ran zai taka rawa yayin da PSG ke fatan samun nasarar wasanni uku a jere a Gasar Zakarun Turai idan ta je baƙunta Jamus a gobe Talata.
Loic Bade, ɗan wasan bayan Leverkusen kuma abokin Dembele a ƙungiyar Faransa, ya ce babu wani “sirri na musamman” wajen taka wa Dembele birki.
A yayin da PSG ke murnar dawowar Dembele, tana kuma maraba da dawowar ‘yan wasan gabanta — Desire Doué da Khvicha Kvaratskhelia.
Sai dai har yanzu ƙungiyar na rashin ‘yan tsakiyarta, Fabian Ruiz da Joao Neves, duk da cewa kyaftin Marquinhos, wanda shi ma ya dawo daga jinya, za a tafi da shi Jamus.
A nasa ɓangaren, kocin Leverkusen, Kasper Hjulmand, wanda ya karɓi ragamar ƙungiyar bayan sallamar Erik ten Hag a watan Satumba, ya ce tsarin matsin lamba da PSG ke amfani shi a tamaula “makami ne amma kuma yana da haɗari idan ta kuskure.”
Leverkusen, wadda ta lashe Bundesliga a shekarar 2024, ta tashi kunnen doki da FC Copenhagen da PSV Eindhoven a wasannin farko na gasar Champions League na bana.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Bayer Leverkusen jinya
এছাড়াও পড়ুন:
An aiwatar da sauye-sauye a wasu muhimman kwamitocin Majalisar Dattawa
Majalisar Dattawa ta sanar da aiwatar da sauye-sauye a wasu muhimman kwamitocinta waɗanda suka haɗa har da na tsaro da na tattara bayanan sirri, sakamakon ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta.
Shugaban Majalisar Dattawan, kuma shugaban kwamitin majalisar kan harkokin zaɓe, Sanata Godswill Akpabio ne ya sanar da hakan yayin zaman na yau Talata.
Mutane 9,854 na ɗauke da cutar AIDS a Yobe Tinubu ya naɗa Janar CG Musa sabon Ministan Tsaron NijeriyaA sabbin sauye-sauyen da majalisar ta aiwatar, Sanata Yahaya Abdullahi daga Jihar Kebbi ya zama shugaban kwamitin tsaro da na tattara bayanan sirri bayan ya bar kujerar kwamitin tsare-tsare na ƙasa.
An naɗa Sanata Shehu Buba daga Bauchi a matsayin shugaban kwamitin harkokin Kiwo, bayan cire shi daga kujerar kwamitin tsaro da tattara bayanan sirri a makon da ya gabata.
Haka kuma, Sanata Mustafa Musa daga Yobe ya karɓi ragamar shugabancin kwamitin tsare-tsare na ƙasa.
A ɓangaren kwamitin Sojin Sama kuma, Sanata Osita Ngwu daga Enugu wanda shi ne mataimakin shugaban Marasa Rinjaye a Majalisa ya zama muƙaddashin shugaban kwamitin bayan rashin lafiya ta hana tsohon shugaban ci gaba da aiki.
Majalisar ta ce waɗannan sauye-sauyen na da nufin ƙarfafa aikin sa ido da inganta duk wasu hanyoyin ɗaukar mataki kan batutuwan tsaro da ke tasowa a faɗin ƙasar.