Bidiyoyin baɗala: Kotu ta umarci Hisbah ta daura aure tsakanin ’yan TikTok
Published: 21st, October 2025 GMT
Wata kotun majistare da ke Kano ta umarci Hukumar Hisbah ta jihar da ta shirya ɗaura aure tsakanin wasu fitattun ’yan TikTok guda biyu — Idris Mai Wushirya da Basira Yar Guda — cikin kwanaki 60.
Kotun ta bayar da wannan umarnin ne bayan yaɗuwar bidiyon Mai Wushirwa da ’Yar Guda a kafafen sada zumunta, da Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta bayyana a matsayin “na batsa da rahsin tarbiyya.
Bidiyoyin sun nuna waɗannan ’yan TikTok ɗin suna nuna soyayya a bainar jama’a, abin da hukumomi suka ce ya saɓa da ɗabi’u da koyarwar addini da al’adun mutanen Jihar Kano.
A yayin zaman kotun ranar Litinin, Mai Shari’a Halima Wali ta yi gargaɗi cewa idan ba a ɗaura auren cikin lokacin da kotun ta ƙayyade ba, za a ɗauki hakan a matsayin raina kotu.
EFCC ta ƙwato fiye da naira biliyan 500 a shekara biyu — Shetima An maka mahaifi a kotu kan cefanar da gidan ɗansa a KanoKotun ta kuma umurci Shugaban Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano Jihar Kano da ya tabbatar da aiwatar da wannan umarni na aure.
A makonnin baya an gurfanar da Mai Wushirwa da ’Yar Guda a gaban kotu bisa zargin yi da kuma yaɗa bidiyoyi masu nuna abin da aka bayyana a matsayin “batsa ko rashin kunya” a kafafen sada zumunta.
Tun da farko sai da kotu ta tura Mai Wushirya gidan yari saboda bullar wasu bidiyoyi da suka nuna shi yana aikata abin da hukumomi suka kira “aikata rashin kunya da tauye darajar addini” tare da yarinyar abokiyar aikinsa.
Hukumar tace fina-finai ta jaddada cewa waɗannan bidiyoyi sun karya dokokin jihar da ke haramta samarwa da yaɗa abubuwan da ke da alamar batsa ko rashin kunya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yam TikTok Yar Guda Mai Wushirya
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan
ShareTweetSendShare MASU ALAKA