Kasar Sin Ta Sake Farfado Da Muhimman Koguna Da Tafkuna 88 A Kokarin Inganta Muhalli
Published: 22nd, October 2025 GMT
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Zimbabwe Ta Jinjinawa Jarin Sin A Matsayin Wanda Ya Bunkasa Masana’atun Samar Da Siminti A Kasar October 22, 2025
Daga Birnin Sin Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya October 21, 2025
Daga Birnin Sin Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da Karfin Iska A Karkashin Ruwa October 21, 2025
এছাড়াও পড়ুন:
DSS ta kama likitan da ke duba ’yan bindiga a dazukan Kwara
Hukumar Tsaro ta DSS ta kama wani likita da ake zargin yana ba da magunguna tare da kula da ’yan bindiga masu garkuwa da mutane da ke wasu sassan jihar Kwara.
An kama wanda ake zargin, wanda ba a iya gano sunansa ba a lokacin rahoton, a yankin Jebba bayan rahotannin sirri sun nuna cewa wasu masu safarar kaya suna kai magunguna daga Sakkwato domin kula da ’yan fashin daji da suka samu raunuka a dazukan jihar.
Kakakin majalisar dokokin Ribas da takwarorinsa 16 sun fice daga PDP zuwa APC An kashe matashi yayin rikici a wajen raɗin suna a BauchiMajiyoyin tsaro sun ce da dama daga cikin waɗannan ƙungiyoyin masu laifi sun samu raunukan harbin bindiga a fafatawar da suka yi da jami’an tsaro a baya-bayan nan.
“Saboda haka muna ba da shawarar ƙara tsaurara matakan tsaro a cibiyoyin lafiya da ke cikin dazuka, domin masu garkuwa da mutane na iya kai hari a wuraren,” in ji wani jami’in tsaro.
Mai magana da yawun gwamnan jihar ta Kwara, Rafiu Ajakaye, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa kamun wata babbar nasara ce a ƙoƙarin da ake ci gaba da yi kan ’yan fashin daji.
“Wannan babban mataki ne daga DSS. Ya ƙara tabbatar da cewa hukumomin tsaro suna matsawa wa waɗannan ’yan ta’adda, suna kuma toshe hanyoyin tallafi da ke ba su damar gudanar da ayyukansu,” in ji shi.
Ajakaye ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin tsaro domin rufe dukkan hanyoyin da ke taimaka wa ayyukan garkuwa da mutane.