Wani Masani Dan Iran Ya Samu Lambar Yabo Ta WHO Don Kirkiro Abin Da Zai Kare Cututtuka Da Basa Yaduwa
Published: 22nd, October 2025 GMT
Dr Majid Ghayour Mubarhan kwararre kuma farfesa a jami’ar kiwon lafiya ta birnin mashahada ya samu kyautar hukumar WHO na gabashin meditareniya saboda namijin kokarin da yayi na kirkiro abin da zai kula da kuma kare kamuwa da cututtuka da basa yaduwa, kamar cutar kansa ciwon zuciya da kuma ciwon Sugar.
Wannan kyautar tana nuna irin ci gaban da Iran ta samu ne a bangaren kimiyyaa yankin duk da takunkumi da kuma takurawar da take fuskanta daga bangaren kasashen turai dake takaita halartar masana kimiyyar kasar hallara a matakin kasa da kasa.
A duk shekata hukumar lafiya ta duniya tana bada kyauta ga duk wani masanin kimiya da yayi kwazo wajen kirkiro wata fasaha a bangaren lafiyar gama gari, da kare kamuwa daga cututtuka, kyautar wannan shekarar wata cibiyar bada kyaututtuka ne dake kasar Kuwaiti ta samar, kuma aka bawa Dr Ghayour mobarhan saboda gudunmawar da ya bayar wajen kare kamuwa da cutar zuciya,
Sai dai saboda rashin samun visa a akan lokaci bai samu halartar wajen taron ba, amma Dr Riza’i mataimakin ministan lafiya na Iran ya karbi kyautar a Madadinsa,
Dr Ghayour shi ne wanda ya kafa cibiyar kula da kiwon lafiya ta duniya ta Unesco a iran babbar cibiyar hadin guiwa ta bincike a yankin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Majalisar Najeriya Ta Amince Da Dokar Daurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Kananan Yara Fyade October 22, 2025 Birtaniya Ta Cire Kungiyar Tahrirush -Sham Daga Jerin Yan Ta’adda October 22, 2025 China Ta Kammala Gina Cibiyar Adana Bayanai Masu Amfani Da Karfin Iska October 22, 2025 Iran Ta Godewa Rasha Game Da Goyon Bayan Da Ta Bata A Kwamitin Sulhu Na M D D October 22, 2025 Sudan: Jirgin ‘Drone’ Ya Fada Kan Tashar Jiragen Sama Na Khurtum Kafin A Sake Bude Ta October 22, 2025 Sheikh Qasim: Natanyahu Ya Zubar Da Jini Mai Yawa Amma Babu Lamuni Ga Amincin Isra’ila Nan Gaba October 22, 2025 Aragchi Da Guterres Sun Tattauna Kan Gaza Da Rikicin Yemen Ta Wayar Tarho October 22, 2025 Rasha da Habasha sun tattauna kan karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu a fannin nukiliya October 22, 2025 Sayyed al-Houthi: Mun shirya dawowa fagen daga idan Isra’ila ta ci gaba da kisan kiyashi a Gaza October 22, 2025 Nigeria: “Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Neman Sakin Jagoran ‘Yan Awaren Biafara October 21, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Akwai hannun ƙasashen waje a rashin tsaron Najeriya —Sheikh Gumi
Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Mahmud Abubakar Gumi, ya yi zargin cewa ƙasashen waje na taimaka wa ƙungiyoyin ’yan ta’adda Najeriya.
Sheikh Ahmad Gumi ya danganta ƙaruwar matsalar tsaro a Najeriya a baya-bayan nan da irin maganganun da ƙasashen waje suka riƙa yi a kai.
A yayin wata hira da BBC Hausa, malamin ya bayyana cewa yanayin taɓarɓarewar tsaro a baya-bayan nan ya nuna akwai alamun hannun ƙasashen waje a ciki.
Tsohon hafsan sojin, ya ce matsalar tsaro ta ragu a sassan ƙasar nan sai baya-bayan nan da ƙasashen waje suka fara magana a kai.
Ya bayyana cewa an samu aminci a hanyar Abuja zuwa Kaduna, wadda baya ta kasance tarkon mutuwa, amma sai kwanan nan matsalar ta fara dawowa bayan maganganun ƙasashen waje.
Ya ce manoma a yankin Birnin Gwari sun ci gaba harkokin nomansu, bayan samuwar zaman lafiya, abin da ya gare su a baya lokacin da ake ganiyar rashin tsaro.
“Akwai maganar da ƙasashen waje suka yi, kuma mun jima muna cewa ƙasashen waje ke taimak aa ’yan ta’adda da irin muggan makamai da suke amfani da su.
“Akwai attajirai da shugabannin ƙasashen waje da ke yin katsalandan ga harkokin wasu ƙasashe.”
Don haka ya ce ba abin mamaki ba ne samun ƙaruwar hare-haren ta’addanci da aka yi a Najeriya bayan maganganun ƙasashen waje a kan matsalar tsaro a ƙasar.
Kan matsayinsa game da tattaunawa da ’yan bindiga, ya ce: “Kowa ya san su. Amma abin da mutane ba sa magana a kai shi ne: me ya sa mutanen da muka taɓa rayuwa lafiya da su suka juya mana baya suka zama annoba a cikin al’umma? Akwai dalili.”
“Mutane biyu ne ba za a yi mamakin abin da suke yi ba: mahaukaci da jahili. Babu wani bayani da za ka yi musu da zai sa su fahimci cewa aikata laifi ba daidai ba ne.”
“Babu abin da suka sani face ɓarna. Amma wa zai yi musu nasiha su daina? Lokacin da muka yi ƙoƙarin kusantar su muka gaya musu cewa haramun ne sata, ƙwace dukiyar mutane haramun ne, yin garkuwa da mutane haramun ne, gwamnatin da ta gabata ba ta ba mu goyon baya ba.
“Da an ba da wannan goyon bayan, watakila da zuwa yanzu an warware wannan matsala.”
Sheikh Gumi ya yi gargaɗi cewa muddin ba a magance tushen matsalar ba, to akwai sauran rina a kaba.
Ya kuma ja hankali jama’a su fahimci cewa matakin yaki da ta’addanci da ya ɗauka, musamman neman sulhu da ’yan bindiga ba, ba ya nufin goyon bayan ayyukansu.
“Addininmu ya haramta zalunci; Duk abin da muke yi, muna yi ne domin Allah,” in ji shi.