Aminiya:
2025-10-21@16:31:44 GMT

Tinubu ya naɗa sabon Minista

Published: 21st, October 2025 GMT

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa sabon Minista a gwamnatinsa.

Karin bayani na tafe..

.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu Ya Nemi Alkalai Su Kara Kaimi Wajen Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Alkalan Najeriya su kasance masu gaskiya, rikon amana da tsoron Allah wajen yanke hukunci. Ya ce duk wata al’umma tana fara rushewa ne idan bangaren shari’a ya lalace.

Ya bayyana cewa gwamnati na kokarin inganta walwala da albashin Alkalan domin karfafa ikon cin gashin kansu.

Da yake bude taron bita na EFCC da NJI a Abuja, Shugaban  wanda Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta  ya ce adalcin Alkalai ne ginshikin ci gaban kasa.

Ya nuna damuwa kan yadda ake jinkirta shari’o’in manyan laifukan rashawa, yana mai cewa an fi hanzarta shari’ar masu laifin yanar gizo.

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa ba a taba kare kowa saboda siyasa a gwamnatinsa ba, inda ya bayyana cewa EFCC ta samu nasarar gurfanar da mutane sama da 7,000 tare da karbo kadarori fiye da Naira Biliyan 500 cikin shekaru biyu.

Ya bukaci Alkalan su ci gaba da koyon sabbin dabaru, musamman wajen shari’o’in yanar gizo da laifukan kuɗi, tare da tunatar da su cewa cin hanci yana shafar kowa.

A nata bayanin Babbar Alkalin Najeriya, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta bukaci Alkalan su tabbatar da yin adalci ba tare da jinkiri ko son zuciya ba.

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya yaba da hadin kan da Alkalan je basu, yana mai cewa nasarorin da aka samu sun nuna jajircewa wajen yaki da cin hanci da rashawa.

 

Daga Bello Wakili

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu
  • Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira
  • Tinubu Ya Nemi Alkalai Su Kara Kaimi Wajen Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa
  • Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Mukaman Gwamnatin Tinubu inji  Shugaban FCC
  • Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC
  • Sojojin Najeriya: Rahotanni Dangane Da Juyin Mulki Wa Shugaba Tinubu Ba Gaskiya Bane
  • An kama sojoji 20 kan yunƙurin kifar da gwamnatin Tinubu
  • DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki