Jihar Jigawa Za Ta Kashe Sama Da Naira Biliyan 2 Wajen Binciken Albarkatun Kasa
Published: 22nd, October 2025 GMT
Majalisar zartarwa ta jihar Jigawa ta amince da kashe Naira biliyan 2.55 domin gudanar da binciken na musamman, wanda zai mayar da hankali kan albarkatun mai, gas, da sinadarin uranium, tare da cikakken binciken kimiyyar kasa kan ma’adinai a fadin jihar.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya fitar, ya bayyana cewa wannan muhimmin shiri na gwamnatin yanzu babban mataki ne na gaba wajen cika alkawarin gwamnati na ganowa da kuma amfani da albarkatun kasa masu tarin yawa da ke cikin jihar Jigawa.
A cewarsa, wannan bincike zai samar da bayanai masu muhimmanci game da ma’adinai, da mmn fetur da iskar gas da ke karkashin kasa, wanda zai taimaka wajen yanke shawara mai inganci, jawo hankalin masu zuba jari, da kuma tallafawa ci gaban tattalin arziki mai dorewa.
Ya kara da cewa, majalisar ta sake jaddada kudirin gwamnati na bunkasa tattalin arziki ta hanyar bincike da hakar albarkatun kasa bisa tsari da kuma amfani da bayanai na kimiyya.
Sagir ya jaddada cewa, ta hanyar zuba jari a nazarin kimiyyar kasa mai inganci, jihar na da burin samar da sababbin hanyoyin samun kudaden shiga, bunkasa damar samar da ayyukan yi ga matasa, da kuma shimfida tubalin ci gaban masana’antu.
Ya kara da cewa, binciken albarkatun kasa, da mai da iskar Gas zai kasance a hannun kwararrun masana, bisa bin ka’idoji da dokokin kasa da kasa, domin tabbatar da sahihanci, inganci, da amfani mai tsawo na sakamakon da za a samu.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Albarkatun Kasa Jigawa albarkatun kasa
এছাড়াও পড়ুন:
Rundunar ‘Yan Sanda A Jihar Zamfara Ta Gargadi Direbobi Game Da Rufe Lambar Mota
Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Zamfara ta gargaɗi direbobi da sauran jama’a game da rufe lambobin motoci, musamman a cikin garin Gusau, babban birnin jihar.
Gargaɗin ya biyo bayan ƙaruwa da ake samu na rahotanni da kuma lura da direbobi da ke tafiya da lambobin motoci a rufe, wanda rundunar ta bayyana a matsayin karya dokokin hanya da ke kawo barazana ga tsaro da zaman lafiya.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar, rundunar ta bayyana cewa wannan dabi’a tana nuna ƙoƙarin kaucewa binciken jami’an tsaro tare da yiwuwar taimaka wa aikata laifuka.
Sanarwar ta ƙara da cewa, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya jaddada cewa rundunar ba za ta sake lamuntar irin wannan aiki ba.
Ya bayyana cewa an umarci jami’an rundunar da su fara aiwatar da tsauraran matakan doka, inda ya ƙara da cewa kowace mota da aka samu ta rufe lambar mota za a kama ta tare da gurfanar da mai motar a gaban doka.
CP Maikaba ya kuma shawarci jama’a da direbobi a fadin jihar Zamfara da su bi dokokin hanya tare da yin haɗin kai da ‘yan sanda wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya.
Ya tabbatar wa jama’a da cewa rundunar ‘yan sandan za ta ci gaba da jajircewa wajen kiyaye doka da oda, tare da ƙarfafa al’umma da su rika ba da rahoton duk wani abin da suke zargi ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
Daga Aminu Dalhatu