Aminiya:
2025-10-20@21:18:56 GMT

An maka mahaifi a kotu kan cefanar da gidan ɗansa a Kano

Published: 20th, October 2025 GMT

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a unguwar Danbare a Jihar Kano, ta gurfanar da wani mutum mai suna Malam Shaddadu bisa zargin sayar da gidan ɗansa ba tare da izini ba.

Ɗan mutumin wanda ya gabatar da ƙara, Muhammad Shaddadu, ya shaida wa kotu cewa, lamarin ya samo asalin ne tun bayan da mahaifinsa ya saya wa wasu ‘yan uwansa biyu da suke uba ɗaya babura masu kafa uku da aka fi sani da Adaidata Sahu.

APC ta rage wa Mata kuɗin tsayawa takara a Borno Dembele ya dawo PSG bayan jinyar makonni

Sai dai daga baya, tsautsayi ya rutsa da ɗaya daga cikinsu wanda ɓata-gari suka kai masa hari har suka kashe shi, kuma suka yi awon gaba da baburinsa.

Muhammad ya bayyana cewa kwatsam sai mahaifinsa ya ɗora masa alhakin faruwar lamarin, inda ya kai shi har gaban kotu kuma aka tsare shi a gidan yari.

Amma daga baya kotu ta wanke shi daga tuhumar da ake yi masa, kuma bayan ya dawo gida, ya gano cewa mahaifinsa ya sayar da gidansa, bisa zaton cewa ba zai dawo ba.

Yayin da aka karanta masa ƙunshin tuhumar a kotu, mahaifin ya musanta zargin, yana mai cewa ba shi da laifi.

Sai dai alƙalin kotun, Malam Munzali Idris Gwadabe, wanda ya bayyana cewa lamarin a matsayin rikicin cikin gida tsakanin uba da ɗa, ya miƙa shari’ar zuwa kotun sasanci domin ta jiɓanci taƙaddamar da ke tsakanin ɓangarorin biyu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ɗa Jihar Kano

এছাড়াও পড়ুন:

An dawo da malamai 103 da aka kora daga aiki a Zamfara

Gwamnatin Jihar Zamfara ta dawo da wasu malamai 103 da aka kora a baya sakamakon binciken tantance ma’aikata tare da biyan su bashin albashin watanni bakwai.

Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na jihar, Malam Wadatau Madawaki, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai kan sakamakon sake nazarin tantance malaman da ma’aikatars ta gudanar.

Madawaki ya ce an cire sunayen waɗannan malamai ne bisa kuskure “ko kuma ta mantuwa” a lokacin gudanar da tantancewar.

“Bayan an kammala tantancewar, mun gano cewa malamai 103 cikin waɗanda aka cire sunayensu an yi kuskure. Sun cancanci kasancewa cikin jerin malamai da aka tabbatar da su,” in ji shi.

Juyin mulki: Ana zargin tsohon gwamnan da ɗaukar nauyin sojojin Najeriya NAJERIYA A YAU: Shin Ya Kamata A Saki Shugaban IPOB Nnamdi Kanu?

Kwamishinan ya ce bayan gano kuskuren, ma’aikatar ta rubuta wa Gwamna Dauda Lawal takarda tana neman amincewarsa a dawo da su da kuma a biya su albashin da aka dakatar.

“Daga watan Janairu zuwa Yuli 2025, Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya da Fasaha ta rubuta wa Mai Girma Gwamna tana neman ya amince a dawo da waɗannan malamai 103.

“Alhamdulillah, Mai Girma Gwamna ya amince a dawo da su tare da biyan su bashin albashin watan Janairu zuwa Yuli 2025,” in ji Madawaki.

Kwamishinan ya ƙara da cewa gyare-gyaren da ake yi a ɓangaren ilimi na cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na tsaftace tsarin aiki da tabbatar da inganci.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dembele ya dawo PSG bayan jinyar makonni
  • Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da Suka Kashe Malamin Jami’a
  • Kotu A Faransa Ta Yanke Hukumci Zama Gidan Yari Ga Tsohon Shugaban Kasar Nicola Sarkozi
  • An dawo da malamai 103 da aka kora daga aiki a Zamfara
  • Matasa sun kama ɗan fashi ya kai hari gidan burodi a Kaduna
  • An saki Ɗan Uwa Rano bayan tsare shi kan zargin ɓata sunan hadimin gwamnan Kano
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 154
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 150
  • Mahukunta sun kai samame wani gidan shan Shisha a Kano