Sheikh Qasim: Natanyahu Ya Zubar Da Jini Mai Yawa Amma Babu Lamuni Ga Amincin Isra’ila Nan Gaba
Published: 22nd, October 2025 GMT
Shugaban kungiyar Hizbullah Ta Kasar Lebanon Sheikh Na’em Qasim ya bayyana cewa, ya bayyana cewa Firai ministan HKI Benyamin Natanyahu ya zubar da jinin mutanen yankin yammacin Asia da dama, amma wannan bai bashi lamunin cewa haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) zata zauna lafiya a yankin nan gaba ba.
Tashar tal;abijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban kungiyar yana fadar haka a jiya Talata a wani bikin kaddamar da littafi wanda yake bayyana ra’yin Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminaie dangane da wakoki da kidekide.
Yace: Duk tare da zubar da jinin mutanen yankin a duk a lokacinda ya ga dama, Netanyahu ba zai ce yana da lamuni na zaman lafiya ga HKI a nan gab aba.
Sheikh Qassem ya bayyana cewa gwamnatin HKI ta kasa cimma manufarta ta mamayar kasar Lebanon, duk tare da taimakon da ta samu daga manya-manyan kasashen duniya don cimma wannan manufar.
Ya ce HKI bayan fara yakin tufanul Aksa a shekara ta 2023, ta fuskanci turjiya mai tsanani daga kungiyar Hizbullah a yakin da kungiyar ta shiga don tallafawa Gaza, ta kuma ga yadda kungiyar ta maida yakin ya zama mafi muni ga yake-yaken HKI a tarihin yankin. Kuma ta gamu da asarar sojoji da makamanta, musamman tankunan yakin mirkava. Har zuwa watan Nuwamba na shekarar da ta gabata, a lokacinda tanemi tsagaita wuta.
Sheikh Qassem ya yi gargadi da Amurka da kuma HKI kan shirinsu na Isra’ila babba, don kasar Lebanon ba zata kasance cikin shirinsu ba.
Kafin haka dai Natanyahu ya gabatar da shirin ‘Isra’ila babba’ wanda ya hada da kasashen Lebanon, Jordan, Siriya , Iraqi Masar da kuma Saudiya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Aragchi Da Guterres Sun Tattauna Kan Gaza Da Rikicin Yemen Ta Wayar Tarho October 22, 2025 Rasha da Habasha sun tattauna kan karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu a fannin nukiliya October 22, 2025 Sayyed al-Houthi: Mun shirya dawowa fagen daga idan Isra’ila ta ci gaba da kisan kiyashi a Gaza October 22, 2025 Nigeria: “Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Neman Sakin Jagoran ‘Yan Awaren Biafara October 21, 2025 HKI Tana Ci Gaba Da Hana Wa Falasdinawa Abinci October 21, 2025 An Yi Fashi Da Makami A Gidan Adana Kayan Tarihin ” Louvre” Na Kasar Faransa October 21, 2025 Yemen : An yi jana’izar babban hafsan sojin kasar Shahid al-Ghamari a Sana’a October 21, 2025 Iran da Iraki sun bukaci duniya da ta dakatar da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza October 21, 2025 Equatorial Guinea ta zargi Faransa da karan-tsaye wa zaman lafiya a kasar October 21, 2025 Faransa : Sarkozy, ya fara zaman gidan yari na shekara 5 October 21, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Kira Yi Gwamnatin Canada Da Ta Kama Olmert Da Livini Na “Isra’ila
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasar Canada sun shigar da kara ga jami’an ‘yan sandan kasar, da kuma ma’aikatar shari’a da su kama tsohon Fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Ehud Olmert da kuma ministan harkokin waje Tzipi Livni bisa rawar da su ka taba a baya a laifukan yaki a Gaza a tsakanin 200-2009.
Kungiyoyin sun bukacin ganin an fitar da sammacin kamo ‘yan sahayoniyar biyu a bisa dogaro da dokokin kare hakkin dan’adama da laifukan yaki na kasar Canada, saboda kasar tana karkashin yarjejeniyar Geneva ta 4 da ta bukaci kasashe su hukunta masu irin wadannan laifukan.
Bugu da kari, kungiyoyin sun ce Olmert wanda ya yi fira minista daga 2006 zuwa 2009, shi ne mai rike da mukami na koli a lokacin hare-haren soja da su ka kashe fararen hula da lalata muhimman cibiyoyi. Haka nan kuma a wancan tsakanin sojojin Haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi amfani da makamin Phosphorus mai fitar da farin hayaki da aka haramta amfani da shi a yake-yake. Sojojin na mamaya sun kuma rusa gidaje da lalata tsarin magudanan ruwa na kiwon lafiya, kamar kuma yadda su ka yi wa fararen hula da dama kisa ba tare da shari’a ba. Bugu da kari, sun hana shigar da kayan agaji zuwa yankin Gaza a wancan lokacin.
Ita kuwa Livini ta kasance memba a cikin karamar majalisar tsaro wacce ta taka rawa wajen shatawa sojoji ta’asar da su ka yi, ta kuma furta cewa, martanin da ya kamata “Isra’ila” ta mayar wa Falasdinawa ya kamata ya zama ” Na Hauka.”
Dama dai mutanen biyu suna da wata shari’ar da aka kai su kara a gaban kotuna daban-daban na kasashen turai. Kuma a 2009 ne wata kotu a Birtaniya ta fitar da sammaci a kamo su.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Kashe Shugaban ‘Yan Dabar Gaza “Abu Shabab” Da Isra’ila Ke Goyon Baya December 4, 2025 Iran : Jagora Ya Bayyana Ra’ayin Musulunci Kan Hakkokin Mata December 4, 2025 Taron IMO : Tehran Ta Yi Watsi Da Zarge-zargen Isra’ila Marasa Tushe December 4, 2025 MDD ta nemi a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma Tuddan Golan December 4, 2025 Rundunar Ruwa ta IRGC na Gudanar Da Atisayen Soja a Tekun Fasha December 4, 2025 Dan wasan Taekwando Na kasar Iran Ya Samua Lambar Yabo Ta Zinariya December 4, 2025 Hamas Za ta Mikawa Isra’ila Samfurin Da Aka Samu A Karkashin Burabutsai A Gaza December 4, 2025 Iran: Tsaron Yankin Tekun Fasha Jan Layi Ne Da Za’a Fuskanci Mayar Da Martani Adan Aka Taba Shi December 4, 2025 Kungiyoyin Kare Hakkin Dan Adam Sun Kira Ga Kasar Kanada Ta Kama Olmert Da Livni December 4, 2025 Majalisa Ta Tabbatar Da Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro December 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci