Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu
Published: 20th, October 2025 GMT
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Siyasa Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027 October 17, 2025
Siyasa Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu October 16, 2025
Manyan Labarai Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson October 16, 2025
এছাড়াও পড়ুন:
Lewandowski Ba Zai Buga Wasan El Classico Ba
Dan wasan gaba na Barcelona Robert Lewandowski ba zai buga wasan hamayya tsakanin FC Barcelona da Real Madrid wanda ake yi wa take da El Classico ba bayan da zakarun na Sifaniya suka gano cewa yana fama da rauni a kafarsa ta hagu, dan wasan mai shekaru 37 ya samu rauni ne a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da Poland ta buga da kasar Lithuania ranar Lahadi.
Lewandowski yana da tsagewar tsoka a cikin femoris na cinyarsa ta hagu,” in ji Barcelona a cikin wata sanarwa, yayin da kafofin yana labarai na Sifaniya suka ruwaito cewa zai iya yin jinyar makonni hudu zuwa shida, Barcelona za ta kara da Real Madrid wadda ke jagorantar gasar La Liga a wasan Clasico a Santiago Bernabéu a ranar 26 ga Oktoba, yayin da kuma dan wasan ba zai buga wasannin gasar cin kofin zakarun Turai da za ta yi da Olympiakos da Club Brugge da sauran wasannin ba.
Mai tsaron gida Joan Garcia da dan wasa Dani Olmo suma ba za su buga wasan na El Classico tare da Real Madrid ba, amma matashin dan wasan gefe Lamine Yamal ya dawo atisaye ranar Litinin bayan ya fara murmurewa daga raunin da ya samu, an tura dan wasan Barca Ferran Torres gida daga sansanin ‘yan wasan kasar Sifaniya saboda rashin jin dadin jiki, amma kungiyar ta tabbatar a ranar Litinin cewa bai samu rauni ba,
Torres ya jagoranci Barca a lokuta daban-daban a kakar wasa ta bana, yayin da Lewandowski ya kan yi wasa a matsayin wanda zai maye gurbinsa daga benci.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA