Yadda Zanga-zangar Kanu ta ja wa ’yan kasuwa da ma’aikata asara
Published: 21st, October 2025 GMT
Harkokin kasuwanci sun tsaya cik a wasu sassan Abuja sakamakon zanga-zangar neman a saki shugaban ƙungiyar ’yan ta’addan IPOB da ke neman ɓallewa daga Najeriya, Nnamdi Kanu, inda masu ’yan kasuwa da ma’aikata da dama suka yi asarar kuɗaɗen shiga.
A yankunan Wuse, Banex da Mararaba, shaguna da kasuwanni da dama sun kasance a rufe saboda fargabar tashin hankali.
“Na kasa buɗe shagona yau saboda kowa yana tsoron tashin hankali. Ko da ka bude, babu wanda zai fito saye da wannan yanayin tsoro,” in ji Peter Ayuba, mai sayar da na’urorin lantarki a kasuwar Wuse.
A Smart Bridge Plaza da Zuma Garden da ke unguwar Utako, yawancin shaguna an kulle su, sai kaɗan ne suka buɗe. Wani ma’aikaci a shagon sayar da magani ya ce ba su yi ciniki sosai ba saboda rashin kwastomomi.
An maka mahaifi a kotu kan cefanar da gidan ɗansa a Kano NLC ta sa zare da gwamnati kan yajin aikin ASUUSu ma ’yan kasuwa masu yawon talla, zanga-zangar ta shafi kasuwancinsu. Agnes Ojeh, mai sayar da ayaba da gyaɗa, ta ce duk da gargaɗin da aka yi mata kada ta fito, sai da ta fito saboda tana da yara da take ciyarwa.
Ta ce, “Na fito ne daga Mpape, duk da akwai sojoji a kan hanyoyi, amma ban sayar sosai ba saboda mutane ba su fito ba.”
Wani mai shagon aski da ya bayyana kansa da “Black Governor” ya ce kasuwar Wuse ta zama tamkar fanko saboda yawancin ’yan kasuwa musamman ’yan ƙabilar Ibo ba su buɗe shaguna ba.
“Kasuwar ta kasance shiru har zuwa kusan ƙarfe shida na yamma,” in ji shi. “Kasuwar Utako ma an rufe da farko, daga baya ne aka buɗe bayan jami’an tsaro sun dawo da doka.”
Ya kara da cewa an kama wasu matasa da suka tada zaune tsaye a yankin Zone 6 domin dawo da zaman lafiya. Wani ɗan sanda a Utako ya tabbatar mana cewa an kai waɗanda aka kama ofishin SARS da ke Guzape.
A yankunan kasuwanci kamar Central Area, Jabi da Nyanya, ofisoshi da dama sun yi aiki kaɗan kaɗan saboda ma’aikata da dama sun makara ko kuma ba su fito gaba daya ba. Wani ɗan kasuwa a Mararaba, Uche, ya ce da dama daga cikin masu shaguna sun zauna a gida bayan jin labarin cewa masu zanga-zanga na nufin shiga tsakiyar birnin.
Duk da cewa zuwa misalin ƙarfe uku na rana, an fara samun ɗan kwanciyar hankali a wasu sassan Abuja, amma jama’a da dama sun ce zanga-zangar ta dagula musu rayuwa.
Wasu ’yan kasuwa sun ce sun rasa kusan duk kuɗin shigarsu na ranar Litinin, musamman waɗanda ke sayar da kaya masu saurin lalacewa.
Yanayin garin su KanuA Umuahia, babban birnin jihar Abia inda Kanu ya fito, ma zanga-zangar ta durƙusar da harkokin kasuwanci yayin da jama’a suka kulle shaguna da kasuwanni.
Masu zanga-zangar sun bayyana a wurare daban-daban suna waƙa da rawa suna kuma kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya saki Kanu.
An lura cewa babu motoci a tituna, bankuna, tashoshin mai, manyan kasuwanni da makarantu — duka a rufe suke.
A garin Afaraukwu, inda Kanu ya fito, mazauna yankin sun taru suna waƙar neman a sake shi. Wani da ya ce sunansa Chidi ya tambayi dalilin ci gaba da tsare Kanu a ofishin DSS.
Fadar Shugaban Kasa ta magantuMai ba Shugaban Kasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya buƙaci a dauki mataki kan lauyan Kanu, Barista Ejimakor, saboda shiga zanga-zangar da aka yi a Abuja.
Onanuga ya zargi Ejimakor da “saɓa dokokin aikin lauya” bayan da ya shiga zanga-zangar neman a sake Kanu.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Onanuga ya ce: “Ban san abin da Ejimakor yake tunani ba lokacin da ya shiga wannan zanga-zanga mai ban dariya.”
Ya ce lauya ya kamata ya san cewa batun Kanu yana gaban kotu, kuma akwai dokar ‘sub judice da ta haramta irin wannan tsoma baki.
Ya ƙara da cewa Ejimakor ya zaɓi hanyar siyasa da ba ta da tushe a doka domin tasiri kan shari’ar. “Ya kamata hukumar lauyoyi su ɗauki mataki saboda wannan rashin ladabi da rashin kiyaye ƙa’idar aikin lauya,” in ji shi.
Ra’ayoyin MasanaWani Farfesa a fannin shari’a, Okoh Akubo (SAN), ya bayyana cewa shari’ar Kanu ta zama abin damuwa.
“An taɓa wanke shi daga wasu tuhume-tuhume amma gwamnati ta ci gaba da sake gabatar da sababbi, shi ya sa shari’ar ke ci gaba har yanzu,” in ji shi.
Shi ma Farfesa Eno Cyprain daga cibiyar Institute of Law Research and Development ta Majalisar Dinkin Duniya da ke Washington DC, ya ce ya dace a saki Kanu ba tare da wani sharaɗi ba.
Ya ce idan gwamnati tana tsoron kalamansa, kotu na iya saka masa takunkumi maimakon tsare shi da ya zama tauye haƙƙinsa na faɗin albarkacin baki.
Ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta HURIWA ta soki yadda aka gudanar da zanga-zangar #ReleaseNnamdiKanuNow tana cewa tsare Kanu ya zama “azabar hadin gwiwa ga ƙabilarsa da magoya bayansa.”
Neman haɗin kan Kudu da ArewaMasani kan tsaro, Dakta Kabiru Adamu, ya bayyana tsawon shari’ar Kanu a matsayin “rashin nasarar tsarin shari’a” da kuma “bala’i ga ƙasa.”
Ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta haɗa masu ruwa da tsaki daga yankunan kudu maso gabas da Arewa domin samun hanyar sulhu ta siyasa.
“A gaskiya, shari’ar ta yi tsawo saboda dokokinmu ba su fayyace laifin da ake tuhumar Kanu da shi ba,” in ji shi.
Ya ce gwamnati na buƙatar “tsarin fita cikin mutunci” da zai kwantar da hankali a duka ɓangarorin kasar — musamman saboda ɓarnar da ta shafi rayuka, dukiyoyi da harkokin kasuwanci.
Shari’ar Kanu za ta ci gabaBayan rahoton Ƙungiyar Likitoci ta Ƙasa (NMA) ga Babban Kotun Tarayya a Abuja cewa lafiyar Kanu ba ta da hatsari, an tsara cigaban shari’ar sa ranar Alhamis, 23 ga Oktoba.
Alƙali James Omotosho ya ɗage karar zuwa wannan rana domin Kanu da lauyansa su fara kare kansu a shari’ar ta ta’addanci da ake yi masa.
A baya jami’an DSS sun shaida wa kotu cewa kalaman Kanu da kafa ƙungiyar tsaro ta Eastern Security Network (ESN) ne suka haddasa asarar rayuka da dukiyoyi a lokacin zanga-zangar #EndSARS a 2020
Kanu an dawo da shi daga Kenya a watan Yuni 2021 domin fuskantar sababbin tuhume-tuhume.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan kasuwa kasuwa Shari a zanga zangar
এছাড়াও পড়ুন:
Miliyoyin Mutanen Amurka Sun Yi Zanga-zanagr Nuna Kin Jinin Donald Trump
Amrukawan sun yi gangami a cikin wuraren da sun kai 600 a fadin kasar domin nuna kin amincewa da siyasar Donald rump akan batutuwa da dama da su ka hada da batun korar ‘yan hijira.
Masu Zanga-zangar sun daga kwalaye dake bayyana Trump a matsayin mai nuna wariya, wanda kuma yake daukar kansa a matsayin sarki.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sheikh Na’im Kassim Ya Mika Sakon Ta’aziyyar Shahadar Gumari Na Kasar Yemen Ga Sayyid Husi October 19, 2025 Sojojin HKI Sun Shiga Cikin Yankin Qunaidhara Na Kasar Syria October 19, 2025 Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Keta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta October 19, 2025 Hamas ta yi Allah wadai da Isra’ila kan keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta October 19, 2025 An gudanar da zanga-zanga a sassa da dama na Amurka October 19, 2025 MDD : “Zai dauki lokaci” kafin a rage yunwa a Gaza October 19, 2025 ICC ta ki amincewa da daukaka karar Isra’ila October 19, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 159 October 19, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Hassan(a) 158 October 19, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Al-Hassan (a) 157 October 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci