2025-10-13@13:37:59 GMT
إجمالي نتائج البحث: 5
«rarraba wuta»:
Hukumar da ke Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta ce kamfanonin rarraba wutar lantarki guda 11 sun tara Naira biliyan 546.71 daga hannun abokan cinikinsu a cikin zango na biyu na shekarar 2025. Sai dai hukumar ta ce wannan adadi bai kai kaso 60 cikin 100 na wutar da aka tura musu daga babbar hanyar rarraba wuta ba, sakamakon matsalolin lissafin wutar da suka karɓa da kuma yadda aka raba wutar ga rukunan abokan ciniki daban-daban. Zulum ya ba ma’aikaciyar lafiya ’yar kabilar Igbo kyautar gida, ya ba danta aiki Matar aure mai ’ya’ya huɗu ta rataye kanta a Jigawa Hakan, a cewar hukumar, ya haifar da gibin biyan kuɗi na naira biliyan 167.25. kazalika, NERC ta ce...
A ci gaba da ƙoƙarinta na tabbatar da kyawawan halaye da kuma samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma, Hukumar Hisbah ta Jihar Yobe ta lalata katan 243 na barasa da galan 100 na barasa da aka haɗa a gida, da aka fi sani da sukudaye. A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na Hukumar, Adamu Muhammad ya sanya wa hannu, ta ce an lalata barasa a Damaturu, a wani mataki na aiwatar da dokar hana sha da kayan rarraba barasa a jihar. Guguwar ruwan sama ta yi ɓarna a Kwalejin Kimiyya da Fasaha a Kogi Tinubu na ƙaddamar da wasu ayyuka a Jihar Kaduna Shugaban Hukumar Hisbah na jihar, Dokta Yahuza Hamza Abubakar ne ya bayyana cewa aikin ya...
Jami’ai a Falasdinu sun ce akalla mutum 31 ne sukayi shahada sannan wasu sama da 150 sun jikkata, bayan wani hari da Isra’ila ta kai kusa da wurin rabon abinci a birnin Rafah. Dama shugaban hukumar MDD da ke kula da yan gudun hijirar Falasdinawa, Philippe Lazzarini, ya ce rabon kayan agajin ya zama tarkon mutuwa. Lamarin dai ya faru ne a kusa da wata cibiyar rarraba kayan abinci da gidauniyar agaji ta Gaza (GHF) ke gudanarwa, wani kamfani mai zaman kansa da ke samun goyon bayan Isra’ila da Amurka da kungiyoyin agaji na kasa da kasa suka yi suka. Kakakin kungiyar Hamas Sami Abu Zohri yayi Allah wadai da gwamnatin Isra’ila kan harin da ta aikata a rabon kayan...
Hukumar Kula Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC) ta ci kamfanonin rarraba lantarki tarar naira miliyan 628 kan laifin karɓar kuɗin wuta fiye da kima daga hannun kwastomomi marasa mita. Hukumar ta kuma ba wa kamfanonin rarraba lantarkin da hakan ta shafa wa’adin ranar 15 ga watan Mayu, 2025, sun tabbatar sun biya kwastomomin da suka canza fiye da kima, ta hanyar ba su wuta daidai da abin da suka ƙware su. NERC ta bayyana cewa ɗaukar wannan mataki ya zama dole saboda kamfanonin sun yi kunnen ƙashi bayan umarnin da ta ba su, wanda ya ƙayyade kuɗin da su caji kwastomomi da ba su da mita. Ta ce waɗanda aka ci tarar sun haɗa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na...
Wani rahoto da aka fitar yau Talata, yayin zaman taron shekara-shekara na shekarar 2025, na dandalin tattaunawa na Asiya na Boao, ya nuna yadda kasar Sin ke ci gaba da kasancewa cibiyar rarraba hajojin da masana’antu ke sarrafawa. Rahoton mai taken “Nazarin tattalin arzikin Asiya, da hadadden rahoton ci gaba na shekarar”, ya nuna yadda tun daga shekarar 2017, hada-hadar cinikayya ta duniya a fannin rarraba matsakaitan hajoji, ke kara dogaro kan kasar Sin sama da dogaronta ga yankin arewacin Amurka. Kazalika a shekarar 2023, dogaron sassan kasa da kasa kan kasar Sin ta fuskar samar da matsakaitan hajoji ya kai kaso 16 bisa dari, sama da na yankin arewacin Amurka mai kaso 15 bisa dari. Bugu da kari, rahoton...