Dan Wasan Barkwanci A Finafinan Indiya, Asrani Ya Rasu
Published: 20th, October 2025 GMT
Fitaccen jarumin barkwancin finafinan Indiyan nan Asrani ra rasu.
Asrani, wanda asalin sunansa shi ne Govardhan Asrani, ya rasu yana mai shekaru 84, kuma ya shafe sama da shekara 50 yana fitowa a finafinan Indiya, inda ya fito a finafinai sama da 350.
Dan wasan finafinan, ya shahara wajen taka rawar barkwanci da kuma ƙaramin jarumi wanda ake kira da mai taimaka wa jarumi wato supporting actor.
Ya karbi lambobin yabo da dama da suka hada da jarumin da yafi kowa iya barkwanci wanda kamfanin Film Fare ya ba shi.
Ya mutu ya bar matarsa wadda ita ma jaruma ce wato Manju Asrani da kuma ɗansa Naveen Asrani.
Ya yi fina-finai da jarumai da dama da suka hada Amita Bachchan da Dharamendra da Jeetandra da Shatugan Sinha da Rajesh Khanna da Rishi Kapoor da Vinod Khanna da Akshay Kumar, da Shahrukh Khan da Aamir Khan da Salman Khan da Ajay Devgan da Sanjay Dutt da dai sauransu.
Bbc
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Rikicin Kungiyoyin Asiri Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Wani Matashi A Jihar Kwara
Daga Ali Muhammad Rabi’u
An samu mummunan rikici tsakanin mambobin ƙungiyoyin asiri wanda ya shafi tsofaffin daliban kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kwara da ke Ilorin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa dalibin mai suna Oyelade Olawale wanda ya karanci aikin Injiniya a fannin Gine-gine, ya rasu ne a yayin wannan rikici na kungiyoyin asiri.
An samu labarin cewa an kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da hannu a tarzomar da ta faru a Kwalejin.
A cikin wata sanarwa, Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Kwalejin, Halima Garba, ta tabbatar da mutuwar matashin da kuma kama wasu mutane da ake zargi da hannu a rikicin.
Sanarwar ta yi kira ga dalibai da al’umma su rika kai rahoton duk wani abin da suke zargin zai iya haddasa fitina ga hukumomin da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a makarantar.